SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sauri ta k’arasa ta run gume ta tana fad’in, “Mom burina ya cika Dad ya d’aura min aure da Salman gashi ana nuwa a gari kowa yana gani kai tsaye”.

Mom duba takai ga tv dai-dai lokacin da Salman ya mik’e kamar zaki ya ansa speaker a hannun Limam yace,” ni Salman Sulaiman D’ingyad’i na saki Lubabatu Labaran saki uku sabida aure dole baban ta yamin sabida yana matsayi abokin Baba na”.

Lubabatu da taji saukar maganan kamar duran kibiya a zuciyar ta tafiya tayi luuuuuuuuu ta zube kasa a sume.

Mom a kid’ime tayo kanta ta na jijjigata,da gudu tai kitchen ta bud’e firichi ta d’auko roban ruwa tayo waje duddule nata tayi duk a jiki amma ko motsi batai ba d’akin tayi da gudu ta d’auko wayar ta ta danna number mijinta.

Mama ko ta idar da sallah kenan ta jiyo d’aura auren ran ta ya b’aci mik’e wa tayi ta fito falo ta d’auka wayar ta ta kira Alhaji Taheer k’anin baban Salman,sai ta jiyo Salman na saki,bata san sanda murmushi ya sub’u ce mata ba
[11/21, 7:17 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

           ????????????????????
                 ????????????
                         ????

????SAMHA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Story nd writing by
Khadeejatou Muhammad

Dedicated by ummaima Aliu wannan page din nakine gaskia inajin dadin comment din ki Allah yabar zumunci

Page 2⃣9⃣

Bissimillahi Rahmani Rahim.

Wayar ta ta d’auka zata kira Alhaji Taheer k’anin Baban Salman ta sanar dashi abin da ke tafiya ,sai ta jiyo Salman na saki,take wani murmushi ya sub’u ce mata,zama tai akan kujera tana ta murmushi da wayar ta ahannu ta na jujjuya wa.

“Assalamualaikum” cewar So alm.

Tace, “wa’alaikumusalam, d’an albarka”fusakar ta da murmushi take maganan.

K’ara sowa yayi ya zauna gefenta yana maida numfashi gami da lumshe idanuwan shi.

Mama ko rik’o hannuwan sa tayi duka biyu kafin tace,”lallai Salman kaci ka d’an halak naji dad’i da ka nuna masa bai isa dakai ba,tun da bai haifeka ba shi kuma ba dan ginaba,balle na mahaifin ka ta d’an nisa kafin tace Allah yayi ma albarka”.

Murmushi kawai yayi yace,”ameen uwata-uwa ta gari”.

Dai-dai lokacin Samha tafito ciki doguwar riga na atamfa da hijjab d’in ta har k’asa,gaida Mama tayi kafin ta gaida shi,waje ta samu ta zauna ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace, “Mama”.

Mama tace,”na’am Daughter” ya aka yine?

Tace, “lafiya k’alau dama ina so inje gidan mu inga Babana”.

Mama tace, “tou shikenan ki tambaye Yayan ki sai ya kai ki,in kuma driver kike so ya kai ki sai asa ya kaiki”.

Shiko yana jin tace zata je gida azuciyar sa yace mara kunyar banza mara kunyar wofi bari in ga zata iya tambayata.

Ita ko Samha tana ji ance ta tambaye shi taji wani kala a zuciyar ta,tace lallai kam bazan je ba ashe ace ma fitar in zanyi sai na tambaye wannan me fuska biyun sai kace mijina.

Mama ko da taga tayi shiru tai tinanin k’ila nauyin shi take ji tai murmushi irin nasu na manya tace,”tou tunda kin kasa tambaye shi bari in aran miki baki inci miki albasa”,duba Salman tai tace, “Son dan Allah kakai Daughter wajen Baban ta kaji”.

Murmushi yasake idon shi a lumshe yace,”Mama ita bata da baki ne , dasai ke zaki tambaya mata?

Had’e rai Mama tayi tace,” “kai bani son iya shege in zaka tashi kashirya ka tashi kashirya ka kai ta ta ga mahaifin ta ehee”.

A ran shi yace lallai yarinyar nan nizata sa Mama tai tamin masifa,wallahi sai ta gane kuren ta k’wafa yayi tare da mik’ewa fuuuu yayi d’akin shi.

Mama duban Samha tai tace,”keku ma daga yau in zaki fita kirink’a tambayan shi da kanki,ki d’auke shi a matsayin Yayan ki kamar uwar ku d’aya uban ku d’aya kide najin nauyin shi da kunyar shi keda shi duk d’aya kuke awaje na”.

Tace, “tou Mama na gode”.

Dad din Lubabatu kuwa yana tsaye kamar mutum-mutumi duk mutane da ya gayyato sun watse kowa da abin da yake fad’a saura tsiraru da ga cikin su ko har da y’an jaridan da ya gayyato.

Niko nace uhmmm su khadeeja Abba yakubu da Amratu Mukhtar abin nema yasa mu sai anga k’wak’waf kafin a wuce gashi kai tsaye suke gwada dauka d’an jarida badai gulma ba.

Wayar shine take ta ringing ba k’ak’k’autawa sai da Alhaji Saminu ya k’ara so kusa dashi ya tab’a shi.

Firgi-git ya yi alaman tunanin shi bai kusa, kallon Alhaji Saminu yake kamar bak’on halitta kamar yau yafara ganin shi.

Yace, “Alhaji Labaran wayan ka fa tun d’azu take k’ara tuna nin me kake haka?

Shiko daya zuba ma Alhaji Saminu ido a cikin zuciyar shi yace, ji wanan Alhaji Saminu d’an rainin wayo ne in ba rainin hankali da mida ni mahaukaci ba wai tambayata yake mi nake tunani haka, k’ara wayar ne yaka tse masa tuna nin zuci saurin fitowa sa hannu yayi a aljihu ya fiddo wayar ganin me d’akin sa ne yasa gaban shi yace dummmm hannu na rawa ya d’auka yanafad’in, “miya farune?

Cikin kuka Mom take magana tace, “kazo ta mutu ka kashe ta ta mutu “k’it ta kashe wayar ta koma kan Lubabatu tana ta girgiza ta tana kuka ga y’an aiki tsaye carko-carko harda me gadi.

Alhaji Labaran ko da gudu ya fad’a motor sa ya mata wuta acikin minutes ya isa Yahaya road hon yake amma ba me gadi ficewa yayi
munafukar uwar shi.

Mom ko tana ganin shi ta k’ara rushe wa da kuka tace,”shikenan Alhaji ta mutu ita kad’ai na haifa ita kad’ai ce k’waina a duniya”.

Tsawa ya buga mata tare dace dalla ki min shiru kin ishe ni da koke-koke asbiti yaka mata ki nufa da ita a tabbatar ta mutu ko tana raye” cin-cibar ta yayi ye waje da ita dai-dai lokacin Alhaji Saminu da y’an jarida suka k’ara so k’ofar gidan, cikin motor ya sata baibi ta kan kowa ba yashige yayi ma motor wuta sai Garkuwa Hospital yana parking ya fita da gudu ya na k’walla ma nursing kira kowa kallon shi yake kamar sabon mahaukaci.

Wata nurse ce tace, “love Alhaji?

Tsaki yaja tare da cewa “dalla kuzo y’ata ta sume ku shigo da ita Dr ya duba ta in ta mutu ne yau shima ba zai kwana duniya ba wallahi”.

Tab’a b’aki tai kusan nurse da iskanci tace, “tou security zakai ma magana”.

Wani ca Kuma ya mata saida idanuwan ta suka firfito da k’yar wasu maza suka k’wace ta.

Shiko numfashi kawai yake maida wa yana nunata da d’an yatsa amma ya k’asa magana.

Juyawa yayi ya koma cikin motor ya cin-cimota yayo ciki da ita idon shi na sauka akan emergency room nan ya nufa da ita ya aje ta kan gado yafito yaje bakin Office d’in Dr bugu yake ba k’ak’k’autawa.

Asuk’wane Dr yafito yana fad’in, “lafiya?

Rik’o kwallar rigar shi yayi yana janshi har cikin emergency room yanu na masa Lubabatu dake kwance ba numfashi yace, “kadawo min da ita yanzun nan kar kace min ta mutu”.

Dr daya kwalalo ido yana kallon shi cike da mama kin K’arfin hali irin nashi yace, “tou sakar ni kai waje”.

Yace, “wallahi na rantse ma ba inda zani ai komi a gabana”.

Dr ko had’e rai yayi yace,” tou nikuma bazan duba ta ba tun da ka iya sai ka duba ta” ya juya zai fice.

Dank’o rigar sa yayi yana fad’in, “wallahi baka isa ba sai ka duba ta y’ata k’wal tin k’wal ita d’aya na haifa wallahi in ta mutu likita bazan boye ma ba sai na kashe ka kai ma”……..!

Kuyi manage
[11/21, 7:17 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

           ????????????????????
                 ????????????
                         ????

????SAMHA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button