RAUDHA Page 1 to 10

Suna shiga sai idanun mutane da yawa yadawo kan su sai kallon RAUDHA ake yi wacce ita kuma ta kafe inda MC ke tsaye yana surutun sa da idanu
Sai da Ramcy tariƙo hannun ta suka shige wajen kujerun sannan ne tadawo da hankalin ta gare ta
Zama sukayi akan kujeran da babu kowa
Hankalin fa abokan ango gaba ɗaya ya koma kan RAUDHA tun sanda tashigo tatafi da duk wani nutsuwar su
Har wani daga cikin su dai sai da yaciri baki yayi ma ango magana “ko ya santa ne?” Shi kuwa yakaɗa kansa kamar ƙadangare yana murza baki yace
“A’a Niii..? wlh bansan taba, sai dai ko Babyna?”.
Shatu dake gefen sa tana jin duk abinda suke faɗa tace “nima haka yanda kuka ganta haka naganta..”
Maganar da MC yayi ne yadawo dasu daga surutun da suke yi
Sai suka tashi suka fita filin rawa inda MC yakira ango da amarya akan su zo su taka
Duk abokan tashi sukayi suka nufi yin musu manne, amma banda wanda yake tambayar Ango ɗin ko sun san RAUDHA ne
Hankalin sa gaba ɗaya yana ga su RAUDHA, sai daga baya ne shima yatashi yanufi fili yana sakar musu maƙudan kuɗi kamar wanda be san zafin sa ba
Yana gamawa kuwa yaratsa yafito cikin cunkuson ƴanmata da samarin da suka cuɗe waje ɗaya duk wai akan sun zo ma Ango da Amarya manne
Wajen su Ramcy yanufa dake zaune su basu tashi ba, sai ma RAUDHA da takifa kanta saman table sakamakon Ciwo da kanta ke mata, duk da sosai take son daurewa amma abin ya gagara dole takwantar da kanta don taji daɗi
Yana isowa yayi musu sallama idanun sa akan RAUDHA wacce ma batasan yana yi ba
Amsa masa sallaman Ramcy tayi tana kallon sa, ganin dai ba ita yake kallo ba sai itama taɗauke kai taci gaba da latsa wayan ta
Zama yayi sannan ne alokacin yadawo da idanun sa kan Ramcy ɗin yana murmusawa yace “ƴan mata sannun ku dai”.
“Yauwa sannu”. Ramcy tabashi amsa batare da tasake kallon sa ba
Numfashi yasaki yana ƙara mayar da idanun sa kan RAUDHA ɗin yace “amma wannan lafiyan ta ƙalau ana shagali tana kwance?”
Sai alakocin Ramcy tasake dawo da idanun ta kansa, kuma a lokacin ne tayi masa kallon ƙurilla
Kyakkyawar saurayi ne me ji da kyau da kuɗi, ko kaɗan baya da makusa, yana sanye cikin farar Gezna wanda akasarin abokan dama shi suka saka, sai ɗai-ɗai ku da suka sanya farar Shadda
“Lafiya lau”.
“Ok Allah yasa hakane, but don Allah ko zaki iya min magana da ita coz wurin ta nazo”.
Ramcy tace “ai tana jinka duk abinda zaka faɗa”.
Dafa table ɗin yayi yana ɗan bugawa yace “ƴan mata Plz ki tashi muyi magana”.
Ramcy da taɗau Juice tana sha ta’ajiye tana faɗin “me zai sa sai tatashi? Kawai kayi maganar ka mana ai kunne???? ke ji”.
“Kuma hakane fa”. Yafaɗa yana dariya
Sai kuma yasake mayar da idanun sa kan tulin gashin ta cike da sha’awa yace “Baby Ni dai har ga Allah kinyi min ne shiyasa nataho don na yaɗa manufa na akan ki, sunana Saifullah zan zo insan naki sunan?”
Shiru RAUDHA tayi bata da alamun tashi duk da tana jin sa
Ramcy kuwa ganin ya hau mata magiya sai takatse shi da faɗin “Besty bata da lafiya kayi haƙuri ka ƙyale ta haka nan”.
Bada son ransa ba yayi shiru but ya so yasake ganin baby face ɗin ta, amma babu yanda ya’iya sai yanemi Numban wayan ta wajen Ramcy
Ita kuma Ramcy tabashi nata kamar yanda tayi ma Sojan can
Miƙe wa yayi yayi musu sallama yakoma wajen abokan ango wanda tuni sun ƙosa yazo yabasu labarin RAUDHA don sun san wajen ta yatafi, duk da kuwa su ma suna son ace su ne suka samu gurbi a wajen ta
Ramcy magana tayi ma RAUDHA akan zata je wajen Shatu kafin tatashi tatafi, bata jima ba tadawo tace
“Besty tashi muje naga alamun wajen baya miki daɗi”.
Kamar jira take yi kuwa tamiƙe dafe da kanta tayi gaba Ramcy tabi bayan ta
Wani daga cikin abokan Angon da tun sanda yaƙyalla idanu akan RAUDHA yasusuce, yana ganin sun fita yamiƙe kamar yana waya shima yafice
Yana fita yasoma waige-waige ko zai hango su amma ko me kama da ƙeyan su be gani ba, sai motar da yagani tafice da gudun tsiya, sai da yaɗan ƙara duddubawa ko zai gansu kafin yayi tunanin ko su ne suka fita, sai yayi saurin shiga motar sa yatake musu baya, but ko me kalan motan su ma be gani ba a hanya amma haka yaci gaba da tafiya ko Allah zai sa yadace
Abinda be sani ba bata hanyan ma da suka bi yabi ba, domin suna soma tafiya RAUDHA tatsayar da motan, sosai kanta ke sara mata kamar zai rabe gida biyu, riƙe kan tayi da hannu ɗaya tana yarfe ɗaya hannun
“Lafiya Besty menene?” Ramcy tafaɗa cike da tashin hankali
Jujjuya kanta take yi kafin tace “kaina ke ciwo zafiii”.
Duk hankalin Ramcy ya tashi haka take ta mata sannu, daga baya tace “su je asibiti”
But ita RAUDHAN tagirgiza mata kai alamun a’a, sai tabuɗe Lockern cikin motan taciro Cocaine ɗin ta tasoma shaƙa wai ko zai sa taɗan ji dama-dama idan hankalin ta yagushe
Ramcy dai sai kallon ta take yi tana mata sannu
Tsawon mintuna 5 taɗauka idanun ta a lumshe kafin tayi ƙarfin halin kunna motan taci gaba da tafiya, but sai dai yanzu ɗin a hankali take tuƙa motar har sanda suka ƙarisa cikin hotel ɗin tayi parcking, fita tayi batare da takashe motan ba
Sai Ramcy ce tazagayo ta’amsa keey ɗin takashe kafin takulle motan suka nufi ciki, har sun shiga reception Ramcy tatuna basu ɗauko Jakan kayan su ba, sai tadubi RAUDHA dake riƙe da kanta tana faman haɗa hanya tace
“Besty jira Ni anan bari in ɗauko Mana Jakan mu”.
Gyaɗa mata kanta tayi, ita kuma tafice dasauri
Ci gaba da tafiya tayi tahaye benen, daƙyar take tafiyan saboda yanda Cocaine ɗin yasoma gusar mata da hankali, ahaka tahaura saman tadoshi ɗakin su, tana shan kwana taji tayi karo da mutum sai dai takasa ɗago kanta bare taga wanda tabuge, illa lafewa da tasake yi ajikin sa tana shaƙar daddaɗan ƙamshin sa
Hannun sa biyu yasa yaɗago kanta yana kallon Beauty face ɗin ta da talumshe idanuwan ta, wani irin ƙunci da baƙin ciki ne yaji ya ziyarce shi lokaci ɗaya
Sosai yagane ta tunda kayan ɗazu ne ajikin ta
Tabbas tun kallon farko da yayi mata yatabbatar da ita ɗin mara tarbiyya ce duk da har yanzu be tabbatar wa kansa ita musulma ce ko Christian ba, yanzu kuma gashi ya ganta cikin hotel kuma a buge hakan ya tabbatar masa da zargin sa, hakan yasaka kuma yaji mugun tsanar ta da haushin ta cikin ransa wanda be san dalili ba
RAUDHA buɗe kyawawan idanunta da a yanzu suka sauya kala tayi, tasauke cikin nasa idanun da yakafe ta dasu
Duk da gaban sa yayi mugun faɗuwa amma hakan be sa ya tattakura ya tunkuɗe ta ajikin sa ba
Da bango tabugu kafin tafaɗi yarab a ƙasa, tsananin azaban da yaziyarce ta batasan sanda taware idanun ta duk ka waje ba tana fashewa da kuka, ban yi zaton idanun ta sun kai girman hakan ba sai yau da tafiddo su waje tsaban taji azaba ????
Kallon kallo kawai suke yi yayinda take gunjin kuka
Cike da takaicin ta yatamke fuska yana aika mata da banzan kallo yace “kin zata kowa irin ki ne mara tarbiyya ƴar ƙwaya Da zaki haɗa jikin ki da nawa? Wawiya kawai”. Yaja dogon tsaki yana tsallake ƙafafun ta yawuce dasauri-sauri cikin tafiyan sa na zaratan maza
Lumshe idanuwan ta tayi hawaye na kwaranya saman kuncin ta
Yau da tana da ƙarfi a jikin ta wlh da babu abinda zai hana ta cin collarn rigansa sai taga wanda yaɗaura wa Uwar sa aure
Tana nan zaune har sanda Ramcy tadawo, ganin RAUDHA a ƙasa ya ɗaga mata hankali, cikin sauri tace “Besty ya haka faɗi kika yi?”