SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wata dattijuwar tsohuwa nagani tayo hanyar waje wacce bazata haura araba’in da biyar ba a bakin k’ofa sukai ki ci’bis.

Lubabatu fad’awa jikin tayi tana kuka tana fad’in “Momy ina Dad baby yace bayaso na bazai aureni dan Allah kisa shi dole ya aure ni”.

Tsawar da ta bugama ta yasata yin shiru ta shanya maganan .

Tace “keeee waike wace kalar shasha ce kina tsu inbakya cikin hankalin kine kidawo”.

Dayake tana matukar tsoron mahaifiyar ta murya na rawa .

Tace “kiyi hak’uri mom Ina son shi zan iya mutuwa in ban same Shiba”.

Shiru mahaifiyar ta tayi tana k’are mata kallo kafin tace mushiga bed room d’ina miyi magana kije kijiran ina zuwa”.

Gyada kai tayi ba tare da tayi magana ba ta wuce.

Mahaifiyar ta ko da ido tabita tana mamakin hali irin na Lubabatu Baban ta ya sangar ta ta komi take so sai yamata.

A b’angaren Samha ko tun da ta tashi da asubah tai sallah bata koma ba tana zaune kan daddu ma ta zuba ma waje d’aya ido tuna nin Baban kawai take sai wajen bakwa ta mik’e ta nufi parlour bakowa aciki alaman ‘yan gidan Basu tashi ba fara gyaran falon tayi duk da bawani datti yayi ba k’ara gyarawa tai ta kunna tiraran wuta falon yad’au k’amshi me dad’i kitchen ta nufa ta tsaya tana tunanin me yaka mata tayi yanzu azuciyar ta tace bari dai inje inga Mama ko ta-tashi in tambaye ta juyawa tayi ta nufi d’akin Mama zaune ta isketa tana karanta wani littafin addu’o’i sallama tayi tare dazama gefen Mama tana jiran ta ta gama ta tambaye ta.

Mama ganin shigowan ta ya sa tarufe littafin ta dubeta tana me ansa sallamar tace “Amin wa’alaikumusalam, Samha antashi?

Dukar da kai tayi tare da fad’in “eh Mama Ina kwana antashi lafiya”.

Cike da fara’a Mama ta amsa “da lafiya k’alau ya bak’unta?

Shiru tayi cike da kunya saima k’ara duk’ar da kanta k’asa datayi.

Murmushi kawai Mama tayi kafin tace yadai Daughter akwai matsala ne.

Girgiza kanta tayi tare dacewa “a’a Mama dama nazo tambayan ki me za’a dafane?

Gwalo ido Mama tayi tare da cewa “haba Daughter wane irin girki kije ki kwanta ki huta yanzun Inna Lami me girki zatazo ta d’aura”.

Shiru Samha tai na dan lokaci kafin tace “to Mama ni wani aiki zan rink’a yi?

Shiru Mama tayi da alamar tunani kafin tace “ki bari in Yayanki ya tashi zami magana yanzu kitashi kije ki kwanta”.

Mik’ewa tayi tare da fad’in “tou Mama ahuta lafiya”.

Murmushi dake fuskar Mama har yanzu bai d’auke ba tace Allah yasa my Daughter.

Ficewa tayi ta koma d’akin ta ta zare hijjabin da ke kanta ta hau gado ta kwanta .

Mama ko da ido tabita.

Kwance yake bisa tafke ken gadon sa sai juyi yake ya hurga k’afa can d’aya can ahankali ya gama bud’e idanuwan shi yad’aura su kan a gogon dake manne jikin bangon d’akin, ganin eight saura yasahi saurin mik’ewa don yatina zaikai ma Baba abinci mik’ewa yayi ya fad’a bayi don yin wanka ……..
[11/21, 7:15 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

           ????????????????????
                 ????????????
                         ????

SAMHA

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Story nd writing by
Khadeejatou Muhammad

Dedicated by ummaima Aliu wannan page din nakine gaskia inajin dadin comment din ki Allah yabar zumunci

Page 2⃣5⃣

Bissimillahi Rahmani Rahim.

Mik’ewa yayi ya fad’a bayi bai jima ba yafito yana tsane jiki da wani farin towel, wajen dresin mirror ya k’ara sa mai yashafa ko ina na jikin sa ya feshe jikin sa da turare, wardrobe ya bud’e ya jawo jallabiya me ruwan toka da vest fara ya saka k’ara feshe jikin shi yak’ara yi da tirare ya d’an k’ara taje kan sa da kum, d’aukan wayar sa yayi yafita.

Dai-dai lokacin Mama tafito sanye cikin doguwar jallabiya pink colour tayi kyau sosai ,cike da fara’a take duban shi.

Shima fara’a ya sake mata.

Yace “ina kwana Mama antashi lafiya?

Tace “lafiya k’alau my son.

Kujera yasamu ya zauna,itama zama tayi tace “yau lafiya ka tashi da wuri?

Yace “lafiya k’alau Mama abinci na tashi in kai ma su Gwaggo naga har tara saura”.

Tace “ai naba ma driver ya kai masu na d’auka ka manta”.

Yace “wallahi Mama bacci ne me nauyi ya d’auke ni bud’e ido kawai naga eight yayi”.

Tace ai dole kaine inka tashi da safe ko d’an irin bacci nan ba kayi kuma fa wai kazo hutu ne ahaka zaka k’are hutu baka huta ba ina ganin”.

Murmushi yasake tare da cewa Mama ni ban iya baccin rana kamar wata mace nafi so inyi na dare”.

Samha ce ta fito sanye cikin doguwar riga bak’a da d’an k’ara min hijjabin ta da bai wuce guywa ba fari tayi kyau sosai k’ara sowa tayi ta duk’a har k’asa tace “Mama ina kwana?

Mama tace “lafiya k’alau Daughter”.

Tadube Salman da ya lumshe idanuwa tace” Yaya ina kwana?

Ahankali ya bud’e idon shi ya sauke akan ta saida gaban shi yace dumm yai saurin kawar da kai yace lafiya”atakai ce yayi maganan.

Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da zobe ya tsunata.

Mama ce ta katse shiru tace “kutashi muje ai break”.

Mama tafara mik’ewa Samha ma ta mik’e sukai dinning, mik’ewa yayi ya bi bayan su lokacin Mama har ta zuzzuba musu.

Zama yayi yafara ci ahankali, Samha ma ci take cike da yanga kamar batason ci, Mama ma zama tayi ta fara cin nata.

Ba’abin da kake ji sai k’aran cokula.

Ringing d’in wayar sa yasa ya kaste mai cin abinci,sa hannu yayi a cikin aljihu ya fiddo wayar sunan da yagani jikin screen din wayar yana yawo ne yasa shi sakin mur mushi d’aga wayar yayi yasa akunne yayi shiru

Acan b’an garan tsaki Dr Abbas yasaki tare da cewa “kai fa tsiyana da ki d’an rainin wayone kud’i fa na saka ba bonus ba”.

Salma ko gintse dariya sa yayi yace “miye da sassafe ake damuna tun ban kar yaba”.

Tsaki Dr yak’ara yi tare da cewa “nide katashi ka kai mata waya ina so naji muryanta”.

Yace “wa kenan?

Tsaki ya k’ara saki nifa ban san iskanci k’anwata mana”.

Yace ai k’anwan taka tana gidan ku.

Dr afusa ce yace “Samha”.

“Ohh ni zam bata waya tou baku isa ba” yana gama wayar ya katse kiran yana murmushi.

Mama tace “kai kuma dawa?

Yace” nida Dr ne “.

Mama tace “kunfi kusa”.

Dr ta ko yana office zaune yacika fammmm.

Kuyi manage
[11/21, 7:16 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

           ????????????????????
                 ????????????
                         ????





         *SAMHA*

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Story nd writing by
Khadeejatou Muhammad Basheer Basskkwace

Dedicated by Samha fans,Izzar mulki fans, Gaskiya writing fans

Page 2⃣6⃣

Bissimillahi Rahmani Rahim.

Dr ko yana office zaune yacika fammm sai tsaki yake ja zuciyar sa na masa zafi.

Ab’angaran Salman kou murmushi yakeyi lokaci-lokaci harya gama cin abincin sa ya mik’e ya koma falo ya ya kwanata kan kujera.

A’ban garan su Inna Larai ko takai Zainab gyaran k’afa an dawo da ita gida ita kemata komi sauk’in ta ma akwai sauran kud’in da Salman yabata itama Zainab d’in akwai kud’i awajen ta taba ma Inna Larai taje ta siyo musu kayan abinci da kayan shayi da ruwan gora.

Gwaggo ko ba’a da take sai kula da Baba kullum sai ankawo musu abinci daga gidan su Salman duk da ya aiko masu da kayan abinci.

Salman ne kwance kan kujera three sitter yana kallon tashar MBC action hannu sa d’auke da remote.

Mama ce tashi go falon d’auke da jaka ahannun ta tasa gyale ta dibe shi tace “ashe kanan kwance”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button