RAUDHA Page 1 to 10

Tatambaye ta tana ɗago ta a lokaci ɗaya
RAUDHA bata iya ce mata komi ba sabida tsananin tuƙuƙin da zuciyarta take mata da maganar da wannan mutumin yafaɗa mata da kuma abinda yayi mata, sabida tsaban baƙin ciki ma gaba ɗaya ta dena jin ciwon
Har sanda taɗaga ta sannan tariƙo ta suka ci gaba da tafiya
Suna shiga ɗakin RAUDHA taƙwace jikin ta tanufi kan gado tafaɗa kai tana lumshe idanuwan ta da har yanzu sun kasa dena fid da hawaye
Ramcy duk bata kula da hawayen da take yi ba, sai zama da tayi tana tambayan ta abinda zasu ci
Sai alokacin ne ma ita RAUDHAN tatuna rabon ta da abinci tun daren jiya, tunda koda Ramcy tazo gidan ta ita tatashe ta a barci, kuma bata ci komi ba suka taho, gashi yanzu har duhun magriba ya shiga bata sanya komi a bakin ta ba
Bata kula Ramcy ba itama kuma sai bata sake cewa komi ba, tasan halin ƙawarta ba ko yaushe take son magana ba sai idan taga dama koda zaka shekara kana mata maganan ne, ita ɗin ƴar ganin dama ce
Har aka kira isha’i RAUDHA bata motsa daga inda take ba
Ita kuma Ramcy tuni har tayi wanka ta sauya kaya ta gabatar da sallan da ake bin ta yau ɗin, sai da tagama ne tasake dawowa tatambayi RAUDHA abinda zasu ci
Sosai a yanzu take buƙatar abinda zata sanya a bakin ta koda kuwa bazai mata daɗi bane, sabida tsaban yunwan da a yanzu take ji, daƙyar ta’iya buɗe baki tace ma Ramcy ɗin “duk abinda taga yayi mata tace akawo”
Nan kuwa Ramcy taɗau wayan ɗakin tayi musu odan abinci sannan tazauna zaman jiran kawowa, babu jimawa taji ana Nocking taje tabuɗe ta’amso tadawo ta’ajiye akan table ɗin dake tsakiyar ɗakin
“Besty taso muci ga abincin an kawo”.
Shiru RAUDHA tayi, sai kuma daga baya tayunƙura tatashi duk jikin ta babu ƙwari, ga fuskarta a a ɗaure kamar bata taɓa yin walwala ba
Sai a lokacin ne Ramcy takula tatambaye ta
“Besty lafiya wai meke damun ki ko kan ne?”
Girgiza mata kai kawai tayi tamiƙe tadawo kusa da ita da take zaune saman sofa, bata yi magana ba har suka soma cin abincin
Bayan sun gama ne tamiƙe tanufi Toilet tayi wanka, tana fitowa wayan Ramcy yasoma ringing
Ɗaukan wayan tayi taduba sannan taɗago tana kallon RAUDHA tace “Sojan nan ne da nabashi Number yake kira’.
RAUDHA batace uffan ba sai buɗe Trollyn ta da tayi tana ciro kayan da zata saka
Har wayan tatsinke aka sake kira amma batace komi ba, ita kuma Ramcy bata amsa ba, sai da yayi 3missed call kafin yadena kira
A lokacin har RAUDHA tagama saka kayan ta na barci riga da wando Three qweater farare masu taushi sosai, sai time ɗin takalli Ramcy tace “ki cire layin ki sanja wani”.
Ramcy tasan me take nufi don haka tabuɗe wayan tacire layin tabar ɗaya simcard ɗin ciki, karyawa tayi tazubar sannan taci gaba da latsa wayan ta
Dama Numban ne kuma taba ma wanda suka haɗu a partyn Shatu
Kwanciya RAUDHA tayi tajuya bayan ta tana lumshe idanuwan ta
Itama Ramcy bata wani daɗe ba tazo takwanta nan da nan barci yafige ta
RAUDHA tana nan kwance amma barcin yakasa ɗaukan ta, takaicin Sojan da sukayi karo duk ya addabi zuciyarta, daƙyar tayi barci bayan ta haɗiye ƙwayoyin ta.
Share this
[ad_2]