RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 1 to 10

Cike da jindaɗi  Abba yamatsa musu a hanya yace “yauwa masoyiya to shikenan sai mun haɗu ɗin, zan Bama Aunty Nafeesa saƙo sai ki amsa a wajen ta”.

Yatsina fuska tayi kawai tawuce don tuni RAUDHA tafice abinta tunda yamatsa musu a hanya

Sai da Aunty Nafeesa tabi su har ƙofar gida tasake ɗaga musu hannu kafin tashige gida

Suna zuwa wajen motan suka shige RAUDHA taja suka tafi, a ƙofar gidan su Ramcy tatsaya taɗau jakan ta tabuɗe taciro kuɗi tamiƙa mata

Gashi ki Bama Amarya Ni zan tafi bazan shiga ba, gobe sai kizo ke ki amsa naki sai ki siya duk abinda kike buƙata a bikin, ban da ishashshen kuɗi anan”.

Murmushi Ramcy tayi ta’amsa tace “thanks Babe Allah yabar mana ke”.

RAUDHA riƙe sitiyarin motan tayi tana kaɗa yatsunta akai batare da tace uffan ba, ita kuma Ramcy ganin haka yasa tabuɗe motan tayi mata sallama tafice sannan taja motar tatafi.

Itama Ramcy halayyan su ɗaya da RAUDHA na rashin kula maza ko kaɗan babu ruwan su da shiga shirgin namiji, wannan dalilin ne yasaka RAUDHA tasake yarda da Ramcy tazama ƙawarta tunda halin su ɗaya, kuma shiyasa take mata duk wani abu ba sai ta buƙata wajen samari ba, duk da iya ƙoƙari dai mahaifin ta yana mata duk abinda tatambaye shi in dai yana da halin yi zai yi mata.

Cikin ƙanƙanin lokaci RAUDHA ta’isa gida, tana yin parcking tafito tarufe ƙofan tanufi cikin gidan, Direct ɗakinta tanufa, tana shiga taci karo da Babban baƙin leda ajiye saman Centre table dake kusa da kujera, siyayyar da Saude tayi mata ne

Kan gado tafaɗa tana sauke ajiyan zuciya, gaba ɗaya duk ta tara ma kanta gajiya a ɗan wannan fitan da tayi, sai faman yamutsa fuska take yi duk tana jinta babu daɗi sakamakon mummunan ƙaton kwatan nan na anguwan su Aunty Nafeesa da tagani, miƙe wa tayi a yanayin gajiya tafara cire kayanta tashige Toilet, wanka tayi sosai wanda yaɗauke ta tsawon lokaci kafin tafito, shiryawa tayi cikin Shuɗin Vest da baƙin Leggings takoma Kan kujera tazauna, buɗe ledan tayi tana duba duk abinda ke ciki, kayan zaƙi ne kala da iri su Chaculates, Biscuits, sweets da sauran su, ɗaukan Sweet tayi tabuɗe tasoma sha tatashi tanufi wajen gadonta taciro wayan ta cikin jaka, komawa kan kujeran tayi tasoma latsa wayan takira Daddyn ta, yana peacking tace

“Daddy Good Evening”.

“My daughter kina lafiya?”

“Lafiya Daddy ya aikin ka?” Tace hakan tana lanɗe baki

“Me kike ci haka ki tsanmin my dear?” Daddy yafaɗa cike da ƙaunar yarinyan tasa

RAUDHA dariya tayi har fararen haƙoran ta suna bayyana tace “Daddy sweet ne”.

“Oh Daughter ba na hanaki Shan kayan zaƙi ba?”

Cikin shagwaɓa tace “Daddy ai bana sha, wannan yanzu ne nasiya nasha”.

“Ok to ki kula bana so, kinsan nafison lafiyan ki”.

RAUDHA tace “ok.. Daddy zan bi Ramcy Kaduna ana bikin Cousin ɗin ta”.

“Kaduna kuma Daughter?”

“Eh Daddy”. Tafaɗa tana marairaice murya

Daddy yace “ok to shikenan but Sweetheart ki kula da kanki uhmm?”

“To Daddy Kai fa yaushe zaka dawo?”

“Zuwa nan da One Month insha Allahu ina tare dake my sweetheart”.

Kuka tasaki cikin taɓara, nan da nan hankalin Daddy yatashi yasoma tambayan ta

“My daughter lafiya menene faɗa min mana kiyi shiru kinji?”

Cikin kukan take cewa “Daddy har sai One Month zaka dawo? Gaskiya Ni bazan yarda ba sai na biyo ka”.

Cikin rarrashi Daddy yace “sorry My Baby umm? Kinga inada aiki sosai ne kuma zan wuce Chaina wani Business Ni da abokan aikina, zan yi two weeks acan kinga zan iya kai wata ɗaya kafin in dawo”.

Tsalle tabuga akan kujeran tana cewa “Daddy Chaina?”

“Yes my dear”.

Cike da tsananin murna tace “Daddy please kaje dani ina son zuwa”.

Murmushi yayi don yasan babu ƙasar da tafi so sama da Chaina, Allah ya ɗaura mata son ƙasar kamar ranta, tana son duk wani abu da yadanganci can ɗin kuma sau ɗaya tataɓa zuwa, sai da tayi wata ɗaya acan ita da Daddyn ta har yaren sai da tasoma koya a lokacin, daga wancan zuwan bata sake komawa ba

“Kar ki damu Babyna kibari idan kin soma zuwa school kuna samun hutu acan zakiyi Holiday ɗin ki”.

“Yeeeee Daddy I Love you so much”.

Tabuga masa Kiss ???? ta wayan cike da tsananin murna

Dariya Daddy yayi yace “I love you too my dear Daughter, ki huta kinji sai anjima zamuyi waya”.

“To Daddy Byeee”.

Daga nan katse wayan tayi tana ajiyewa cike da farin ciki.

.

????????????????????????????????

     Yau kwana uku kenan da kama Jawad, idan kuka ganshi baza ku iya shaida shi ba sabida dukan da yake sha duk sun sauya masa kamanni, kuma an ƙi barin kowa yaganshi

A ranan na huɗun ne daƙyar DPO yayarda yagansu, Mahaifiyar Jawad ɗin ne tare da Deeni suka zo, duk iya magiyan da sukai masa sam ya hanasu ganin Jawad kuma yaƙi bada belin sa, daga ƙarshe sai ce musu yayi su je can su nemi RAUDHA su bata haƙuri sannan idan ta yafe sai asake shi

Babu yanda suka iya suka fito suka nufi gidan su RAUDHA, babban katafaren gidan mahaifin ta sukaje don nan Deeni yasani, sunyi bugun duniya amma an ƙi buɗe musu ƙofa, sun fi awa ɗaya a wajen ko zasuga wani yafito amma babu kowa dole suka tafi gida da niyyar gobe su bugo sammako su dawo.

[11/14/2020, 8:15 AM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

  *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR*✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON NINE*

_______????Ƙarfe 11:30am. Suka bugo sammakon komawa ƙofar gidan, yau ma sunyi bugun duniya amma shiru anƙi buɗe musu ƙofa, wasa-wasa sai da suka share fiye da awanni biyu a wajen suna jiran tsammanin marabbuka

Can daga ƙarshe da sukayi ta bugun ƙofan sai gashi an buɗo ƙaramin Door ɗin wani shirgegen mutum ya fito fuska a ɗaure, Me gadi ne kuma tun sanda suka soma buga ƙofan duk yana ji amma yaƙi fitowa a tunanin sa masu maula ne tunda sun saba zuwa, koron duniya idan yayi musu sai gobe ma sun sake dawowa kasancewar Alh. Mustapha mutum ne me kyauta sosai, abun hannun sa baya rufe masa idanu kuma a wajen shi RAUDHA takoya, don tacire maƙudan kuɗi ta kyautar hakan ba komi bane

“Wai uwar me za’ayi muku kuke ta bugun ƙofa? An ce muku Alhajin baya nan amma tunda ku mahaukata ne baza ku dena zuwa ba”. Me gadi yafaɗa hakan yana bin su da uwar harara kamar yamaƙure su yake ji sabida tsaban takaici

“Bawan Allah ba abinda kake tunani bane yakawo mu, mun zo ganin Hajiya ne”. Cewar Mahaifiyar Jawad cike da muryan tausayi

Me gadi sake bin su da kallon ƙasƙanci yake yi kamar ma be ji me suka ce ba yace “Hajiya..? Kuke neman Hajiya wata Hajiyar kenan?”

Tace “Yarinyan Alhaji”.

Dogon tsaki yaja don takaici be tsaya sake jin me zasu ce ba bare yabasu amsa yajuya da ninyan komawa

Deeni yayi saurin matsawa kusa dashi yace “don Allah kataimaka mana kayi mana magana da ita, itace tace har sai munzo mun bata haƙuri kafin tasaka asaki Abokina da ƴan sanda suka kama”.

Sai alokacin me gadi yaɗan dakata daga rufe ƙofan da yasoma yi, fuska babu walwala yace “to babu ita anan, ku neme ta acan gidan ta”.

Sai da suka sake roƙon sa gaba ɗayan su don yafaɗa musu inda gidan ta yake, daƙyar yasanar dasu shima ɗin sai da yagama musu wulaƙanci da faɗa musu baƙaƙen maganganu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button