SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Abin da bai sani ba ta jima da tashi rik’o da ya mata ne ko motsi ta kasa yo shi yasa bata tashi ba tana jin sa ya tashi har ya mata kiss ya fice.

Shiko bud’e k’ofar yayi ganin Driver gidan sune da kayan abinci gaisawa sukai kafin ya ansa basket d’in abinci ya shiga ciki,kan dining table ya aje basket d’in direct d’akin shi ya nufa don ya watsa ruwa yaga lokacin azahar saura kad’an.

Itama mik’ewa tai ahankali ta na tafiya wani zafi taji ya ratsa ta k’yar ta d’an sake kafin ta ci gaba da tafiya ta shiga toilet ruwa ta tara ta shiga ta gasa jikin ta sosai kafin tai wanka ta fito zama tai bakin gado ta rafka ta gumi tunanin Baban ta ya fad’o mata arai.

Dai-dai lokacin Salman ya shigo cikin lal-lausar farin yadin sa ashe colour d’in ki tazar ce kansa sanye da hula bak’a sai kan shi yake tashi,duban ta yayi harya k’ara sa inda take amma bata san ya shi go ba zama gefen ta yayi ya dafo ta.

Firgi-git tai ta juyo ta kalleshi bak’a ramin tsoro taji ba don sam bataji shigowan shi ba,sai kima ta sunkuyar da kai alaman kunya.

Murmushi yayi mata yace, “tinanin me kike?

Ahankali tace,”ba komi”.

Yace,”bazaki fad’a min ba sai na k’ara miki kalan najiya?

Da sauri ta d’ago ta kalleshi.

Idanuwan su ne ya sark’e .

Da sauri ta kuma sunkuyar da kai ta na girgiza masa kanta,hawaye ne ya fara zubo mata daga kuncin ta.

Ganin haka yasa shi saurin sa halshen sa a fuskan ta yana shanye hawayen,saida ya debe su tas kafin yace,”dan Allah kukan ya isa haka banson kina min asaran hawayen ki haka wasa nike miki,bari in shafa miki lotion kisa kaya ki sallah”.

Tace,”dan Allah kabar shi zanyi dakai na”.

Yace,’wallahi ni zanai miki,kawai kiyi shiru kidena b’an-nan miyau d’in bakin ki”.

Jin ya rantse ya sata yin shiru.

Mik’ewa yayi ya d’auko mai d’in ya duk’a a gaban ta ya sa hannu ya jaye towel d’in dake d’aure jikin ta.

Saurin rintsa idon ta yi sabida kunyar shi takeji yanzu.

Shiko murmushi yayi yafara shafa mata mai d’in amma idanuwan shi nakan hips d’in ta daba din kar ya karya mata alwala ba da ya k’ara yake fad’a azuciyar shi sai lashe baki yake.

Ahaka yagama shafa mata man kafin ya mik’e ya bud’e wardrobe ya ciro mata dogon rigan atafa da inner wear da pant da bra ya dawo inda take idanuwan ta rufe kamar an dasa ta.

K’ok’arin sa mata bra d’in yaketai saurin bud’e idanuwan cike da kunya tace,”bashi nasa dakai na”.

Yace, “a’a baki isa ba sai na k’ara she lada ta”.

Cigaba da samata yayi aiko da yasa mata cif kamar ya iya pant da inner wear yasa mata kafin ya zira mata dogon rigan yace,”tou mik’e ki bud’e idanuwan kigani in ban iya ba”.

Bud’e idanuwan ta tayi tana duban kanta acikin mirror aiko rigan ta mata d’as ajiki,kallon sa tai ta kawar dakai kafin tace,”ko kyau bama ka iya ba”tana magana tana ya mutsa baki.

Murmushi yayi yace ai ban shafa miki powder da janbaki ba sai kinyi Sallah hijjab d’inta ya d’auko ya sa mata ya ja hannun ta kan sallaya yace,”yi sallah kafin na k’are sauran”.

Bata ce komi bacci tada Sallah da tayi .

Shi ko gyaran gadon ya fara,kan ta idar da Sallah ya gyara d’akin tas.

Da ta idar saida tai addu’o’i da azkar kafin ta mik’e.

Tahowa yayi ya rik’o hannunta tare da zare hijjabin da ke jikin ta kan kujeran madubi ya zaunar da ita kum ya d’auko ya fara taje mata kai.

Kara tayi tace,”da zafi kabarni inyi abuna” .

Yace,”affuwan my Nurul K’albi zanyi ahankali” ahankali ya fara yi mata gyara mata gashin yayi da kyau kafin ya d’aure mata da ribbon, powder ya d’auko ya bud’e ya fara shafa mata.

Duk tana zaune tana ganin ikon Allah azuciyar tace sai kace bashine yamin rashin imani ba jiya dadare.

Sai da ya gama shafa mata powder kafin ya d’auko jan janbaki ya sha fa mata.

Wow ba k’ara min kyau tayi ba simple makeup yama amma shima kallon ta yake sabida yaga tsantsan kyau.

Itama taga kyawun da tayi sai kace ya saba yin ma mata kwalliya.

Tura-ruka ya fara feshe ta dasu masu k’amshi da sanyi.

Yana gamawa ya koma bayan ta ya rungumota yana kallon ta ta madubi yace,”iye tayi kyau yammatana”.

Murmushi tayi tace,”ko kyau haka akace ma anayi?

Yace,”ni haka nikeso kuma yamin kyau”.

Tace,”niko saina wanke sa nayi nawa daban me kyau”.

Yai kici-kici da rai yace,”aiko dayau na miki yafi najiya”.

Zare idanuwan ta tayi kafin tace,”wasa nike wallah yayi kyau”.

Dariya taso bashi amma ya matse.

Tace,”saura d’aya bakayi ba”.

Yace,”mikenan?

Tace,”d’ankwali baka d’aura min ba”.

Yace,ni haka nikeso indai ina gida nafiso inga kanki a haka…………!

Ku k’ara hak’uri

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34

Leave a Reply

Back to top button