SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Itako Samha murmushi d’ai take.

Sumayyah ko abin nema ya samu sai zuba take tana musu pic’s kala-kala.

Samha mik’ewa tai,da ido tamai alaman ya biyo ta.

Shiko mik’e wa yayi zuguy-zuguy yabita,suka nufi dining table.

Sumayyah ko saki baki tayi tare da tafa hannu tace,”oh ni Sumayya Ahmadu yau naga d’an kwali yaja hula”.

Samha ta juyo ta galla mata hara-ra na wasa kafin tace,”kinji haushine?

Suna tace,”ba dole ba”.

Salman yace,”tou sha fiya-fiya ki mutu”.

D’aura hannuwa tai bisa kai ta gwalalo ido tace,”Bross dama ashe haka kake baka sona?

Gira ya d’aga mata kafin ya ce, “sosai-sosai kuwa in har ina wajen princess d’inta duk wata mace kamar namiji take”.

K’ara gwalalo ido tayi.

Samaha ko gwalo tai mata kafin ta fara sama Salman abinci.

Sumayyah ko cewa,”tayi lallai aizaka tafi kabar ni da ita”.

Yace,injiwa k’afata k’afar ta bazan barta anan……

Fitowa Mami yasa shi yin shiru.

Mami da fara’a ta tace”,a’a ango yasha k’amshi”.

Sunkuyar da kai yayi cike da kunya yace,”Mami barka da dare”.

Tace, “yauwa ya kake ya kawana biyu idon ka kenanwato da ba amaryan ka anan bazanga k’yeyar kaba?

Murmushi kawai yake kansa a sunkuye.

Sumayyah tace,”bashi Mami ba zamu bashi matar ba ko bayan aure”.

Mami tace, “a’a shida matar sa waya isa yace uwar sarki shegiya ce”.

Dariya su kasa duka,nan Mami ta gama masa tsiya kafin a basu waje.

Kallon Sumayyah yayi ya galla mata hara-ra yace,”tou Malama abamu waje zan ke’be da mata-ta”.

Murgud’a masa baki tayi tare da cewa,”yanzu ma in gaya muku”.

Yace,”to Allah ya raka taking gonna, Kuma dan Allah kiyi kyau ranan bikin mu ko zaki sami mashin-shini”.

Wani kallo tayi masa tare da ta’ba baki tace, “ai banga abin da kwad’o ya d’are gaya ba,wanga kod’ad’an matar taka aina fita kyau da lafiya” tana Kai wa nan bata jira mi zaice ba tai shigewan ta.

Dariya Samha take,shima murmushi yayi kafin yace, “Sumayyah-Sumayyah bade baki ba”.

Samha tace, bissimillahi,”tunda ta ruga ra wuce”.

Tab’e fuska yayi kafin yace ,”Madam k’ara she ladan ki”.

Ciki rashin fahimta tace,”wani k’arashe?

Baki shi ya gwada mata da hannun sa yace,”inba haka ba banci”.

Murmushi tayi ta jawo kujera kusa dashi tafara bashi abaki.

Ashe Sumayyah ta na la’be tana musu pic’s.

Shike mata Shira itako daga eh sai a’a.

Harta gama bashi abincin ta zuba masa kunun aya nan wai saide tabashi abaki,hakanan ta bashi yanayi yana mata shagwab’a.

Itako biye masa ta rik’a yi duk mi yace haka take biye mai.

Saida ya gama iyayin shi har bayan ishaa’i kafin yamata Sallama ya tafi gida,ita kuma tashige ciki ta shaida ma Mami ya wuce,kafin ta wuce d’akin ta.

Tana shiga ta iske wayan ta na ringing duba wan da zata yine taga shine, murmushi ya sub’u ce mata……..

WANNAN PAGE D’IN NAKINE MY KANKANOTY???? ALLAH YA K’ARO YAWAN SHEKARU MASU ALBARKA YAWAN KU’DA’DE KAMAR KETA (CBN)DA MIJI NA GARI KAMAR NAWA???? SAURA KUMA KIJI KINA SONAI????
[11/23, 8:05 PM] Sumayya: ???? SAMHAA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya d’aya ce daga k’inta sai b’ata burinmu mu fad’akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}

          ```????G•W•A????```

GASKIYA DOKIN K’ARFE•????????

~VOTE & FOLLOW 4Wattpad @~
~GasjiyaWritersAsso.~

WRITTEN BY MRS BASSKKWACE

DEDICATED BY UMAIMA ALIU

PAGE 48

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

Kallon screen din wayar Samha tayi ganin sunan shi yana yawo murmushi kawai tai,amma har ya katse bata d’aga ba.

Shiko ganin bata d’aga ba yasa shi saki gajeren tsaki yaci gaba da tuk’in shi.

Toilet ta fad’a tawa tso ruwa tare da d’aura alwala tafito ta gabatar da sallah ishaa’i.

Gwaggo Dije kuwa ta d’au ke Zainab ta kaita asbiti nan Likita ya diba ta yace baza ayanke k’afar ba za’a sake sabon karya ta a d’aura,sai a rink’a mata dressing.

Aiko Gwaggo Dije ta amince aka k’ara karya k’afar aka gyara,inkun ga Zainab tazama abin tausayi kamar ba ita bace yar gayunan me wanka da kwalliya.

Inna Larai ko yanzu duk tayi sanyi ta kwantar da kanta sai hidiman biki ake inka ganta yanzu ta murmure, Gwaggo Dije ta Bata Kaya da yawa,gashi har ta yi masu kayan fitan biki kala guda hidima kawai ake.

Bangaran Dr kuwa tun da ya kama Lubabatu da wani suna aikata masha’a bai k’ara bi ta kanta ba yayi blocked d’in numbers d’inta yanda ko ta kira bazata same shi ba,yayi dan gana ga ubangiji ya maida komi kaddara.

Lubabatu kuwa tashi ga cikin wani mugun hali ta rame akwana biyu ta kod’e taza ma kamar ba ita ba,tayi da na sanin abin da take aikatawa.

Dad d’in ta ko sai abinda yayi gaba arana inbai nemi mata ba yanema biyar shida kuma alokaci d’aya yake la-laceewar sa da su.

Salman anan ana shirye-shiryen angwan cewa kan nan rawa kawai ya keyi.

Mami ko sai k’ara gyara Samha take sabida gobe zata koma gidan su daganan in and’aura aure sai adauketa akaita d’akin mijinta.

Akowani b’angare hidima akeyi sosai-sosai.

Kwance yake bisa kan gado yayi matashi da hannayen shi idon shi na kallon sama tunanin shi d’aya gobe tayi ya koma gidan Malan Nura ya duba masa aikin yaga yayi,don shi wallahi ko ta halin ka-ka sai ya sure Samha inba haka ba kowa ya rasa ta don wollahi yanda yakeji yanzun duk yanda yake da Salman zai iya kashe shi don ya aure ta,haka yake ta tinani har bacci ya d’auke shi.

Ance fa rana bata k’arya saide uwar d’iya taji kunya.

Ayaune dubban jama’a suka shaida aure Engineer Salman Sulaiman D’ingyad’i da Amaryan sa Samha Salis K’aura akan sadaki naira dubu d’ari biyu da hamsin lakadan ba ajalan ba.

Lokacin Dr Abbas yana zaune a office dinshi yana tinanin miya sami wayar Rabi’u in ya kira switch off kullum,wayar shine datai k’ara ya saurin duban ta atina nin shi Rabi’u ne sai yaga Muhseen ne, d’an tsaki yaja kafin ya d’aga ya kara akunne.

Dai-dai lokacin ake sanar da d’aura auren Samha da Salman.

Shiko Muhseen ya kira shine yaji inda ya shiga baizo wajen d’aura auren Salman ba,sai hello hello yake.

Amma Dr ya kasa ko ansawa domin lokacin dayaji an d’aura auren Salman da Samha tuni jijiyoyin jinin jikin shi ya tsaya.

Muhseen kashe wayar yayi,da yaji baya ji.

Amarya ko tana zaune acikin bedroom d’in Gwaggo Dije tasha kyau gefen ta Sumayyah ce da k’awayen Sumayyah da ta gay-yato su sun sha anko sai hira suke,itako Samha shiru tai musu bata cika sa baki ba.

Canna hago ango tsakiyan taro sai washe baki yake kamar gonan audiga yana gaisawa da mutane bak’in da ya gayyato duk inda ya gilma d’auka hoto kawai ake masa ga tarin y’an jarida da suke nunawa kai tsaye.

Lokacin Lubabatu da Dad d’in ta suna falo suna hira lokaci-lokaci suna duban Tv,ba zata suka ga ana d’aura auren Salman .

Take k’irjin Lubabatu ya buga.

Dad d’inta ko tsaki yaja tare da cewa, “shege matsiyaci wanda baisan abin arziki ba”.

Ita ko Lubabatu mik’ewa tai tashige d’akin ta sabida taji wani abu da bata san na miye ba ya to kare mata k’irjin ta.

Shiko Dad kashe Tv yayi yanata zage-zage.

Dr ko d’aukan wayar shi yayi yakira wani abokin sa yace, masa yana son ya had’a shi da tsagerun y’an ta’ad-da wanda zasu kashe mutum lokaci guda,aiko ba ajima ba sai gashi nan yaturo mai number su.

Kira yayi ya masu kwatancin inda yake don suzo su same shi.

Dad ko mik’ewa yayi ya d’auko drinks a firich ya ciro wani k’waya a aljihun shi ya zaz-zage a ciki, direct d’akin Lubabatu ya nufa,akwance ya isketa tayi ruf da ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button