SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

????G. W. A????
GASKIYA DOKIN ƘARFE ????????

Writing by
khadeejatu Muhammad

Dedicated by Umaima Aliu

PAGE1⃣5⃣

Bismillahir Rahmanin Raheem.

Dai-dai lokacin Samha tasawo kai cikin falon ta tsaya waje d’aya ta daskare cikin rawan murya tace, “AU…AUU….AURE kuma Yaya? “

Harara ya galla mata cikin kakkausar murya yace, “dake nake magana, koh dashi ,baki da kunya koh ,manya na magana kina sa baki koh toh zan gyara miki zama”

k’wafa yayi yadubi Baba yana murmushi,sosa k’eya yake cikin kwantacciyar murya yace,

“Baba kayi haƙuri da shishigin danayi maka ban nema umurnin ka ba ko izini daga gareka”

ya d’an nisa kafin yaci gaba da fad’in,

“Baba naga kana buk’atar kulawa sosai wanda Samha bazata iya bakaba kuma tayi k’arama da kula dakai dole sai babbar mace dattijuwa”

shiru yayi na d’an dak’ik’a kafi yaci gaba da fad’in,

“Baba baka ce komai ba,ko baka farinciki da kyautar dana mane”

Nisawa Malan Sale yayi tare da fad’in,

“Salmanu banda bakin gode maka a gaskiya, ka kaini asbiti an dubani anbani kulawa mai kyau,sannan ka kula dani da y’ata kabamu muhalli mai kyawu”

shiru yayi nakusan dak’ik’a biyar kafin yaci gaba da fad’in,

” gashi kuma kamin aure,Salmanu ba auren nike gudu ba kasan dai awannan lalurar da nike ciki ba macen da zata zauna dani ban iya komai saide tai ta jigila dani fitsari nan kashi nan komai sai anmin hatta abinci sai ansa min abaki , wanka sai anmin ina ganin bawanda zai bani kulawa kamar yan da Samha tah zata bani sai kai da Allah yakawo mana cikin rayuwa dan ka taimake mu Salmanu Allah yama albarka”.

“Ameen Baba…ka kwantar ta da hankalinka bazakai dana sani ba inshaallahu zaka sameta cikin mata salihai masu kula da miji masu tattalin miji,masu san ganin farin cikin miji”

murmushi Baba yayi yace, “Salmanu kafaɗa mata lalurata koh? dan kartazo taga ba lafiyayye ba ta gudu ta barni”

murmushi Salman yayi yace, ” Baba kenan karka damu zata kula dakai sosai da sosai”

shiru na d’an lokuta sukayi kafin Baba yakatse shirun da cewa, “infa Larai taji akwai bala’i”

murmushi Salman yayi azuciyar shi cewa yayi ai na tabbata Larai bata kokamo k’afar amaryanka ba wajen fitina koh don ta gyara mata zama shiyasa na zab’ota.

“kayi shiru Salmanu”

cewar Baba.

murmushi yak’ara yi yace, “Baba karka damu da wan nan kasan duk masifar mace kafin ayi ne bayan anyi koh bayanda zatayi dole dole ta hak’ura,alokacin ne itama zata nema hanyar da zata faranta ma”

“Hakane Salmanu Allah yamana jagora.

“Ameen Baba”

ita koh Samha tana nan daskare waje d’aya kanta a k’asa tana wasa da zoben hannunta tarasa ma wani tinani zatayi akan wannan bak’on al’amarin,duk hiran dasuke bama taji balle ta fahimta.

Salman ne yace, “toh Malama kin tsaya ma mutane akai kamar wata ƴar sanda,in zaki zauna ki zauna in zaki fita ki fice”

sum-sum ta samu kujera ta zauna kanta a k’asa cike da kunya.

Salman koh k’ara duban Baba yayi kafin yace, “Baba ina neman wata alfarma kuma a wurinka idan ba damuwa”

Baba shima da duban Salman d’in yake yace,

” Salmanu kafaɗa nama alk’awari ba irin alfarman da zaka naima ban makashi ba matukar bai sab’ama addini ba kuma bai gagare ni ba”

“bai sab’a ba Baba ba, kuma nasan bazai gagareka ba, ba komai bane Baba tunda kasami mai kula dakai zan tafi da Samha gidanmu taci gaba da zama kaga nan babu inda zata zauna”

Samha arazane tad’ago ta zuba masa ido.

Shima kallonta yake ganin kallon-kallon da take masa yasa shi saurin d’auke kai yamaida kallon shi wajen Baba.

Shima Baban zuba masa ido yayi acikin ransa yana tunanin komai Salmanu yanema ba zan iya hana shiba aciki koh da kuwa auran Samha ne.

A zahiri ko murmushi yasaki yace ,

“Salmanu nabaka amanar Samha tah ka kulamin da ita kamar yanda zaka kula da kanka ko bayan raina nabaka ita amana har ka aurar da ita ga wanda kaga hankalin ka ya kwanta dashi Salmanu”

zumbur tamik’e fuskan ta duk ta jik’e da hawaye tace,

” haba Baba ya za’ayi kabada ni kyauta ashe zaka iya rabuwa dani sam Babana bazan iya tafiya in barka ba koda kuwa aure nayi saidai mijin ya dawo da kai kusa dani inba haka ba bazan aure shiba”

sakin baki Baba yayi cike da mamaki kafin yace,

” Samha ashe zaki iyayin butulci,ashe zaki iya maida alkhairi sharri,indai ni na haifeki kuma na isa dake kibi umurnina ki koma gidan su Salmanu………”

kuyi manage da wanga.

vote
comments
nd
share
[11/21, 7:10 PM] Sumayya: ????????????????????????????
????????????????????
????????????
????

      ???? *SAMHA* ????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira }.

????G. W. A????
GASKIYA DOKIN ƘARFE ????????

Writing by
khadeejatu Muhammad

Dedicated by Umaima Aliu

PAGE1⃣6⃣

Bismillahir Rahmanin Raheem.

Samha ashe zaki iyayin butulci,ashe zaki iya maida alkhairi sharri,indai ni na haifeki kuma na isa dake kibi umarnina ki koma gidan su Salmanu”

Kuka Samha ta k’ara fashe dashi,ta zauna a k’asa tafara tirje -tirje kamar k’aramar yarinya.

Malan Sale koh kauda kai yayi cike da haushi.

Salman koh ido ya zuba mata azuciyar shi koh mamakin sangar cewar yarinyar nan yake,ranshine yafara b’aci,lumshe ido yayi yabud’e baisan sanda ya daka mata tsawa ba yace” keeeeeeeeee miye haka kinta sa mu a gaba da ihu akan zakibini ne kike wannan kukan kamar za’a kaiki lahira to wallahi ko ki mana shiru ko in tattaka ki”

Tsittt tayi ta matse kukan ta don matuk’a ya bata tsoro.

Baba koh ko magana yakasa sabida haushi da takaici yaune ranan farko arayuwar shi dayafara jin haushin mafi soyuwar ‘yar sa,kome yace mata bata tsallake wa,gashi yau tayi masa abinda
baiyi tsammani ba.

Salman ne ya k’ara duban ta yace “kinga abin da kikai yajawo ran mahaifinki ya ‘baci,kinsa illar fushin mahaifi kuwa Samha? ki gaggauta tashi kizo ki duk’a da guywoyinki kine mi afuwan sa”

Jikinta ne yayi sanyi da abinda taji yace da jan gwiwa ta k’arasa inda Baba yake ta kamo hannunsa me lafiya tarik’e gammm tafashe da wani sabon kuka.

Salman koh takaici yakama shi ya k’ara daka mata tsawa yace “keeee kimana shiru inbazaki abinda nasa kiba kifita mana anan kinsa mu a gaba kina ta kuka kamar gidan mutuwa”

Saurin had’iye kukan tayi tare da rintsa ido aranta tace mugu azzalimi me raba d’a da mahaifin sa”batasan magan zuci yafito fili ba,saidataji yace “me kikace

Yawan comments dinku shine k’warin gwiwar writers.
[11/21, 7:11 PM] Sumayya: ????????????????????????????
????????????????????
????????????
????

      ???? *SAMHA* ????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira }.

????G. W. A????
GASKIYA DOKIN ƘARFE ????????

Writing by
khadeejatu Muhammad

Dedicated by lovely Daughter Nanah khadeejatou

PAGE1⃣7⃣

Bismillahir Rahmanin Raheem

Saurin had’iye kukan ta tayi da rintsa ido aranta tace mugu azzalimi,me raba d’a da mahaifin sa ” batasan magan zuci yafito fili ba.

Sai taji yace “me kike cewa?

Waro ido tayi ta zuba masa su.

Shima shi ita yake kallo,take wani abu yaji ya sarke masa wiya tare da jin wani bugun zuciya,saurin kauda ido yayi tare da lumshe su.

Duban baba tayi ta ruk’o hannun sa a san yaye tace “Babana dan Allah kayi hak’uri kayafe min,na amince zan bishi in dai hakan zai zamo sanadiyan farin ciki ka Babana”ta k’arashe maganan tana murmushi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button