RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 1 to 10

Gyaɗa kai kawai RAUDHA tayi tana ɗaukan wayan ta tana latsawa, hira Ramcy tafara mata tana jinta bata amsa ba har sanda tagama abinda take yi a wayan taɗago kai tana kallon ta, cikin yatsina tace “zan biki mu tafi tare”.

“Dagaske kike yi don Allah?” Ramcy tafaɗa cike da zumuɗi”.

Murmushi RAUDHA tayi tana gyaɗa mata kai

“Wow besty naji daɗi wlh, dama Ni kaɗai ne zani don Aunty Nafeesa tace min bata jindaɗi baza ta je ba tunda tare zamuje da ita”.

“Me yasame ta?” RAUDHA tafaɗa cike da kulawa tana kallon ta

“Wlh tunda tasami cikin nan abun dai babu daɗi, gashi har ya shiga wata shida bata dena ciwo ba”.

“Ok Muje ki rakani in gaishe ta”. RAUDHA tafaɗa tana miƙewa tsaye

Tashi itama Ramcy tayi taɗau gyalen ta suka fito waje

 Da Amaryan Baban Ramcy sukaci karo tana fitowa daga ɗaki

“A’a babbar baƙuwa mukayi ne?” Cewar Amaryan Baba tana faɗaɗa fuskarta da fara’a

Murmushi RAUDHA tayi cike da rashin tarbiyyar da be ishe ta ba tace “Yakike?”

Murmushi Amarya tayi tace “lafiya lau RAUDHA, ya gidan naku?”.

“Lafiya”. Ta’amsa ataƙaice

Ramcy tace “Zamuje gidan Aunty Nafeesa ne?”

“To adawo lafiya”.

Daga haka suka fice tabi bayan su da kallo tana murmushi, aranta tana tunanin yanda yarinyan take shigan banza babu me kwaɓa mata, tana da kirki sai dai babu tarbiyya ko a ido aka ganta an san haka, wuce wa kichen tayi aranta tana nema musu shiriya gaba ɗayan su

Duk da gidan babu nisa amma a mota suka je, bayan sun kai lungun gidan su Aunty Nafeesa inda mota bata shiga sai suka fito suka soma takawa a ƙasa, wani babban kwata suka zo tsallaka wa RAUDHA sai toshe hanci take yi tana yatsina fuska, abinda yake sawa bata zuwa anguwan kenan saboda wannan mummunan kwatan dake bata tsoro

Daƙyar tatsallaka shima sai da taimakon Ramcy, mutanen dake wajen kuwa sun kafo musu idanu sun saki baki suna kallon abun mamaki

Sun ɗan yi tafiya da suka shiga lungun sannan suka isa gidan Aunty Nafeesa, ita kaɗai ce agidan kuma ba wani babban gida bane, gida ne me ɗakuna biyu da Ban-ɗaki da kichen.

[11/14/2020, 8:02 AM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

  *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR*✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

_wannan shafin naku ne masoyan Littafin RAUDHA, ban taɓa tunanin laittafina yana da ɗumbin masoya haka ba sai yau, gaskiya naji daɗi, kuci gaba da sporting ɗina Ni kuma zan ci gaba da suburbuɗo muku me daɗi wanda zai saka ku farin ciki, nagode ???????? ????_

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON EIGHT*

_______????Suna shiga ciki Ramcy tarangaɗa sallama

Aunty Nafeesa dake kwance saman kujera ta’amsa musu tana tashi zaune daƙyar

Su kuma lokacin ne suka shigo cikin ɗakin

Aunty Nafeesa tana ƙyalla idanu taga RAUDHA dake bayan Ramcy tafaɗaɗa fuskarta da fara’a tana cewa “kai kai kai yau RAUDHA ce a gidana?”

RAUDHA kuwa murmushi tayi tasami kujera taɗan ɗofana akai kamar wacce take jin tsoro

Ramcy itama zama tayi tana cewa “Aunty cewa tayi in kawo ta tagaishe ki”.

“Allah Sarki ai kuwa na gode sosai”.

Sai lokacin ne RAUDHA tabuɗi baki ahankali da muryan ta adishe tace “ya jiki?”

Cike da fara’a Aunty Nafeesa tace “Alhmadulillah RAUDHA, kina lafiya?”

Gyaɗa kanta tayi tana wasa da igiyoyin wandon ta (bazar)

“Rahma ɗauko mata ruwa mana”.

Miƙewa Ramcy tayi tabuɗe ɗan ƙaramin Fridge ɗin dake ɗakin taciro fure water guda biyu taɗaura akan Fridge ɗin, sai da tarufe sannan taje taɗauko plate tajera ruwan takawo gaban RAUDHA ta’ajiye, ita dai kallon ruwan kawai take yi batare da ta motsa ba

“Besty kisha ruwa”. Cewar Ramcy tana kallon ta da murmushi

Ɗan kwaɓe fuskarta tayi kawai tana girgiza mata kai alamun baza ta sha ba

Ƴarinyan Aunty Nafeesan ce tashigo ɗakin aguje, sai tatsaya kawai tana kallon su Ramcy, sai kuma tamaida idanun ta kan RAUDHA da itama takafe ta da idanu, ga duk kan alamu yarinyan bata gane ta ba don tasan Ramcy sosai, sai tanufi wajen ta tana ɗaura ƴan ƙananun hannayen ta saman cinyan RAUDHA, dai-dai wajen tsakankanin inda wandon ta da Socks ɗin da tasa basu rufe ba, sai kuma takoma tana wasa da bazar ɗin wandon

Ramcy tace “ke uwar ki tashi awajen nan”.

Yarinyan kamar bataji ba sai tasake matsawa sosai wajen RAUDHA tana tattaɓa ta, ita kuma RAUDHA sai janye jikin ta take yi kamar taga abun tsoro, duk da yara suna burge ta amma bata son ko kaɗan su zo kusa da ita sabida suna bata tsoro wani lokacin idan suka cika ƙanƙanta, bare kuma wannan itama ƴar ƙanƙanuwa ce don baza tafi 2yrs ba

Ganin dai baza ta dena taɓa ta ba sai tazare mata manyan idanuwan ta tana hararan ta tare da matse jikin ta waje ɗaya, ko kunyan akwai Maman ta awajen bata ji ba

Aunty Nafeesa kuwa murmushi kawai tayi tamiƙe tana janyo hannun yarinyan tace “zo nan Khadeeja, bakiga baƙuwa bace?”

Ɓata fuska Khadeejan tayi tasoma gwarancin ta, sai kuma taƙwace hannun ta tana ficewa da gudu

Ajiyan zuciya RAUDHA tasaki wanda hakan yasaka duk suka kalle ta, ita kuma bata ma san suna yi ba

“Kin ƙi shan ruwan RAUDHA, gashi kuma babu abinci” 

Yaƙe tayi tana sake girgiza kanta, sai kuma tace “a’a anty na ƙoshi ne”.

Ramcy tace “Aunty tare da besty zamuje bikin Shatu fa”

“Haba dai don Allah dagaske?”

“Wlh kuwa tace zataje”.

Murmushi Aunty Nafeesa tayi tace “Allah Sarki mun gode kuwa, idan kinje sai kigaishe ta dakyau ki faɗama Mama bani da lafiya ne, nima dai zan kira ta awaya in sanar musu”.

RAUDHA miƙe wa tayi tana kallon su, hakan yasa itama Ramcy tamiƙe tana cewa

“Aunty mu zamu tafi, zan faɗa mata insha Allah”.

Itama tashi tayi daƙyar tana cewa “to muje in taka muku”.

RAUDHA da taciro kuɗi cikin jaka tamiƙa wa Aunty Nafeesa tana cewa “gashi anty”.

Kallon kuɗin me uban yawa tayi tana cewa “ah RAUDHA har da ɗawainiya?”.

Murmushi RAUDHA tayi

Kuɗin ta’amsa tana ta mata godiya cike da farin ciki, fitowa sukayi gaba ɗayan su Aunty Nafeesa sai sake mata godiya take yi aranta tana yaba halin kyauta irin na RAUDHA

Wani matashin saurayi ne yashigo gidan yana taje kansa da kumb, tsayawa yayi akan hanya yana kallon su gaba ɗaya kamar yanda suka tsaya su ma suna kallon sa, sai yarausayar da kai yana sauke idanun sa kan RAUDHA

“Aunty Nafeesa wannan kuma fa? aina kuka samo mana inyamura har cikin gida?”

Sai kawai tasaki baki ita da Ramcy suna kallon sa a yanayin tsoro

Ita kuwa RAUDHA naɗe hannayen ta a ƙirji tayi tana zuba masa lumsassun idanun ta da bata iya buɗe su sosai

Zai sake magana Ramcy tayi saurin katse sa da faɗin “haba don Allah Yaya Abba, tare fa mukazo da ita ina ruwan ka da ita?” Taƙarike maganar ta tana hararan sa

Washe baki yayi yace “eyya ai bansani ba my dear, shiyasa wlh nake ƙara son ki sabida wannan farin da kike min da ido????????, wai yaushe ne zaki bani dama ne nariƙa zuwa gidan ku? kinsan son da nake miki Rahma bazan iya rabuwa dake ba, ki daure kiduba maganata”

Ramcy turo ɗankwali gaba tayi cike da jin haushin sa, tasan halin sa sarai zai iya tsokano RAUDHA yanzu abu yacaɓe musu idan har basu rabu lafiya ba, don haka tace “kabar wannan maganan idan muka sake haɗuwa zamuyi magana yanzu ina da baƙuwa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button