SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi yay yace,”tou Mama na gode inshaAllahu baza ma asamu matsala ba”.

Tace,”Allah yasa”.

Yace,”Ameen”.

Ta dubi Salman tace, “My son”.

Ahankali ya bud’e idanuwan shi ya sauke akan ta yana murmushi da iyakan sa kan fuska.

Tace,”yaya dai ko jikin ne?

Ya girgiza mata kai alama a’a.

Tace,”naga muna magana kayi shiru ya akayi ne?

Yace,”bakomi wallahi” atak’aice yayi maganan.

Tace,”tou shikenan tashi ka kira min Samha kaga Dr ya bata waya kai mai godiya itama tazo ta mai godiya”.

Yace,”tou” badon ran sa yaso ba ya mik’e ya nufi hanyar d’akin ta.

A zaune ya isketa tana ta tilawan alk’urani cikin muryan ta me dad’i kamar ana busa sa rewa lumshe idanuwan shi yayi tare da jingina jikin jikin k’ofa.

Itako ko d’agowa bata yi ba duk da taji alaman tsayu war mutum ciga ba tayi da karatun ta.

Shi ko ganin bata tsaida karatun ba yasa shi ya juya ya fice ya koma falo yace,”tana zuwa”.

Tace,”tou me takeyi da ba ku taho tare ba?

Yace,”karatu take”.

Tsawan lokaci bata taho ba har aka fara kiran sallah ishaa’i bata fito ba, Salman ya mik’e ya nufi hanyar k’ofa yace, “
Mama zanje sallah”.

Tace,”tou ai mana addu’a”.

Murmushi kawai yayi yafita.

Dr ta ma mik’ewa yayi ya bi bayan sa.

Mama ma tashi tayi ta nufi d’akin ta don yin sallah.

Samha naji ankira sallah ta mik’e ta tada sallah,tana idar wa saida tayi addu’o’i kafin ta tashi kan sallayar ta ninke ta fito falo.

Dai-dai lokacin Dr da Salman suka shigo falon, kallon-kallo sukai da Salman sai da taji yarrrr har cikin jikin ta wani kwarjini taga ya mata.

Dr ko washe baki yayi yace,”haba baby tun d’azu nike jiran ki saida aka gama jamin aji kafin a fito”

Wani dummm taji tare da wani k’ulu-lun bak’in ciki ya tsaya Mata k’afon zuciya,k’ak’alo murmushi tayi tace,”ina wuni?

Ya amsa cike da fara’a yace, “lafiya k’alau”

Mama ce ta fito tace,”a’a har kun dawo ?

Dr yai saurin cewa,”eh Mama”.

Zama tayi ta duba Samha tace, “ki zauna mana ga waya ylYayanki ya saya miki ki masa godiya”.

Zama tayi gefen Salam cike da farin ciki a tuna nin ta Salman ne ta kamo hannayen sa tace,”Yaya na gode sosai”.

Dr yaji wani abu ya tokare shi a mak’oshi.

Salman ko yarrrr ajikin shi.

Mama tace, “ke bashi ba Likita nike nufi”.

Take fara’a ta ya gushe saide nakan fuska tace,” na gode amma gaskiya bazan ansa ba”………!

Kuyi manage Allah am busy morning duty nake.
[11/22, 7:04 PM] Sumayya: ????????????????????????????????????
????????????????????????

              ????????????????????????????
                                ????????

????SAMHA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Written by khadeejatou Muhammad

Dedicated by k’amshi,jikan hajiya

Page38

Bissimillah Rahmani Raheem .

Tagumi tayi ta lula duniyar tinani.

Salman ko da ido ya bishi tare da ta’ba baki kafin ya juya ya koma cikin gida falon ba kowa direct d’akin Samha ya nufa tura k’ofar yayi ba tare da sallama ba.

Jin anbud’e k’ofar ne yasa ta saurin d’agowa ganin Salman ne yasa gaban ta ya buga dummm.

Ta kowa yayi a hankali ya k’ara sa inda take ya tsaya yana me k’are mata kallo.

Itama kallon shi tayi ido cikin ido take taji ya mata kwarjini saurin jaye idon ta tayi.

Cikin kakkausar murya yace,”ke ni sa’an wasan kice,kin ga nayi kama sa’an aure ki da a gaban Mama zakice kina sona,da yake baki da kunya,tou wallahi ki gaggauta zuwa kice mata ba k’yaso na Dr Abbas kike so”.

Kallan shi tayi ido cikin ido ta murgud’a masa baki kafin ta tace,”to dama nace ma ko da na fad’a haka ina sonka ne nima tou mizan ma yi dakai jibe ka ni wallahi inna aure ka raina ka zanyi don ni kamin kad’an kamin k’ara mi”.

Baki wan game yake kallon ta da k’yar ya iya cewa,”haka kika ce?

Tace, “eh” atakai ce.

Murmushi yayi kawai yajuya ya fice.

Da ido ta bishi tana galla ma bayan sa hara-ra.

Shiko d’akin shi yayi direct ya cire kaya ya fad’a toilet ya watso ruwa ya fito ya shirya cikin kayan baccin sa,fito wa yayi ya nufi dining ya zuba abinci shi yaci han kali kwance, azuciyar shi ko sak’e-sak’e abin da zai ma wancan mara kunyar wofin.

Samha ko mik’ewa tai tai wanka ta fito ta shirya cikin kayan baccin ta gado ta haye tai kwanciya ta.

Akwana atashi ba wiya yau watan zainab biyu da karye wa,amma ba abin da yaci gaba k’afar ta fara ru’bewa sabida ta fara wari,gashi duk k’awayen ta suma sun dena neman ta hatta samarin ta ba me bid’an ta,duk ta rame tayi bak’i man bleaching ya k’are gashi ba halin fita ta sami kud’i ta sai wani,ga abinci ma wiya yake musu don Inna Larai sai ta fita yanzu ta nimo wanke-wanke ta samu awajen wata me saida abinci layin su duk wuni naira saba’in ake bata,dashi take samu ta sayo musu gari kwaki da sikari ko kuma dankali su ci shine dare rana safe duniyar ta musu k’unci.

Inna Larai ce ta d’ago labule ta dubi zainab da ke zaune shirin guda kamar kayan wanki duk tabi ta rame tayi bak’i cikin tau sayawa tace,”sannu ki da hutawa”.

Wani kallo ta watsa mata tare da jan tsaki cikin tsawa tace,wani hutu ba dukke kika jamin ba kece silar kasan cewa ta ahaka gashi nan na-nakasa bani moruwa, nayi da na sanin kasan cewa y’arki Allah Larai bazan yafe miki ba,ki duba kiga yanda na koma nazama abin k’yama cikin muta ne da baki sanadin koma wata haka ba da yanzu naza ma wata Abu”.

Inna Larai ko da ido ta bita har ta da katar da maganan bata ji haushi ba illa kawai cewa,tayi” Allah ya baki hak’uri,ki kawo wayar ki insai da in kira me gyara ya k’ara duba k’afar”.

Wani kallo ta k’ara watso ma Inna Larai kafin tace,”kambu wa yata fa kika ce kin san nawa take, dubu d’ari takwas da saba’in Alhaji Labaran ya saya min shine za kice na saida”.

Gwalalo ido lnna Larai tayi tace, “zainab kina rik’e wannan zun-zurutun kud’in kina zaune da ciwo wallahi baki isa ba sai ansai da wayar”.

Tace,”uwar da ya fasa saida wa ya raina Allah da ya halicce shi”.

Inna Larai jin abin da tace yasa ta Kwan tar da murya ta fara la-llamin ta .

Amma ina zainab tak’i fahimta.

Haka ta hak’ura ta barta.

Gwaggo Dije ko cigaba take da kula da mijin ta kullum abinda yake so shi take mai,gashi sauk’i yafara samuwa sosai don gashin da ake mai ya amshe shi har ya fara motsa gab’obi’n shi.

B’an garan Lubabatu kuwa tun ranar da ta bud’e ido ta sauke akan Dr Habeeb duk duniya taji ba wanda take so bisa da shi,take taji ciwon ya tafi.

Hakan ba k’ara min dad’i yayi Dad ba da Mom.

Itako bata b’oye ma Dr ba ta fad’a masa son shi take,shima ya amince sabida duk wanda yaga Lubabatu yasan big girl ce ga shi tana da kyau da diri ba k’arya, amince yayi da soyayya ta.

Dad ko yana gani yar shi ta ji sauk’i yasa shi ya koma barikin shi arana sai yane mi y’ammata takwas lokaci d’aya.

B’an garan Samha ko kullum zaman doya da manja suke,duk inda Salman ya ganta sai ya b’alla mata hara-ra in yasa mu dama ma ya buga mata ran k’washi akai,bata ta’ba fad’a ma Mama ba iyakan ta shige d’aki Tasha kukan ta.

Ashe duk abin da suke Mama na kula dasu d’auke kai kawai take yi, Salman bai sani ba taje ta sami Baba akan maganan aure su,inda Baba ya ji dad’i Gwaggo Dije ma tayi farin ciki.

Duk tsawan lokaci nan da aka d’auka Samha ba ta ta’ba takowa gidan su ba,saide suyi waya ta wayar Mama in takira Gwaggo Dije sai taba Baba su sha hiran su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button