SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dai-dai lokacin Sumayyah yarinyar Hajja Ganah ta fito ganin Samha tsaye tana niyan Kiran waya yasa ta k’ara so in da suke fuska d’auke da murmushi tace,”kece amaryan Salman d’an gidan Mama Lailah?

D’agowa tayi ta dube ta yarinya ce batafi sa’an taba saide ita black beauty ce tana da d’an k’iba madai dai ciya ce ta murmushi ita ma tace, “eh nice”……….!

Wolle comment dinku yayi kasa sosai????????????????
[11/23, 8:04 PM] Sumayya: ????????????????????????????????????
????????????????????
????????
????

????SAMHAA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍????
{ Gaskiya d’aya ce daga k’inta sai b’ata burinmu mu fad’akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}

    ```????G•W•A????```

GASKIYA DOKIN K’ARFE•????????

Written by khadeejatou Muhammad Basskkwace

4⃣1⃣

Dedicated by MY ONE ND ONLY ALHAJI IBRAHIM MUHAMMAD,ALLAH YA K’ARA MA LAFIYA DA NISAN KWANA.)

Bissimillah rahamani raheem

Jikin Dr na rawa yace,”to Malan an gama bani A/N ka in ma transfer”.

Malan Nura ko washe baki yayi yafa ra zay-yano masa numbers din.

Nan take Dr ya tura masa.

Sai da Malan Nura yaga alert kafin yace musu zuwa one week su dawo,tafiya sukai suna masa godiya.

Abin da yaban mamaki bayan Dr ya aje abokin shi,yayi kaman ya shiga gida sai da ya tab-batar Dr ya wuce,ya fito da sauri ya haye mashin.

(Nima ganin haka bin bayan shi nayi)

Abin mamaki bai tsaya ko ina ba sai gidan Malan Nura,kai tsaye cikin gidan yashiga inda matan Malan Nura take,akwance kan kujera na hango shi,shiko Rabi’u da sallama ya shiga.

Malan Nura bai ansa ba illa dariyan da ya shek’e dashi tare da cewa,”haba Rabi’u dawo wa haka da wuri da sai kabari gobe mana”.

Rabi’u shima dariya yake yace,”haba Nura ai abari ya huce shike kawo rabon wani,da sassafe ake kamun fara”.

Nura dariya ya kuma yi tare da cewa, “abokina kasan kan tsiya ina ka samo mana wanan kitsen?

Ta’ba baki yayi kafin yace, “wallahi abokina ne daga na kai Nana budurwa ta asbitin da yake aiki acire mata ciki nan fa muka had’u”.

Malan yace,”amma shi ba k’ara min samna bane,bani account din naka nasa ma kason ka”.

Nan Rabi’u ya fad’a masa ya masa transfer miliyan d’aya da dubu d’ari hud’u.

Rabata dai-dai sukayi.

Sun jima suna hiran Dr kafin sukai sallama Rabi’u ya wuce.

Niko nace Allah ya sawak’a.
Cin amana.

Washa gari kawunan Salman su kazo gidan su Samha don nema ma Salman auren ta,sun sami tarba ta musam-man daga wajen Gwaggo Dija,sun tambaye aure Samha baba ya basu,nan take Alhaji Taheer ya bada kud’in gaisuwa da sadaki naira dubu d’ari uku ,da k’yar Baba ya amsa,basu tafiba saida aka tsaida rana nan da kwana biyar yakama ranan sati me zuwa kenan.

Ko da Alhaji Taheer suka bar gidan su Samha direct gidan su Salman ya nufa,ya tadda Hajiya Lailah ya fad’a mata komi ba k’ara min farin ciki tayi ba,sallama yamata ya tafi.

Nan take ta d’aga wayar ta takira Hajiya Abidah kanwar ta ta shaida mata tace,tana so ta had’o mata akwatina na ban mamaki,suna gama wayar ta kira bab-bar aminiyan ta Hajja Gana tace tana so a gyara mata amaryan d’an ta,ta buk’ata nawa zata biya, Hajja Ganah ta gwada mata bata bukatar komi gare ta.

Cike da farin ciki ta mik’e ta nufi d’akin Samha,akan gado ta iske ta k’wace.

Ganin Mama ne yasa ta tashi da sauri tana fad’in,”sannu Mama”.

Mama tace,”yauwa Daughter,sannuki da hutawa, ki rubuta duk me kike so game da kayan akwati”.

Jimmm tai kamar bazatai magana ba zuciyar ta na mata wani iri, kafin tace, “Mama ko mi kuka ga ya muku kusaya ba matsala”.

Mama dafa kafad’a ta tayi tace,ki shirya yanzu zakije gida ki gaida mahaifinki daganan driver zai d’aukeki ya kaiki gidan Hajja Ganah,don ta fara miki gyara tunda bikin saura kwana biyar”.

Da sauri ta d’ago ta dubi Mama fuska d’auke da ma-maki……..!

GASKIYA BAN GANIN COMMENT KO BA DADI NE LITTAFIN WAI????
[11/23, 8:04 PM] Sumayya: ????????????????????????????????????????????????????????????????
????????????????????
????????
????

???? SAMHA????

WRITTEN BY
Khadeejatou Muhammad Basskkwace.

4⃣4⃣

Dedicated by zee yero, Dr ummiey boko nd Umaima Aliyu

Bissimillahi Rahmani Rahim

Yarinyar tace, “mushiga ciki Mami na jiran ki”.

Jerawa sukai,sumayya sai zuba take mata kamar sun saba.

Itade Samha murmushi kawai take sai eh ko a’a.

Da sallama suka shiga, Hajja Ganah dake kan kujera zaune da fara’a ta amsa tana me mik’ewa tana tarbo Samha tana fad’i, “lale-lale amaryan mu”.

Duk’ar da kai tayi cike da kunya tace,”ina wuni Mami”.

Tace, “lafiya k’alau, yasu Mama ki?

Tace,”lafiya take tana gaishe ki”?

Tace,”ina amsawa”, zaunan da ita kan kujera tayi ta dubi sumayya dake tsaye tace, “kawo mata ruwa”.

Da sauri ta nufi kitchen ta d’auko mata ruwa ta kawo mata.

Zama tayi gefenta sai fara’a take.

Mami tace, “mik’e ki wuce inda zaki karki dameta da surutu”.

Shagwab’e face tayi tace,”na fasa tunda nayi sabuwa k’awa”.

Samha ko murmushi kawai tayi.

Sumayya janta da hira ta keyi kan kace mi Samha harta saki jiki da ita sai hira suke.

Mami ko cewa tayi,inkun gama kikai ta d’akin gyaran jiki”,tana gama fad’a bata jira mi zata ce ba tai shigewan ta ciki.

Nan suka sha hiran su har aka kira magrib d’akin sumayya suka shiga ta nuna mata toilet ta shiga tai alwala fito tayi sallah.

Bayan ta idar da sallah ne Sumayyah tace,suje falo suci abinci.

Fita sukayi suka nufi dining Sumayya ta zuba mata abincin tafara ci.

Itama zama tayi don taci nata.

Suna gamawa suka mik’e d’akin gyaran jiki suka nufa kankujera ta zauna.

Sumayya kuwa d’auko tsumi tayi kala-kala ta fara zuba mata tana Mik’a mata tana sha wani taji dad’i wani ko babu hakanan ta daure tasha,tana cikin sha sai ga Mami ta shigo,zama tayi kan kujera ta jawo wasu robobi wasu ta dama da nono wasu ta dama da madara haka ta rink’a d’irka mata kayan mata kala-kala.

Ta nuna mata ruwan da zata rink’a tsarki dashi da wanda zata sha,tace mata kuma nan d’akin ne wajen kwanan ta kasan cewar komi akwai aciki, saida ta gama bata abin da yaka mata kafin ta fice,ta barsu da Sumayya.

Sumayya ta dibeta tace,”Sis bak’ya wtspp ne ?

Samha ta kalle ta cikin rashin fahimta tace,”menene kuma hakan?

Dariya Sumayyah tayi kafin tace, “charting mana”.

Tace,”niko banyi ban ma iya ba”.

Sumayyah tace,”ban wayar ki in tura miki”.

Tace, “tou” mik’a mata wayan tayi.

Nan Sumayya ta bud’e xender ta tura mata wtspp kawai ta bud’e mata tasata a group guda kusan biyar kafin ta gwada mata yanda zatayi ta bata.

Godiya tayi mata.

K’aran da wayar Sumayya da yayi ne yasa ta ta mik’e tace mata tana zuwa ta fice.

Washe gari bayan sun karya nan Hajja Ganah ta fara mata gyaran jiki yayin da Sumayya ke taya ta har wajen azahar,bayan sunyi Sallah kitchen suka shiga tafara koya mata kalolin abinci iri-iri kan kace me Samha duk ta gane su bayan sun gama suka dawo falo suka ci abinci saida aka kira sallah la’asar kafin suka mik’e don yin sallah.

B’an garan Dr Habeeb kuwa yace yau surprise d’in Lubabatu zaiyi ya je gidan su ba tare da ya mata waya ba,ya isa gidan su dai-dai lokacin sallan magariba anfara kira saida ya tsaya masallacin kusa da gidan su yayi sallah kafin ya fito ya shiga motor shi yayi hon me gadi ya bud’e masa ya shiga parking yayi ya fita kai tsaye ya nufi d’akin bak’i sabida bayau bane farkon zuwan shi in yazo ma kai tsaye yake shiga.

Yana kai wa bakin k’ofar yaji numfashi da nishi, kirjin shine ya buga kan shi ya sara,daure wa yayi ya bud’e k’ofa ya shiga.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button