RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 1 to 10

“A ah Ranki yadaɗe kece yau a office ɗin mu? Barka da zuwa zauna mana”.

Babu musu tazauna tana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya taɗaura HangBag ɗin ta a jikinta, shima komawa yayi yazauna yana sake mata Barka da zuwa, sannan yaƙara dacewa

“Ranki yadaɗe da kanki yau Alhaji ya aiko?”

Yana nufin mahaifin ta sabida mutumin sa ne kuma shine yasama masa aiki lokacin da yake ganiyan Siyasan shi, shiyasa duk abinda Daddy yanema awajen sa yana masa da gaggawa sabida albarkacin muƙamin da yaɗaura sa akai

Zare Eyeglasess ɗin ta tayi sai ga kyawawan lumsassun idanuwan ta sun bayyana, cikin muryan ta me daɗi ga kowa tace “No DPO wannan aikina ne”.

DPO dake haɗiyar yawu kamar wanda zai cinye ta sabida kafe ta da idanu da yayi, yasake washe baki yace “to ranki yadaɗe wani aiki kenan za’a yi miki?”

Murmushi tayi me zautar da mutum kafin tace “Wani yaro nake so ku kama min shi, ina son ku hukunta shi bisa laifin Fyaɗe da yai ninyan min, sannan bana son ku bada belin shi har sai anzo an bani haƙuri”.

“Ai baki da damuwa ranki yadaɗe duk abinda kikace shi za’ayi, aina yaron yake?”

Kamar yanda Ramcy tasanar da ita bayani akan sa haka itama tafaɗa masa, sannan taƙara dacewa “wannan maganan Ni da kai ne DPO, ko Daddyna bana son kasanar masa”.

Sai kuma tabuɗe Jakan ta taciro maƙudan kuɗi ta’ajiye masa batare da ta furta komi ba, shi kuwa cikin tsananin murna yaɗau kuɗin yana kallo, sai kuma yamaida idanun sa kan ta yana lanɗe baki, Allah ya sani yafi buƙatar ta akan kuɗin nan, duk da yawan kuɗin da ace zata riƙe tabashi kanta da yaji daɗi fiye da bashi kuɗin da tayi, sai dai bazai taɓa iya nuna mata maitan sa ba gudun samun matsala, don yasan aikin sa ma da yake taƙama dashi zai iya rasa shi, yasan cewa rijiya ba wajen wasan makaho bane, yanzu sai yajawo ma kansa gobarar da bazai taɓa iya kashe sa ba

Muryan RAUDHA yakatse masa tunanin sa, yayi firgigit yana kallon ta da har ta rigada ta tashi, shima dasauri yatashi yana cewa

“Ai ranki yadaɗe yanzu ma zamuje har dani don mu soma miki aikin ki da wuri”.

Murmushi tayi tace “nima ina son in bi ku”.

“Ok babu matsala muje”. Cewar DPO yana yin gaba dasauri kamar ana hankaɗa shi yabuɗe mata ƙofa

Sai da tafice sannan yabi bayan ta, tare da wasu ma’aikatan su biyar suka tafi, motan su ne agaba nata abaya suka nufi anguwan su Jawad

Suna zuwa da tambaya aka nuna musu shagon sa, huɗu daga cikin ƴan sandan ne suka shiga shagon, babu zato babu tsammani Jawad dake aikin zanen sa yaji anyi ram dashi, dasauri yajuyo yana kallon kwalawan dake tsaye kan sa biyu sun riƙe sa, miƙewa yayi jiki na rawa yasoma tambayan su abinda yayi

Ɗaya daga ciki yabuge masa baki yace “idan mukaje zakaji wuce muje”.

Turjiya yasoma nuna musu suka hangaɗa shi sukayo waje dashi, lokacin ne Deeni abokin sa yaƙariso wajen don har an kai masa rahoton ga ƴan sanda can a shagon Jawad, dayake shima Shagon sa yana layin anguwan ne, ganin za’ayi wajen mota dashi Deeni yayi saurin zuwa yana cewa

“Dan Allah ranku yadaɗe me yayi zaku tafi dashi?”

Wani kallo ɗan sandan cikin su yayi masa yace “idan kuka biyo mu Office zakuji”.

Jama’a sun taru ana ta tambayan ba’asi amma firr ƴan sandan nan sun ƙi magana sai son tura Jawad suke acikin mota, shi kuma ya dage akan lallai bazai shiga ba tunda yasan be yi komi ba duk da akwai tsoro a tattare dashi

 Lokacin DPO yafito a mota yana cewa “wai ya gagare ku ne?”

RAUDHA dake cikin mota zaune tana kallon duk abinda ake yi sai faman cije laɓɓa take yi tana sakin murmushi, sai da taga an saka sa cikin mota sannan tafito tana gyara zaman Eyeglasess ɗin ta, nufan wajen tayi cikin tafiyan ta me ɗaukan hankali, nan kuwa sauran mutane suka maida kallon su gare ta har sun manta me ma ake yi

Deeni tunda yahango ta yasha jinin jikin sa, dama ya rina aransa dole ne abokin sa yafuskanci hukunci duk ranan da tajuyo kansa, shi yarigada yasanta yasan waye ita sabida ya daɗe yana zuwa Club ɗin

Tana zuwa wajen ƴan sandan suka matsa mata hanya ta’isa jikin motan tana kallon Jawad da shima yake kallon ta, sai dai nashi kallon na rashin sani ne don ba wani sanin ta yayi ba, bare cikin club ɗin akwai duhu sosai, cire Eyeglasess ɗin ta tayi tana sake ƙare masa kallo tana murmusawa, batace komi ba  kuma takalli DPO tace

“Daga nan zan wuce gida DPO, ku gana masa azaba sosai bana son ko kaɗan ku raga masa”.

Daga haka tajuya batare da tasake bi takan su ba tanufi motan ta tashige taja tabar musu ƙura nan, ƴan sandan har suka shige su ma suka ja tasu motan Jawad kallon motan ta yake yi, har alokacin ƙwaƙwalwan sa be kawo masa inda yasanta ba duk da kuwa yaso yagane muryan, shi dai mamaki da yarufe sa ne yasa yamanta ahalin da yake ciki har suka tafi dashi

Jama’an wajen kuwa sai mayar da zance suke yi sun kasa sanin meke faruwa, wasu kuwa har sun rigada sun bata laifi sai zagin ta suke yi suna cewa “dama haka ƴaƴan masu kuɗi suke, don sunga sunfi ƙarfin mutum sai su nemi su takasa koda laifi kayi musu a rashin sani” wasu kuma wajen Deeni suka nufa suna tambayan ba’asi, amma shi hankalin sa duk atashe yake be saurare su ba yayi hanyan gidan su Jawad ɗin, wasu daga ciki suka rufa masa baya don jin ƙwaƙwaf.

      Har ta kai anguwan su sai kuma tajuya kan Motan tanufi gidan su Ramcy, a bakin ƙofar gidan tayi parcking tafito tarufe motan tashige cikin gidan kanta tsaye

Gidan madaidaici ne me ɗakuna biyar dasu Toilet da kichen, gidan yana da kyau irin dai na masu rufin asiri, Mahaifiyar Ramcy ta daɗe da rasuwa sai Amaryan Baban su take riƙe ta, su huɗu ne wajen mahaifiyar tasu, biyu maza sai ɗaya mace da tayi aure sannan ita Auta, Mahaifin su Dattijo ne sosai kuma itama Amaryan da ya’auro dattijuwa ne don bata taɓa haihuwa ba

 Kasancewar Baban su na tafiye tafiye yana sana’ar Gwari wannan yasaka Ramcy take yin duk abinda taga dama, don bata jin tsoron yayyin nata bare Amaryan Baban su

RAUDHA na shiga tanufi ɗakin Ramcy ɗin tabuɗe labule tashige, ɗakin yayi kyau sosai dai-dai na budurwa me ji da kanta, kuma duk RAUDHA ce tasiyan mata duk abinda ke cikin ɗakin, har ta dana Amaryan Baban nasu sai da tasauya mata kayan ɗaki, shiyasa babu wanda be san ta ba agidan, kuma hakan yasaka wani lokacin basa matsa ma Ramcy idan sukaga ta fita don sun san can wajen RAUDHA take zuwa

Babu kowa cikin ɗakin sai tatsaya tana ƙare wa ɗakin kallo na tsawon daƙiƙu sannan tanufi kan katifa tafaɗa har da takalmin ta da bata cire ba, numfashi taja me ƙarfi tana lumshe kyawawan idanuwan ta.

Ramcy ce tashigo cikin ɗakin, ganin RAUDHA abun ya bata mamaki, dasauri taƙarisa kusa da ita cike da farin ciki tace

“Besty yaushe kikazo?”

Lokacin ne RAUDHA tabuɗe shanyayyun idanuwan ta tasauke kan Ramcy ɗin, memakon ta’amsa mata tambayan ta sai cewa tayi “ina kika shiga nashigo bakya nan?”

Ramcy tace “na shiga bayi ne wlh”.

“Ok”. Tafaɗa tana ɗauke kanta daga kallon Ramcy ɗin

“Besty me zakici in kawo miki?”

“Babu”. Tafaɗa ataƙaice tana tashi zaune

Ramcy tace “yanzu dama nake tunanin kiran ki ashe zakizo, zan kira ki in sanar miki bikin da nace miki zani a Kaduna ya matso”.

Kallon ta RAUDHA tayi kamar baza tace komi ba sai kuma tace “yaushe ne kenan?”

“Wannan satin amma sai ana gobe zan tafi”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button