RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 1 to 10

Murmushi kawai yayi yace “Baby ki kula da kanki kinji I Love You”.

Kamar baza ta amsa mishi ba sai kuma tace “me too”.

Still Murmushi yayi kawai yatsinke wayan yana sauke ajiyan zuciya, fatan sa ɗaya kawai kar ƙanwar tasa tayi fushi dashi don yasan fushin ta babu kyau, tana da matuƙar kafiya da taurin kan tsiya, wanda hakan yake sa duk abinda tabar shi ta barshi kenan har abada, idan kuwa tayi fushi dasu tana ɗaukan lokaci kafin takula su, sai tayanke duk wani alaƙa dasu gaba ɗaya.

[11/14/2020, 8:35 AM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

  *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR*✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON TEN*

_______???? *WASHE GARI*

Ranan da zasu tafi Kaduna bikin ƴar ƙanwar Maman Ramcy

12:30pm. Me keke napep yasauke Ramcy a ƙofar gidan RAUDHA

Tayi shiga cikin wata koriyar atamfa me ratsin ruwan hanta ajiki, ɗinkin babu ƙarya yayi kyau sai dai anci ma atamfan mutunci sosai, riga da skert ne akayi mata kuma yayi mata kyau duk da kasancewar ta baƙa amma kyakykyawa ce Ramcy sosai, ta yafa gyale a kafaɗun ta sai jakan da tazuba kayan ta ciki

A haka tashige gidan tana taku ɗai-ɗai

Koda tashiga cikin parlour’n da Saude suka ci karo ta fito daga kichen, gaisawa sukayi tatambaye ta RAUDHA

Saude tafaɗa mata tana ɗakin ta har yanzu bata sauko ba

Bata sake cewa komi ba tanufi upstairs ɗin, tana zuwa tatura ƙofan tashiga tana kallon RAUDHA dake kwance tayi baja-baja saman tafkeken gadon ta dake iya cin mutum biyar, sai sharan barcin ta take yi hankali kwance bata da alaman farkawa

Shigowa ciki Ramcy tayi tanufi bakin gadon tazauna, shiru tayi naɗan wani lokaci tana tunanin yanda za’a yi tatashe ta, daga ƙarshe dai tayanke shawara takai hannun ta tana taɓa ta tare da kiran sunan ta a hankali

Ta jima tana faman tashin ta kafin tabuɗe shanyayyun kumburarrun idanuwan ta da suka sauya kala sosai sabida tsaban barci, sake lumshe idanun tayi tana sake buɗe su akan Ramcy dake faman kallon ta

Cikin tausasa murya tace “Besty har yanzu baki tashi ba? gashi har 12:00pm. Ɗin ta wuce”.

Shiru RAUDHA tayi bata iya ce mata komi ba, sai faman kokuwa take yi da lumsassun idanun ta da suka ƙi buɗe wa

Sai da tayi wajen mintuna 5 kafin tasoma yunƙurin tashi zaune tana faman riƙe kanta

Ramcy kuma tashi tayi takoma kan kujera tana faman kallon ta sai dai bata furta komi ba, don tasan ko ta sake magana ba kula ta zatayi ba

Sai da tagama nawan ta kafin tatashi tasoma cire kayan ta batare da taji kunyan Ramcy ɗin ba tunda ta saba

Ita ma kuma Ramcy ko ajikin ta sai kawar da kai tayi tana latsa wayan ta

Mintuna 20 RAUDHA taɗauka kafin tafito cikin Toilet ɗin, lokacin duk abinda tasha a daren jiya ya sake ta ta koma normal, idanun ta ma sun washe sosai sun koma fari tarrr ɗin su sai dai kumburan da sukayi ne be washe ba, wanda hakan yasaka suka sake lumshewa

A gaban dressing mirror tazauna tasoma busar da yalwataccen gashin kanta da yakasance baƙi siɗik me yawan gaske, bayan ta gama tashafa Expensive Lotions ɗin ta masu tsananin ƙamshi, batayi kwalliya ba illa powder da tashafa tasaka gazal a fararen idanuwanta, hakan yasaka suka ƙara kyau tare da ɗaukan hankali ga duk wanda yakalla, Lipstick tashafa a ƙananun laɓɓan ta tamiƙe tanufi Sif ɗin kayan ta

Kaya tasoma zaƙulowa tana ajiye wa asaman gado

Lokacin ne Ramcy tataso tazo bakin gadon tazauna tana kallon ta tace “dasu zaki tafi?”

Gyaɗa mata kanta kawai tayi taci gaba da ciro kayan

Ramcy tace “ok Aina zan shirya miki?”.

Tsayar da abinda take yi tayi tanuna mata jerin Trolly ɗin ta tace “ki ɗau na saman”.

Tashi Ramcy tayi taɗauko ɗan ƙaramin Trollyn kamar yanda tace mata tasoma shirya mata kayan ta ciki

Ita kuma alokacin taciro waɗanda zata saka tamatsa wajen kujera tasoma saka wa

Riga ce Robber me gajeren hannu baƙa da tatsaya mata iya ƙasan gwiwan ta, gaban rigan me tattara ne kuma anyi masa ado da stone masu tsananin ƙyalƙyali, sannan yana da igiya da taɗaure ta bayan ta, sai tasaka gajeren Socks red colour da Hill shoes ɗin ta me igiya shima Red colour, sai yazamana Ƙwaurin ƙafafun ta a waje suke

Gaban Looking mirror tanufa tasoma gyaran gashin ta sannan taɗaure da jan Ribom a tsakiyar kanta, shi kuma jelan taninke shi tayi kamar Dhounot, sai taɗaura Facing Cap baƙi da akayi harafin *R* agaban da jan zare, Parfomers ɗin ta taɗauka tafeshe jikin ta dashi sai faman zuba ƙamshi take yi, sosai tayi kyau kamar wata baby doll

Duk abubuwan da zata ɗauka sai da tazuba su cikin HangBag ɗin ta sannan suka fito Ramcy na jaye da Trolly ɗin

Su Saude da suke parlour nan sukayi musu adawo lafiya duk da kuwa basusan inda zasu je ba, amma ganin su da Trolly sun san tafiya ne yakama su

Ramcy ce kawai ta’amsa musu har suka fice

Suna fita compound ɗin gidan suka shige cikin farar motan da RAUDHA tace a wanke mata, horn tadanna tanufi bakin Gate a guje

Kafin ta’iso tuni me gadi ya hangame mata Gate ɗin tacilla motan waje sai saman kwalta

Kallon Ramcy tayi kafin takau da kanta zuwa titi tace “Besty ciro min tables ɗin nan cikin HangBag”.

“Ok”. Cewar Ramcy tana ɗaukan HangBag ɗin tabuɗe taciro mata

Nuni tayi mata da yatsu biyu hakan yasa taɓallo mata guda biyu tamiƙa mata, ta’amsa tasaka abaki tasoma tsotsa

Itama Ramcy ɗin cire ɗaya tayi tasaka a bakin ta sannan tamayar da sauran cikin jaka

Gudun da RAUDHA take tsulawa a saman kwalta ɗin baza ka taɓa tunanin zasu iya kai wa lafiya ba, over taking kawai take yi cike da ƙwarewa batare da ko tsoro ba

Sun ɗau hanyan Kaduna ɗoɗar lokacin ƙwayoyin da ta’afa sun soma aiki, gudun yanzu da take yi ma yafi na da

Gab da sun kusa shiga Kaduna tun daga nesa suka hango Sojoji sun tare hanya, but hakan be sa ta rage Speed ɗin motan ba

Wannan dalilin ne yasaka wasu daga cikin sojojin suka tsaya a tsakiyar hanyan riƙe da bindigogi suna jiran isowar motan

Sai da ta’iso gab dasu kamar zatayi ciki dasu kafin taja wani wawan burki da har yatsorata su tatsayar da motan cakk

Tashin hankali, gaba ɗaya Ramcy ta tsure don batasan me zai biyo baya ba da ganin yanda sojojin suka fusata sosai sukayo wajen motan

Ita kuwa RAUDHA ko a jikin ta sai faman ware lumsassun idanun ta dake faman rufewa take yi

Suna isowa biyu daga ciki suka bugi motan da ƙaton takalmin su cikin tsawa suka basu umarnin fitowa

Waɗanda suka hangi su Ramcy cikin motan sai abun yayi matuƙar basu mamaki ganin macece me wannan aika-aikan batare da taji tsoron abinda zai biyo baya ba, sakin baki kawai sukayi suna kallon RAUDHA da tasauke hulan ta ta’ajiye saman cinyan ta tazuba musu narkakkun manyan idanuwanta bata da alamun fitowa

Biyun da suka bugi motan waɗanda suka fi kowa fusata su ma leƙa motan sukayi da ninyan su ci mutuncin na ciki sai suka hangi mata , haɗiyar yawu duk kansu suke yi suna kallon su cike da sha’awa, kun san yawancin sojoji mayun mata ne ????????, bare waɗannan masu ido a tsakar ka kallo ɗaya kayi musu zaka hango zalaman su, yawancin su ma duk Christian ne

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button