SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace, “a’a Mama ina da magani zansha in kwanta………..!

Kuyi manage
[11/21, 7:20 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

           ????????????????????
                 ????????????
                         ????

????SAMHA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Story nd writing by
Khadeejatou Muhammad

Dedicated by ummaima Aliu wannan page din nakine gaskia inajin dadin comment din ki Allah yabar zumunci

Page 3⃣4⃣

Bissimillahi Rahmani Rahim.

Hawayen dole take sabida tsananin azabar da lips d’in ta suke mata,mamayan shi tayi ta gantsara masa cizo a halshe.

Wata azab yaji har cikin k’wak’wal warsa sa, saurin sakin yayi tare da tsuke bakin shi ya sa hannu ya dafe yana kallon ta yana ya mutsa fusaka.

Itako da sauri ta bud’e k’ofar ta fice tana tsoron kar ya k’ara rik’e ta falo ta koma ta fad’a kan kujera tana maida numfashi.

Shiko k’wafa ya yi a zuciyar shi yace lallai yarinyar nan ni ta ciza ko aikam bata ci bulus ba,koma wa yayi kan gadon ta ya kwanta sabida azabar da harshen sa yake masa.

Ita ko kwanciya ta tai a falon da ta rufe ido sai taji kamar bakin ta na cikin nashi ga azabar da lips d’in ta suke mata duk sun kumbura,tsaki taja a zuciyar ta,tare da cewa, jibe shi kamar na kirki ashe d’an iska ne,tsaki ta k’ara ja.

Shiko bai yana kwance yana ya mutsa fuska sabida zafin cizon bai sake shi ba ahaka har bacci y kwashe shi.


Zaune take ta rafka uban tagumi lokaci-lokaci takan ja tsaki.

Inna Larai ta shigo dauke da bak’in leda a hannun ta,ajewa tayi a gaban ta tace,”gashi dankali na samo kuma gashi ba zafi yayi sanyi hakanan na siyo shi sabida in ban saya ba babu abin da zamuci Kuma kin san kud’in naira d’ari ne yayi saura shine nas……!

Dogon tsaki taja kamar harshen ta zai tsinke shi ya katse Inna Larai daga jawa bin ta,tace,” ni dalla kin isheni da surutu ki na tsiya kuma wallahi bazan ci dan kali sandarar re ba, duk gidan uban da zaki ki nemo min abinci kine momin,ba duk ke kika ja min ba” mtsuuu ta k’ara jan dogon tsaki.

Duk’a wa tayi har k’asa kamar ita ce y’ar ta kwantar da murya tace haba zainab kiyi hak’uri kici wallahi ba inda zani in samo miki wani abun,kuma kinsan bana da hali wallahi naira saba’in yayi saura anjima zan sayo gari da suga musha”.

Wani kallo ta watsa ma Inna Larai tare da cewa, kambu,gari naji kince me kike nufi yanzu naci dankali anjima nasha gari sammm bazai yuwu ba ki sake tunani wallahi”.

K’ara kwantar da muryanta tayi tace,kiyi hak’uri ko andomie (indomie) sai in siya in ta fasa miki basai naci ba kinji”.

Dogon tsaki ta Kuma ja kafin ta jawo ledan ta fara cin dankalin tanayi tana zage-zage.

Ita dai lnna Larai tsuru tayi bata iya tanka wa ba, mik’e wa tayi ta fito k’ofar d’akin ta zauna cikin ta nata kukan yunwa.

Gwaggo Dije ce ta fito da bokiti alaman wanki tayi zata shanya ko kallon inda Inna Larai take bata yiba,ta wuce ta fara shanyar ta.

Almajiri ne ya fara bara, Inna Larai tai saurin cewa,” kayi hak’uri”.

Gwaggo Dije tace,”yaka d’an Malan”.

Almajiri ne ya shigo, Gwaggo Dije tace, ina zuwa” daki ta shiga sai gashi ta dawo dauke da kula tace kawo robar ka, Mik’a mata yayi
[11/22, 7:04 PM] Sumayya: ????????????????????????????????????
????????????????????????

              ????????????????????????????
                                ????????

????SAMHA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Written by khadeejatou Muhammad

Dedicated by k’amshi,jikan hajiya

Page37

Bissimillah Rahmani Rahim

Take fara’a ta ya gushe saide nakan fuska tace,”na gode Amma gaskiya bazan ansa ba Mama.

Dr gaban shine ya buga dummmm da sauri ya d’ago yana kallonta.

Mama ma kallonta take cike da mamaki.

Salman kokallon inda take baiyi ba kan shi na k’asa.

Mama tai k’arfin halin tace,”mi yasa Daughter?

Samha ta taso tazo gaban Mama ta duk’a har k’asa cikin sanyin murya tace, “Mama ki gafar ce ni inna ce ina son sa nayi k’arya, ban San sa kuma banso na yaudare shi kiba shi hakuri kawai”.

Mama tai jimmm kafin tace, “Do baki isa ba in ma ba kisan sa wa kike so?

Juyawa tai ta kalle wajen da Salman yake taga hankalin shi bai wajen su ta kalle Mama tace, “Mama Salman nake so shi zan aura shi yafi da cewa da ya zama mijina”.

Zuciyar Dr ta buga dum-dum-dum baki wangame ya mik’e yana nuna ta.

Mama ma kallonta take.

Salman ma saurin d’agowa yayi ya zuba mata ido.

Mama tai k’arfin halin tace,”Samha baki isa ki maida ni k’ara mar tsohuwa ba,agaban yaro wallahi baki isa ba,tunda ai bai ce yana sonki ba”.

Murmushi tayi tace Mama ko be sona ni ina son shi kuma zanje in sami Baba in fad’a masa na fidda miji” tana kawo wa nan tai wuce war ta d’akin ta don bata son ganin Dr haushin shi take ji.

Dr ko tsaya yayi kamar mutum-mutumi Mama ce ta dube shi cike da tausa yawa tace,”Dr kayi hakuri kaga bani na haife ta ba balle ince zan mata dole ta soka ko ta zauna da kai,wallahi ba haka na soba”.

K’ak’alo murmushi yayi da iyakan sa fuska zuciyar sa cike da k’unci yace,ba komi Mama aini da Salman duk d’aya ne Allah ya tabbatar da alkhairi”.

Mama ko kunya ne taji ya lu-llub’e ta da k’yar tace,”ameen” cike da kunya.

Sallama yayi masu ya fice,ko kafin Salman yabi bayan sa har ya fad’a motor yayi mata key me gadi ya bud’e masa ya fice.

Salman da ido ya bisa,cikin zuciyar shi ko cike da farin ciki.

Mama ko zama tayi duk jikin ta ya mutu baza tace tana farin ciki ba balle tace bak’in ciki duk ta rasa yanayin da take ciki.

Samha ko tana shiga d’akin ta ta fad’a kan gado cike da jin haushin kanta,ga wani kunyar Mama da taji ta shige ta,tuna ni ta fara tou data ce tana son shi aishi bayan santa, murmushi tayi ta kuma cewa don in rabu da wannan Dr ne.

K’ara bud’e k’ofar d’akin yasa ta saurin juyawa, Mama ce tsaye.

K’ak’alo murmushi tayi tace, “Mama kece?

Ta tako ahankali ta zauna gefen gadon tace,” in bani bane to waye kita shi muyi magana”.

Mik’ewa tayi ta zauna kanta sunkuye don kunyar Mama take ji.

Mama ta dube ta tace,”miyasa kika min haka Samha?

Kasa magana tayi sai k’ara sunkuyar da kan da tayi.

Mama tace, “gaskiya Samha ban ji dad’i abin da kika min ba tunda haka kika zaba ma kanki Allah ya zab’a abin da yafi zam Alkahairi mik’ewa tayi tace,to in kin gama jin kunyar kifito muci abinci bata jira Jin amsar ta ba ta fita”…….!

Manage masu korafi kuyi hakuri wallahi ina busy ne sosai.
[11/22, 7:04 PM] Sumayya: ????????????????????????????????????
????????????????????????

              ????????????????????????????
                                ????????

????SAMHA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Written by Mrs Basskkwace

Dedicated by Mrs Aliyu(kishiya ta)

Page36

Bissimillah Rahmani Rahim.

Mama ta rik’e baki tace, “ahhhh Likita nifa ban son haka gaskiya,zata rik’e waya amma ba a gidanan ba saide a gidan ka in ka aure ta”.

Mara-irai ce fuska yayi yace, “Mama kenan baki bani ita ba,kuma baki d’auke ni a matsayin d’an ki ba tunda na ba k’anwan ta kyau ta kin k’i karb’a”.

Murmushi tayi tace,”ba haka bane Dr ina so in maida ta makaranta,ban son rik’e wayar nan kar hankalin ta ya rabu biu,amma tunda kace haka shikenan zan bata,in batai karatu ba anshe wa zanai”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button