SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shafo fuskar ta yayi da hannun dayake da lafiya shima murmushi yace “Samha nayafe miki kuma naji dad’i da kikace zaki bishi,Allah yamiki albarka,Allah yabaki ‘ya’ya masu miki biyayya kamar yanda kike min da kuma miji na gari”
Kunya yakamata ta rufe ido tare da kwantar da kanta kan cinyoyin Baba.
Murmushi kawai Baba yayi yashafa kanta,duban Salman yayi yace “Salmanu kutashi kutafi gida dare nayi fa”
Salman murmushi yayi tare da fad’in” Baba koran mu kake har ka gaji damu toh nidai ina nan bazan tafi yanzu ba sai Drive ya kawo ma amaryan ka”yak’arashe magana yana murmushi.
Baba ma murmushi yayi yace kafin yace “ba koran ku nake ba naga dare ya soma ne,ita ni mukwana anan”
Murmushi kawai Salman yayi.
Atsakar gida ko Inna Larai tana nan zaune tafito shan iska d’akin ta zafi ga sauro sai tajiyo tsayuwar motoci k’ofar gidan su nan aka bud’e akafara fitowa hayaniya takeji almar amarya aka kawo,ta’ba baki tayi tace “ko ina akai biki oho,” bata gama maganan zuci ba,tajiyo gud’a kuma alaman gidan za’a shigo,mik’ewa tayi tare da dafa k’irji tare da zaro k’ananun idon ta ,afili ta firta wayayi aure kode ‘batan hanya sukayine don bamu da saurayi a gidan nan wannan dai nakasashen tsohon bawan da zai aure shi,bata ankara ba sadai taga mutane sun shigo sun doshe d’akin Baba……….!
wai yazata kayane gashi dai an kawo amaryan Baba yazata kwashe kubiyoni dan jin yanda zata kaya.
[11/21, 7:11 PM] Sumayya: ????????????????????????????
????????????????????
????????????
????
???? *SAMHA* ????
®
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION•
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira }.
????G•W•A
????
GASKIYA DOKIN ƘARFE ????????
Written by
khadeejatu Muhammad
Dedicated by Habeeby????????
PAGE
Bismillahir Rahmanin Raheem
Afili ta furta wayayi aure kodai ‘batan hanya sukayi ne don bamu da saurayi a gidan nan,wannan dai naka sa shen tsohon bawanda zai aure shi yayi jinyar shi,bata ankara saidai taga mutane sun shigo sun doshe d’akin Baba,bawan da ya kula da ita,wani ashhar ta lailayo ta ta maka musu.
Tsayawa sukai cak suna duban ta,d’aya daga cikin wa’yanda suka shigo da amarya tai k’arfin hali tace “haba baiwar Allah lafiya ki d’aya baki ansa sallama ba sai ashar”
cikin masifa da jaraba tace “ba’a koyamin ba,miye wannan kuka lillibo kamar gawa?”.
Amaryan ta yaye lullu’bin ta,dai dai lokacin Salmanu ya bud’o ‘kofar zai fito tsayawa yayi yana ganin ikon Allah.
Amarya kuwa takawa tayi ta k’arasa inda Inna Larai ke tsaye cikin kakkausar murya tace “kingan ni dakyau koh ba so kike kiganni ba ,ba gawa bace Gwaggo Dije ce kuma amaryan Malan Salis”
Matan wajen suka d’auki gud’a ayiririri kawai kake ji na tashi.
Wani ashar ta kara lailayo wa ta watsa ma Gwaggo Dije.
Gwaggo ko ranta ya ‘baci tacire gyalen da ke kanta ta d’aura a k’ugu,tasa hannu ta fin ciko wiyar rigar Inna Larai tajata k’iyyyyyy har bakin rijiya igiyar guga ta dauka ta ringa shim fid’a mata a jiki.
Amma ina bakin Inna Larai bai mutu ba zagi kawai take.
Niko da nake gefe don d’auko muku rahoto nace cabd’i dama Inna Larai ba karfi gareta ba,inta raina ka shikenan kullum tai tasaka a gaba tana zagi .
Wata daga cikin matan ne tazo da sauri tana k’ok’arin k’watar ta don tasan halin Yayar ta zata iya barinta kwace.
Salman ko nadaga jikin k’ofa ya jingina ya nad’e hanna yensa akan k’irjin sa yana ta murmushi me kama da na mugunta.
Itako Gwaggo Dije dukanta kawai take kamar tasamu ‘yarta,Inna larai koh zagi yak’i barin bakinta.
Daƙyar wannan da tazo tai makon ta ta k’wace ta.
Inna larai tana ganin haka aiko ta hankad’a wancan tai taga-taga zata fad’a rijiya.
Da sauri Gwaggo Dije ta fincikota tai gefe, sa hannu tayi da niyar k’ara kamota.
Da gudu ta juya wa ‘yanda suke hanya ma ta bubbuge su d’akin ta ta fad’a ta maida Ƙofar ta ta langa-langa takulle ‘bam da sakata.
Dariya akasaka Gwaggo Dije koh tana huci tazo jikin k’ofar tana bubbugawa tana fad’in “mara kunyar banza mara kunyar wofi ki bud’e kigani da sai kin fi biredi laushi”.
Inna larai koh daga cikin d’akin tace bana bud’e wa kuma wallahi kinci bashi sai na rama saikin gane ruwa ba sa’an kwando bane”.
Gwaggo Dije ta kwashe da dariya tace “dakika ga an ceceki a wajena ba dole ki fad’a haka saina gyara miki zama jakar mata kawai”
Kwance d’amarar tayi tadube wa’yan da sukai mata rakiya duk ita suke kallo suna mamakin k’ar fin halinta yau daga kawo ta ko d’akin mijin bata k’arasa ba zane masa mata, tace “mushiga da ga ciki”
Juyowar da zatayi sukai ido huɗu da Salman,harara shima ta galla masa.
Murmushi ya sake ya k’araso inda suke tsaye yace “Gwaggo sannu da k’arfin halin zane matar gida”
Murmushi tayi tare da fad’in”ita tajawo waya ce tashiga harkata kad’an nai mata ma wallahi ,nikasan banason raini bana shiri da mutumin da baida mutunci “
Murmushi ya k’ara saki yace “Gwaggo dije ikon Allah,maganin maza da na mata,maganin tsagerun kishiyoyi,muje in kai ki ga angonki”.
Murmushi tayi ta dube ‘yan uwanta tace “muje”
Salman duban su yayi d’aya bayan d’aya yace “Gwaggo yamu kayi dake, gaskiya ba wanda zai shiga saboda hayaniya kin san kuma baison hayaniya”……!
Comment N Share
[11/21, 7:13 PM] Sumayya: ????????????????????????????
????????????????????
????????????
????
???? *SAMHA* ????
®
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION•
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira }.
????G. W. A????
GASKIYA DOKIN ƘARFE ????????
Writing by
khadeejatu Muhammad
Dedicated by Umaima Aliu
PAGE
Bismillahir Rahmanin Raheem
Salman ko sallama yayi musu shima ya fita yana fad’in “gwaggo Amarya gobe zaki ga sak’o”.
A bakin motor ya isketa ta tsaya ,da alama jiran shi take motor ya bud’e ya shiga itama shiga tayi, ya tashi motor suka kama hanyar malali,tafiya suke ba wanda ya ce uffan har suka isa gidan me gadine ya wangale musu get ya danna hancin motor cikin gidan wajen packing ya nufa yayi packing motor ya bud’e ya fita itama bud’e wa tayi tafito kafin ya kulle motor,yana gaba tana binshi abaya har cikin falon,akan kushin suka iske Mama a zaune tana kallon tashar bollywood.
“Assalamualaikum”.
Cewar Salman.
“Waalaikumusalam”. Mama ta amsa dashi tana me duban shi ganin da Samha yake yasa ta fad’ad’a fara’arta tare da mik’ewa tana mai taro ta.
Kunyace ta kama Samha tai saurin duk’ar da kai k’asa.
Mama ko cike da farin ciki take fad’in “sannu da zuwa sannu da zuwa ‘yata”.
Akunyace ta amsa da “yauwa Mama”.
K’arasa tai da ita ciki tare da zaunar da ita akan kujera,itama zama tayi a gefenta tana kallonta tana murmushi.
Salman ko tsayawa yayi ya nad’e hannayen sa akan k’irjinsa yawani b’ata rai da yaga alama yau Mama bata tashi tasami yarinya wucewa yayi bedroom d’insa fuuuuuuuu,da ido ta bishi murmushi tayi don ta gane kishi yake.
vote
share
vote
[11/21, 7:13 PM] Sumayya: ????????????????????????????
????????????????????
????????????
????
???? *SAMHA* ????
®
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION•
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira }.
????G. W. A????
GASKIYA DOKIN ƘARFE ????????
Writing by
khadeejatu Muhammad
Dedicated by
mrs Aliyu
ummu Hanash
ummu Nabeel
Hafsat musa
Aunty Sadiya
Innaro.
PAGE
Bismillahir Rahmanin Raheem