RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 1 to 10

“Bana Son in ganki cikin damuwa ƙawata ki saki ranki”. Cewar RAUDHA da tabuɗe idanu tana kallon Ramcy tana me yalwata Innocent face ɗin ta da murmushi

Tasan da cewa tana son Ramcy sosai aranta, haka kawai jinin su yahaɗu shiyasa taɗauke ta tamkar wata ƴar uwanta batare da taji ƙyamarta a matsayin ita ɗin ƴar talaka bace, tayi friends daban-daban ƴaƴan masu kuɗi irin ta amma duk ta watsar dasu duk a dalilin rashin son takura wa kanta, a cewar ta yawan tara friends trouble ne agare ta, tafi son rayuwa ita kaɗai hakan yafi mata daɗi tunda a haka tatashi

Ramcy dai bata iya cewa komi ba sai miƙewa da tayi tana shirin tafiya tace “Besty Ni zan tafi”.

Miƙewa itama RAUDHA tayi tana nufan hanyan dainning tace “kizo muci abinci sai ki tafi”.

Babu musu Ramcy tabi bayan ta suka zauna a dainning table ɗin, tun ɗazu Saude tagama abincin tajera kuma RAUDHAN na kallo taƙi zuwa taci sai yanzu da taga dama, ita dama cin abincin ta sai taga dama ne, don watarana ma bata ci gaba ɗaya sai dai Saude tazo taɗauke shi yanda ta’ajiye, in kuwa zataci baya wuce sau ɗaya a rana ko biyu, kayan ƙwalan da maƙulashe shine abinda take so, shiyasa bata rabo dasu Chaculates, buskit e.t.c

Ramcy tayi saving ɗin su suka soma cin abincin, babu wanda ke magana cikin su har sanda suka gama, RAUDHA tasoma tashi tana share bakinta da tissue tawuce cikin parlour, ita kuwa Ramcy sai da tacika cikin ta tayi nak kafin tamiƙe tataho wajen ta tana cewa

“To zan tafi Besty”.

“Ok”. Ta’amsa mata ataƙaice tana latsa wayanta

Hanyan ƙofa tanufa tafice cikin parlour’n

Tana fita itama tatashi tanufi ɗakin ta, Direct gaban drower tanufa tabuɗe taciri tables tawatsa abaki takoma kan gado takwanta tana tsotso, wayanta ta’ajiye tana lumshe idanuwan ta, shiru tayi tana tunani aranta, ta ɗau tsawon lokaci ahaka kafin tabuɗe idanunta da ayanzu suka juye zuwa Red, Remote taɗauka dake kan drower daga kwancen takunna t.v, Bom t.v tasaka da ake waƙa tana me ƙure Volume, tuni ko ina ya game da ƙarar music ɗin, kwanciyar ta tagyara tana me rufe idanuwanta cike da kasala, ahaka har barci yasure ta.

     Sai bayan magriba tafarka, daƙyar tatashi tana sakin hamma tanufi Toilet, wanke fuskarta tayi tafito tafaɗa kan kujera, lumsassun idon ta take ta sake lumshewa tana yamutsa fuska, gaba ɗaya jikin ta ciwo yake mata musamman ma kanta, riƙe kan tayi da hannu tana jan siririn tsaki tamiƙe taɗau Remote takashe plasman, wayan ta dake ringing taɗauka ganin sunan Ramcy, nan Ramcy take tambayan ta “yau zasuje Club ne?” RAUDHA tace “baza su je ba”. Daga haka takashe wayan ta’ajiye, ita dama tana da zuciya idan har tayi fushi da abu to ta barsa kenan har abada, tuni ta cire ran komawa Club ɗin sai dai su nemi wani kuma

Miƙewa tayi tashige Toilet taɗauro alwala tafito, zama tayi tasoma lissafin sallan da ake bin ta na wajen kwana biyu kenan, sai da tagama lissafin ta sannan tamiƙe taɗau Hijabin sallanta tazumbula har ƙasa tasoma gabatarwa, gaba ɗaya sai da talissafo sallan nan kafin tasallame, bata tsaya wani yin addu’a ba tamiƙe tasauya kaya zuwa na barci tahaye kan gado tarufe jikinta da bargo taɗau wayan ta tasoma chatting, sai da taraba dare kafin takwanta.

Washe gari ƙarfe 11:30am. Tatashi, wanka tayi tasaka ɗan guntun wando iya cinyan ta baƙi me baza a ƙasan, sannan tasaka have-Vest ɗin wandon shima baƙi, Ash colour ɗin Jarket mara nauyi taɗaura asaman have-Vest ɗin wanda yatsaya mata iya setting wandon, tafeshe jikinta da turare tare da ɗaure gashinta da jelan a tsakiyar kai, tasaka Room Slippers taɗau wayan ta tafito parlour, directly kan dainning table tanufa taja kujera tazauna, Tea cup tahaɗa me zafi tasoma sipping tana faman latsa waya

Wajen mintuna 30 tana nan zaune kafin taɗago kanta tana ƙwala kiran masu aiki cikin dashashshiyar muryan ta, shiru babu wanda yafito don haka tamaida kanta taci gaba da danna wayan ta, sai da tagama abinda take yi sannan tamiƙe tadoshi hanyan ɗakin su Saude, tana zuwa tahankaɗa ƙofan tashige.

.

_Yanzu cakwakiyan yasoma_

_plz ku ƙara yawan comment don Allah, karku manta da danna *Vote, share.*

[11/14/2020, 7:42 AM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

  *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR*✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON SEVEN*

_______????Su Saude dake zaune suna kallo a wayan Larai suka ɗago kai dasauri suna kallon RAUDHA, ko waccen su nan da nan tashiga hankalin ta coz sun san bata shigowa cikin ɗakin su idan har ba wani laifi sukayi mata ba, shanyayyun manyan idanuwan ta tasauke akan su tana bin su da kallo, sai da tagama ƙare musu kallo cike da isa tace

“Uban me kuke yi da har zan kira ku ku kasa amsa min?”

Zuru-zuru sukayi da ido suna kallon ta, sai Larai ne tayi ƙarfin cewa

“Kiyi haƙuri Hajiya wlh bamu ji bane”.

Dogon tsaki taja tace “ki shirya kizo in aike ki supper market”.

Idanunta dake kan Saude shiyasa tagane da ita take yi

“To ranki yadaɗe”. Cewar Saude tana miƙewa dasauri

Ita kuwa juyawa tayi tafice tanufi ɗakin ta, bata daɗe da zama ba Saude tashigo, kuɗi tamiƙa mata tafaɗa mata abinda zata siyo mata tafice, wayan ta taɗauka takira Ramcy, ringing ɗaya taɗauka

“Ramcy kibar aikin nan kawai”.

Cike da mamaki Ramcy tace “meyasa?”

RAUDHA tace “na sauya shawara ne, zan kira ki anjima yanzu zan fita bye”.

Ƙitt takashe wayan ta’ajiye, tashi tayi taɗauko Socks baƙi tasaka, dogo ne da yatsaya mata har gwiwa tasanya Hill shoes black me igiya, wayan ta tasake ɗauka takira Mahaifin ta yana ɗauka tace

“Daddy Ina buƙatar kuɗi”.

“My dear me zakiyi da kuɗi haka?”

“Dad Kai dai kabani akwai abinda zan yi dashi ne”. Tafaɗa a shagwaɓe

“Ok to bari in tura miki”.

Tana katse kiran babu daɗewa taji Alarm ya shigo, HangBag ɗin ta taɗauka tafice, dasauri-sauri take taka Steps har tasauka tabar Parlour’n, a compound tatsaya tana gyara ɗan silin gashin ta da yasauko mata wajen ido, jakan ta tabuɗe taciro wani faskeken Eyeglasess baƙi tasaka, ko kaɗan bataji ɗar ɗin fita da kayan jikin ta ba don tarigada tasaba, sai dai ta zuge zeey ɗin Jarket ɗin  ta rufe iya cikin ta dake waje,  mota tashiga tabar gidan.

      Bank ???? tafara zuwa taciri kuɗi sannan tanufi police station????, tana yin parcking tafito takulle motan, gaba ɗaya duk mutanen dake haraban Station ɗin babu wanda idon sa be kai kanta ba kuma duk kallon da ake mata ba wanda yake mata kallon musulma sai dai waɗanda suka san ita ɗin wacece, kallon ta kawai ake yi ita kuwa ko ajikin ta tanufi ciki cike da tafiyan ta me burgewa

Tana shiga duk ma’aikatan dake zaune wajen suka yi mata caa da idanu, daga masu haɗiyan yamu sai masu sakin baki kamar zasu cinye ta, bata kalli kowa ba tanufi Office ɗin DPO kanta tsaye kuma duk acikin su babu wanda yayi yunƙurin yahana ta

Nocking tayi aka bata damar shiga tatura ƙofan tashige, DPO dake duba wasu files a gaban sa yaɗago kai, dasauri kuma yatashi tsaye yana faɗaɗa fuskarsa da fara’a yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button