SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Story nd writing by
Khadeejatou Muhammad

Dedicated by ummaima Aliu SAMHA FANS Group

Page3⃣0⃣

Bissimillahi Rahmani Rahim.

“Y’ata k’wal tin k’wal ita d’aya na haifa,tou wallahi in ta mutu likita bazan b’oye ma ba sai na had’a da kai da Salman na kashe ku wallahi”.

Dr kam tsoro lamarin ya fara bashi gani yake kamar Alhaji Labaran mahau kaci ne cikin muryan lallashi Dr yace, “Alhaji kayi hak’uri ka sake ni in duba ta kaga tana cikin halin rayuwa ko mutuwa te makon gaggawa ya kama ta a Bata”.

Alhaji Labaran najin haka ya washe baki yayi saurin sakin ta yace yauwa Likita dan Allah ka ceto min rayuwan ta ita kad’ai gareni”.

Dr yace karka damu Alhaji zata tashi insahaallahu saide dan Allah kad’an jira awaje”.

Yace, “to Likita” ya juya ya fice.

Shiko Dr Sa’ad jingina yayi da bango yana sauke ajiyar zuciya tare da dafa k’irjin sa dai-dai lokacin Dr Marwan da Dr Habeeb suka shigo cikin emergency d’in gaisuwa sukai kafin suka rufa akan ta don ceto raywar ta.

Shiko Alhaji Labaran yakasa zaune balle tsaye sai kai da komowa yake.

Lokacin Alhaji Saminu da mom suka shigo cikin reception d’in asbiti da saurin suka k’ara sa inda suka gan shi tsaye.

Mom tace,”Alhaji yaya jikin nata ta tashi kuwa?

Yace Asma’u kita addu’a Likita na kanta yana duba ta”.

Alhaji Saminu yace,Allah yabata lafiya”.

Mom ce ta amsa da, “ameen”.

Alhaji Labaran kuwa harara kawai ya galla ma Alhaji Saminu.

Alhaji Saminu ko dariya yayi irin tasu ta y’an duniya.

Mom kujera ta samu ta zauna ,Alhaji Saminu ma haka,yayin da Dad din Lubabatu yake ta kai da kawowa yana tina nin matuk’ar Y’ar sa ta mutu kisan wulakan ci zai ma Salman da duk dangin shi.

Tsawan awa biyu da mintina kafin aka bud’e k’ofar emergency d’in Dr Marwan ne ya fara fitowa sai Dr Sa’ad ya biyo bayan shi sai Dr Habeeb ganin sun fito Dad din Lubabatu da sauri ya nufe su har yana cin tuntub’e.

Dr Marwan yayi saurin yin gefe cike da tsoro yana kallon shi kamar wani zararre.

Dr Habeeb yai sa’an rik’o ma riga yana fad’in,”Dr ya take bata mutu ba ko?

Murmushi Dr Habeeb yayi masa yace,”ka biyo ni office”.

Binsa yayi a baya har cikin office din sa waje yanu na masa ya zauna.

Shima wajen zaman shi ya ya zauna ya fiskanci Dad d’in Lubabatu yace,”Alhaji a gaskiya y’ar ka tana cikin wani hali halin da zamu iya cewa in har bata sami abin da take so ba zata iya rasa rayuwar ta”.

Zumbur Dad d’in Lubabatu ya mik’e tare da fad’in yanzun Likita ta mutu ne ko bata mutu ba kafitar dani cikin duhu?

Dr yayi murmushi tare da gyra farin glass d’in idon shi yace, Alhaji ka zauna ka kwantar da hankalin ka mi magana y’ar ka tana raye bata mutu ba”.

Zama yayi tare da tattara hankalin sa wajen Likita kafin yace, “Likita ina jinka”.

Dr yace, “Alhaji y’ar ka ta kamu da ciwon zuciya me tsanani zuciyar ta na gaf da fashe wa matuk’ar bata sami abun da take muradi ba,sannan kuma gaskiya zata iya kai wani lokaci me tsawo bata farka ba kamar kwana d’aya sati d’aya wata d’aya kofiye da haka ko kuma yanzu haka zata iya tashi”.

Shiru Dad d’in Lubabatu yayi na d’an lokaci kamar me tinani kafin yace,”Likita tou yanzu miye abinyi?

Dr Habeeb yace,” Abinyi shine zami I k’ok’arin mu zuwa wani lokaci magani”.

Dad d’in Lubabatu ya nisa kafin yace, “Likita tou in kaga da matsala sosai afitar da ita waje inda kwararrun likito ci suke a duba ta.”

Dr yace, “kade bari mi iyakan k’ok’arin mu ninan da kake gani na a k’asar India nai karatun Likita na k’wararrun Likito ci suka bamu horo don haka banga abin da zai gagareni ba a fannin zuciya inko kaga ya gagareni to k’ila da wiya mutun ya rayu”.

Dad d’in Lubabatu yace to shikenan nayar da kai don naga duk kafi sauran hankali da na tsuwa na baka amanar y’ata ka kula min da ita inhar ta tashi komi kake so zan maka”……..

Kuyi manage
[11/21, 7:17 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

           ????????????????????
                 ????????????
                         ????

????SAMHA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Story nd writing by
Khadeejatou Muhammad

Dedicated by ummaima Aliu wannan page din nakine gaskia inajin dadin comment din ki Allah yabar zumunci

Page 3⃣1⃣

Bissimillahi Rahmani Rahim.

Dad d’in Lubabatu yace,”nabaka amanar y’ata ka kula min da ita in har ta tashi koki kake so zan maka”.

Murmushi Dr Habeeb kawai yayi masa bai ce komi ba.

Dad d’in Lubabatu yace, “zamu iya ganin ta?

Girgiza kai Dr yayi alaman a’a kafin yace, “zaku ganta amma ba yanzu ba sai zuwa anjima”.

Yace,”tou shikenan Allah ya kaimu”.

Dr yace,”Ameen” ata k’aice.

Dad d’in Lubabatu yasa kai yafita daga office d’in.

Mom tai saurin taran shi tace,”me Likita yace?

Be mata magana ba illa waje da ya samu ya zauna, tare da lumshe idanuwan shi yana sauke wani irin ajiyar zuciya.

Ita ma kama bakin ta tayi shiru sabida tasan halin mijin ta in yana cikin b’acin rai bai fiye magana ba,zama tayi a gefen shi ta rafka uban tagumi.


Salman ko yana shiga d’akin shi yawani ja tsaki tare dayin k’wafa yace, lallai yarinyar nan sai munsa k’afar wando d’aya da ita bani tasa Mama ta ta d’aga ma murya ba abin da- da bata yi min” k’wafa ya k’ara yi.

Cire kayan jikin shi ya fara yi yana wulla ko wanne gefe towel yad’aura ya shige toilet don yin wanka.

A fall ko Samha mik’ewa tayi ta shige d’akin ta ta kwanta kan gado cike da jin haushin Salman azuciyar ta tace lallai ma wai in zanfita wanan me fuska biyun zan ringa tambaya tou amatsayin shi nawa nifa wallahi an ta kura min da zaman gidan nan da zasu maida ni gidan mu inda Baba na danafi farin ciki,
ahaka take ta tinani har bacci ya kwashe ta .

Shiko Salman anfito wanka anshirya cikin wata dakakiyar shdda fara yasa bak’in takalami da bak’in hula sai k’amshi yake ,yafito falo ya zauna bai iske kowa ba azuciyar shi yace lallai yarinyar nan mi take nufi jira take in shiga in kirata cabd’i,k’wafa ya kuma yi cike da haushi.

Tsawan minutes talatin yana zaune ranshi ya b’aci ya mik’e fuuuuuuu ya nufi d’akin ta ya tura k’ofar ko sallama babu se huci yake kamar maciji,da ma-makin sa yaganta kwance kan gadon ta tayi d’ai d’aya har hijjab d’in ya fice,surarta ya zuba ma ido yayi matuk’ar tafiya da hankalin shi da tunanin shi jiyayi gaban shi ya buga dummmm saurin janye idon shi yayi cike da jin haushin kansa ,takaici ne ya lu-llub’e shi ganin yana jiran ta ita kuma baccin ta ma take ,fita yayi fuuuuu ya nufi kitchen yad’auko ruwa me sanyi a cinkin firich ya dawo d’akin ya k’ara sa in da gadon yake ya bud’e murfin ya d’aga gorar ya shara-ra mata ga jiki.

A firgice ta mik’e ta bud’e baki zatai ihu.

Saurin to she mata baki yayi don kar Mama taji ta shigo taga abin da yayi mata ta bal-bale shi da fad’a.

K’ok’arin k’watan bakin ta take.

Amma ina ta kasa,sa hannu tai tattaro d’an k’arfin ta-ta hankad’a shi.

Gefe yayi tare da tsura mata ido.

Wani irin kuka ya k’wace mata sabida tsanani takaicin abin da ya mata.

Ganin tana kuka jikin shi ye sanyi don shi a duniya ya tsani jin kukan mace, ahankali ya tako in da take ya hayo gadon zai kai hannun sa jikin ta.

Da sauri ta matsa tare da cewa,”Kar kafara mara imani mara tausayi kawai kara bani da mahaifina bai ishe ka ba, aiban ce dole sai ka kaini ba da har zaka zuba min ruwan sanyi a jiki na”, ta d’an nisa kafin tace,”ashe ba saboda Allah ka anso ni wajen mahaifina ba ka d’auko nine don ka rink’a a zabtar dani”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button