RAUDHA Page 1 to 10

“To ai tsoro halas ne, wanga buga ƙofa aradun Allah kiris yarage natsure”.
Saude in banda dariya babu abunda take mata, itama ɗin dariyan take yi suka nufi ɗakin su suna maida maganar
Gaba ɗaya sai da tagama hargitsa ɗakin kafin tanufi Fridge tajido Wine???? tazauna nan ƙasa tasoma kwankwaɗa, sha take yi amma hawaye na kwaranya a idanuwan ta, kawai hango yanda Jawad Yakamata yadunga naushin ta a fuska take yi, abinda ba’a taɓa mata ba koda a mafarki, don ita tunda tataso babu wanda yataɓa ɗaukan hannu yabuge ta a iya tsawon rayuwan ta sai shi, sosai take zub da hawaye duk jinin hancin ta da bakinta da suka fashe ya haɗe da ruwan hawayen ta sun yi mata caɓe-caɓe a face, kuma bata damu ba illa kwankwaɗan giyar da take yi, batasan sanda tashanye kwalba biyar ba don bata cikin hankalin ta, kuma hakan be taɓa faruwa ba don iyakacin ta kwalba biyu-uku bata wuce haka, anan tazube takwanta tana kwarara amai kamar zata zubo da hanjin cikin ta, daga ƙarshe barci ne yakwashe ta bayan ta gama surutan ta.
[11/13/2020, 3:14 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????
????????????????????
*RAUDHA*
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????????????????
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma’il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️ ~What’sapp Number 07065334256~
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
.
*NOT EDITED* ___________________________????
*SEASON FIVE*
_______????Hasken ranan da yashigo ta windon ɗakinta ne yabugi kyakykyawar fuskarta da yakumbura yayi jazur, hakan yasaka tasoma motsa lumsassun idanuwan ta tana son buɗe wa, daƙyar ta’iya buɗe su sai kuma tamayar tarufe tana me saka hannaye biyu takama kanta sakamakon mugun sara mata da yake yi, ta ɗau tsawon mintuna 10 kafin tasake yunƙurin buɗe idanun, sosai suka sauya kala sukayi ja har wani yalo-yalo suke yi sabida tsaban rinewa, ahankali tasoma motsa jikin ta tana bin ɗakin da kallo, nan taganta cikin aman da tayi tai dame-dame aciki, fuskarta kuma gaba ɗaya ya bushe da jini, abun da yafaru da ita jiya ne yadawo mata ƙwaƙwalwa tayi saurin runtse idanu tana jin zuciyar ta na tafarfasa, batasan iya lokacin da taɗauka ahaka ba kafin tasoma yunƙurin tashi, daƙyar take iya motsawa sakamakon tsamin da jikinta yayi mata sabida kwanciyar da tayi a ƙasa wanda bata saba hakan ba, miƙewa tayi tashige Toilet takunna shower tatsaya ruwan na dukan ta batare da ta cire kayan jikinta ba, lumshe idanuwan ta tayi tana ɗago kanta ruwan na dukan innocent face ɗin ta, sai da tayi kusan mintuna 15 kafin tacire kayan jikinta tayi wanka tafito ɗaure da towel, gaban gadon ta tanufa tazauna tare da ɗaukan jakanta tazaro wayanta tasoma dubawa, 20missed Call taga an mata, duk na Dad ɗinta ne sai kuma na Ramcy tare da Suhaib, miƙewa tayi riƙe da wayan a hannu tafito cikin ɗakin, ahankali take taka Steps ɗin benen tana saukowa, gab da zata isa ƙasa Larai tafito daga ɗakin su, tana ganin ta dasauri taduƙa tana gaishe ta, fuskar RAUDHA babu walwala tabi ta da kallo kana tace
“Kishiga ɗakina ki gyara min”.
“To Hajiya”. Cewar Larai tana sake rissina mata
Direct ita kuma RAUDHA cikin parlour’n tanufa tashige cikin luntsuma-luntsuman kujeran tazauna, wayanta tasoma latsawa takira Dad ɗin ta, ringing ɗaya yaɗauka cike da matuƙar damuwa a muryan sa yace
“Sweetheart Ina kika shige ne nayi ta kiran ki baki anwer ba? Lafiya dai ko?”
Cikin muryan ta da yasake dishewa sabida kwanan tyles da tayi tace “Daddy lafiya lau ban tashi daga barci bane”.
Ajiyan zuciya me ƙarfi Daddy yasaki kana yace “har naji daɗi nayi tunanin ko babu lafiya ne gaba ɗaya hankalina ya tashi”.
Shafa kanta kawai tayi bata iya cewa komi ba
“But me yasami muryan ki naji baya fita sosai?”
Shanyayyun idanun ta tasake warewa tana jan hanci cike da jin zafi tace “Daddy a ƙasa na kwana”.
“Subhanallah.. Why dear? Kinsan bana Son wani ciwo yakamaki fa”.
Nan ma shiru tayi don bata son yawan magana sabida zafin da laɓɓan ta ke mata, ga kuma hancin ta dake zugi
Daddy yasake cewa “Sweetheart bari zan kira doctor Sadeeq sai yaduba ki don nasan mura ne yakama ki”.
“A’a Daddy bana so”.
Daddy be sake matsa mata ba don yasan halinta sai ce mata yayi “zai sake kiran ta yanzu yana aiki a office ne” daga haka sukayi sallama ta’ajiye wayan takwanta
Tana nan kwance idanuwan ta a lumshe Larai tadawo tasanar mata “ta gama” hakan yasaka tatashi tanufi ɗakin nata tashirya cikin gajeren wando yellow da yatsaya mata iya cinya, wata ƴar yaloluwar farar Vest tasaka tafaɗa kan gado batare da ta shafa koda Lotions bane a jikin ta sabida ko kaɗan bata jin ƙarfin jikin nata, har alokacin giyar da tasha be gama sakin ta gaba ɗaya ba don daƙyar take iya buɗe lumsassun manyan idanuwan ta, hannu tasanya tana shafa laɓɓan ta zuwa wajen hancin ta tana runtse idanu, ba wani ciwo taji ba kawai haɓo ne amma yanda take nuna rakin ta zakayi tunanin dagaske ɗin ciwo yaji mata, tana nan kwance Saude tashigo tasanar mata “Ramcy tana jiran ta a parlour” bata ɗago kai ba tace da ita
“Kice tashigo”.
Juyawa Saude tayi tafice taje tasanar wa Ramcy saƙon ta, sai gata taturo ƙofan tashigo idanunta akan RAUDHA da har yanzu take kwance idanunta a rufe, wajen gadon tanufa tazauna agefe tana ci gaba da kallonta tace
“Besty lafiya meke damun ki?” Tayi maganar ne cike da kulawa
Shiru RAUDHA tayi kuma bata buɗe idanu ba bare takalle ta, Ramcy bata damu ba don tasan halin ƙawar tata sai sake cewa tayi
“Nayi ta kiran wayanki baki ɗauka ba shine nataho in duba ki, duk abinda yafaru adaren jiya ya ɗaga min hankali sosai”.
Tana ajiye maganar ta RAUDHA tabuɗe kumburarrun idanunta da har yanzu suke a rine takalli Ramcy, fuskarta babu ko ɗigon fara’a hakan yasaka hankalin Ramcy yasake tashi, cike da son rarrashin ta tace
“Don Allah kiyi haƙuri da abinda yafaru karki saka damuwa acikin ranki, duk abinda yafaru yarigada ya wuce bana Son Inga..”
“Wanene shi?” Cewar RAUDHA tana katse mata maganarta da faɗan hakan
Shiru Ramcy tayi tana kallon ta, itama ɗin idanun ta akanta suke tana jiran amsar ta
“Bansan shi ba Gaskiya don baƙo ne awajen”.
Shiru ne yagibta a tsakanin su naɗan wani lokaci kafin RAUDHA tatashi zaune tana kawar da kanta daga kallon Ramcy ɗin tace
“Ina son ki binciko min ko shi wanene, ina son insan komi daga gare shi”.
Sai tajuyo da kallon ta ga Ramcy taci gaba da faɗin
“Dole zan ɗau fansar abinda yayi min bazan taɓa yafe masa ba, zan nuna masa nafi ƙarfin sa, ki tabbatar kin binciko shi ɗin waye na baki nan da kwana biyu”.
Daga haka tamiƙe tashige Toilet tabar Ramcy anan tana Bin ta da kallo.
????????????????????????????????
Alh. El.Mustapha Makamashi wani hamshaƙin me kuɗin gaske ne wanda duk faɗin garin Kaduna da kewaye babu wanda be san shi ba, babban ɗan Siyasa ne da yayi ƙaurin suna ako ina, ya riƙe muƙamai iri da kala har zuwa matakin gwamna, alokacin da yanemi takarar gwamnan Kaduna Allah be sa yaci ba sakamakon juyin mulki da akayi masa, wannan yasaka yafita siyasa gaba ɗaya yakoma harkan kasuwanci tsundum, Asalinsa Bazazzage ne kuma anan Zaria yake zaune, iyayen sa sun daɗe da rasuwa a hannun kawun sa yataso, shima Kawun nasa yanzu haka ya daɗe da rasuwa, yana da gidajen man fetur sun fi biyar agari mabanbanta acikin Nigeria, kuma yana da Companin haɗa auduga agarin Abuja wanda Suhaib ne ke kula dashi, Allah ya albarkace sa da yara biyu rak Suhaib da RAUDHA, tun RAUDHA na ƴar shekara biyar a duniya Allah ya’amshi ran mahaifiyar su, kuma har alokacin Daddy yaƙi aure sabida ƙaunar da yake ma Matarsa.