SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Salman ko tsyawa yayi ya nad’e hannayen sa akan k’irjin sa yawani ‘bata rai dayaga alaman yau Mama bata tashi tasami yarinya wucewa yayi bedroom d’insa fuuuuu da ido Mama tabishi tana murmushi don gane kishi yake.

Mek’ewa tayi tana me duban Samha tace Daughter ina zuwa,d’akin shi ta nufa tura k’ofar tai tashiga bata ganshi acikin bedroom d’inba da k’aran ruwan da taji abayi ya tabbatar masa mata da wanka yake,bin d’akin tafara yi da kallo girgiza kai tayi ganin kayan daya cire ya cilar da wan nan gefe daban wan can daban duk’a wa tayi tafara tattara masa kayan tana sawa a basket d’in dayake sa kayan wanki,gefen gadon ta dawo ta zauna tana jiranya fito tsawan minutes uku sai gashi ya bud’e k’ofar toilet d’in had’a ido sukai yasakar mata murmushi,itama murmushin ta mai.

K’arasowa yayi gefen ta ya zauna lokaci daya ya had’e ransa yana mai tsuke baki kamar k’aramin yaro kwan ciya yayi a bisa cinyar ta.

Murmushi tai tare da d’an tureshi cikin wasa tace niko d’agamin cinya kar ka karyani k’ato dakai.

D’agata yayi yana mai turo baki mik’ewa yayi.

Dasauri ta dank’o hannun sa tana mai fad’in “yi hak’uri my son dawo ka kwanta ai wannan cinyar takace kai kad’ai bada kowa ba”.

Make kafad’a yayi cike da shagwa’ba yace ” nak’i ban son wayo bakin sami yarinya ba shiyasa kikemin abu kala-kala nan gaba in aka kwana biyu mantawa zaki dani gaba d’aya”.

Dariya yaso ya k’wace mata yanda taga yana maganar kamar wani k’aramin yaro shanye dariyan tai tace “haba Salmanun Faris ni na isa in manta dakai, inna manta dakai ashe zan iya man ta masoyina Sulaiman kenan,kasan ita bak’uwa ce acikin mu mun d’auko ta daga wajen mahaifin ta kaga ko tazama amana awajen mu dole mubata kulawa da tattali yanda zataji dad’i mahaifin ta ma yaji dad’i hankalin sa ya kwanta”.

Sakin ran sa yayi kafin yace “ammani gaskiya-gaskiya Mama ba can-can ba zaki sota kar wata rana tafini matsayi a zuciyar ki don in haka ta kasan ce hmmmm Mamana” ya karashe yana murmushi .

Murmushi ita ma tayi tare da fad’in hmmm maine fad’a abin dake ranka Salman”.

Juyawa yayi yanufi dressing mirror yana fad’in “ba komi Mama sallah ishaa’i zanyi infito in ci abin ci”.

Mik’ewa tayi tana fad’in to sai kafito ai mana addu’a” ,bata jira mai zaice ba tasa kai ta fice .

Shima shirya wa yayi a gaggace mai kawai ya shafa ya d’auko jallabiyan sa fara ya saka inda ya tanada don yin sallah ya nufa ya kabbara sallah.

Mama ko datafito a in da tabarta nan ta iske ta zaune karasawa tayi cikin falon ta dubeta tace” tashi muje kiyi wanka kiyi sallah kifito muci abinci”.

Mik’ewa tayi cike da kunya Mama na gaba tana binta a baya wani d’aki tabud’e tashiga gefen nata itama shiga tayi zaro ido tayi gaban ta yabuga ganin kyawun d’akin da tsaruwan shi,Mama zama tayi gefen gado tace mata “ga bayi nan shi ga ki watsa ruwa akwai komi a ciki”.

Zare hijjab d’in dake jikin tayi ta nuke ta aje gefen gado Mama k’ura mata ido tayi ganin surar jikin ta a zuciyar cewa tayi mashaallah Allah yayi halitta anan.

Toilet d’in ta nufa murd’a k’ofar tai tashiga tsayawa tayi tana k’are ma bayin kallo don ita batasan yazatayi amfani da komai ba juyawa tayi ta fito m.

Mama dagowa tayi tana kallonta cike da alamar tambaya.

Sunkuyar da kai tai k’asa tace “Mama nifa ban iya amfani da bayinan ba ba kalan shi bane a gidan mu”.

Mik’ewa Mama tayi tana murmushi tace “muje in gwada miki”.

Juyawa tayi takoma Mama tabita abaya nuna mata yanda zatayi amfani da komai na ciki tayi kafin ta fito ta barta,wajen wardrobe ta nufa ta bude cike yake da kaya ta za’bo mata wata doguwar rigar atamfa ja mai ratsin fari ta aje mata akan katifa ta kalla gefen hijjabai ta ciro mata fari ta aje kafin ta kulle wardrobe d’in dadduma ta d’auka ta shim fid’a mata,kan kujeran dake d’akin ta koma ta zauna.

Samha ko bata jima ba tafito sanye da kayan da ke jikin ta ta mayar don a tuna nin ta batazo da kaya ba.

Mama da ido ta bita tare da waro ido ganin kayan da tacire ta maida tace “Daughter baki bakiga towel bane kika maida kayan da kika cire?

Shiru tayi tare da sunkuyar da kai.

Murmushi Mama tayi tace to ga kaya nan na fito miki dasu kishirya kiyi sallah kifito falo muna jiranki muci abin ci tana fad’a bata jira me zatace ba ta sakai tafice

Samha ko bin kayan tayi da kallo karasawa tayi wajen wardrobe ta bud’e cike da mamaki take kallon tarin kayan ciki wai wa innan duk nata ne sa hannu tayi ta ciro pant da bra masu launin ja ta aje kan gado ta kulle wardrobe d’in wajan madubi ta k’arasa ta tsaya mayuka kala kala da turaruka da kayan kwalliya gasunan duk anjera basilin ta jawo ta bud’e ta fara shafawa azuciyar ta tana fadin dakai nasaba saboda haka kai zan shafa a gur guje ta shafa towel din da tagani kan kofar wardrobe shi ta jawo ta d’aura kafin ta cire rigarta sa bra d’in tayi taga yamata cif tace “kamar ansan dai-dai nine aka za’bo min d’aukan doguwan rigar ta ta zura aiko cifff shima yama kamar angwadata hijjab ta zura mashaallahu don gaskiya tayi kyau sosai inda mama ta shimfid’a mata dadduma ta nufa ta tada sallah da ta idar da sallah bata mik’eba ta jima tana ma mahaifinta addu’a samun lafiya da zama lafiya a auren su da Gwaggo Dije kafin tamike ,sada ta koma bakin madubi ta feshe jikinta da turare kafin ta fito.

Shima dai-dai lokacin yashigo falon,kalon-kalo sukai take yaji gaban shi yace dummmmm……..

comment
vote
nd
share
[11/21, 7:14 PM] Sumayya: ????????????????????????????
????????????????????
????????????
????

      ???? *SAMHA* ????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira }.

????G. W. A????
GASKIYA DOKIN ƘARFE ????????

Writing by
khadeejatu Muhammad

Dedicated by Basakwace Families

PAGE2⃣1⃣

Bismillahir Rahmanin Raheem

Shima dai-dai lokacin yasawo kai cikin falon kalon-kalo take yaji gaban shi yace dummm,saurin d’auke idon shi yayi baisan miyasa ba indai yaganta zuciyar shi sai ta buga.

Itako sunkuyar da kai tai kamar muna fuka jiki a sanyaye ta k’arasa cikin falon ta zauna a k’asan kafet.

Shiko kujera ya zauna yana me sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido.

Mama datafito daga kitchen kallon shi take tare da fad’in “Salman lafiya miya same ka kuma?

Murmushi yayi yana mai bud’e ido asan yaye yace “bakomai fa Mama jiranki nake kizo muci abinci”.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da fad’in Alhamdulillah wlh ban san inganka cikin damuwa”,juyawa tayi ga Samha da take zaune ta takure kan ta waje d’aya tace” ke kuma lafiya?, ga kujeru kin zauna a k’asa bani son haka kuma baniso in k’ara gani kefa ba bak’uwa bace yar gida ce”.

Batace komai ba saima k’ara duk’ar da kai da tayi.

Salman ko ta’ba baki kawai yayi ya mik’e yanufi dining.

Mama ce tace “Daughter taso muci abin ci”.

Mik’ewa samha tai Mama na gaba tana binta a baya har dining,kujera Mama ta ja mata tace “zauna nan Daughter”.

Zama Samha tayi kan ta asunkuye.

Mama ta zuzzuba musu abin cin tuwon shinka fa ne miyar shuwaka taji kayan ciki,sai kunun aya me sanyin gaske, kowa tazuba masa ta tura masa gaban sa kafin ta zauna ta fara cin nata,Salman ma cinashi yake yana korawa da kunun aya hankalin shi kwance.

Samha ko jujuya cokalin kawaitake ta kasa kai koda loma d’aya cikin bakinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button