SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mama ce da ta lura da haka tace “yana ga baki ci komai ba Samha”.

Ahankali ta furta “ina ci fa Mama”.

Gwallo ido Mama tayi tare da fad’in” me kikaci anan kosai na d’ura miki ne”.

Murmushi tayi tana k’arasa duk’ar dakai k’asa tace “Mama zanfa ci dakai na yanzu”.

Mama tace “to fara tukafin kisha d’ure”.

Fara ci tayi ahankali don ita kunya ma takeji da zasu gane da sun barta ta d’auke nata ta tafi dashi d’aki taci.

Salman ko harya gama da nashi kora sauran kunun ayar yayi ya mik’e.

Mama ta dube shi tace “harka k’oshi a k’ara maka mana”.

Girgiza kai yayi alamar ya k’oshi haka tare dafadin “saida safe Mamata ki kula da kanki”.

“Allah yakaimu”,cewar Mama.

Wucewa dakin shi yayi,yarage daga Samha sai Mama kowa cin abincin shi yake.

Koda Salman yashiga d’akin sa wayar sa yafara dubawa kira yagani rututu da sauri ya duba ganin me kiran yaja tsaki yamaida wayar ya inda take hawan kan tafkeken gadon sa yayi yakwanta tare da lum she ido.

A’ban garan Samha ko batawani ci sosai ba ta mik’e tai ma Mama saida safe ta nufi sabon d’akin ta cire kayan jikin ta tayi tad’auko wasu kayan bacci riga da wando farare ta saka ta hau kan gadon saida tayi azkar ta ta shafa kafin ta kwanta,tunanin mahaifin ta kawai take tunawa datayi yana tare da Gwaggo Dije zata kula dashi yasata yin murmushi tare da jan bargo.

A’bangare Inna Larai ko takasa zaune ta kasa tsaye duk ta k’osa safiya tayi zainab ta dawo taga cin amana da rashin mutunci irin na Sale ita zaima kishiya su tare asabna gini da bata ta’ba shigan shiba wlh ko dole ayita ta k’are jawo wani tsumma gyalen ta tayi dayake kan sanda gado taci d’an mara,bude k’ofar tayi tafito k’aton dutse ta samu ta nufi kofar d’aki ji kake kwas-kwas-kwas bugu kawai take ba k’ak’k’autawa.

Daga cikin dakin Gwaggo Dije da Baba suka jiyo bugun k’ofa don lokacin Gwaggo harta temaka masa takai shi kan gado tana gyara masa kwanciya ne.

Kalon-kalo sukayi Baba yace “je kiduba kiga waye da tsohon daran nan”.

Gwaggo ta amsa da to ta fice bud’e k’ofar tayi wazata gani inbanda Larai taci d’amara abin dariya yakusa bata sai kuma ta dake tasha kunu tare da fad’in “lafiya zaki zo kina buga ma mutane k’ofa ko bak’in ciki kike naki baikai nawa ba”.

A harzuk’e Larai tayo kanta ta jawo ringarta tare da fadin don kan babban bura’uban ki yau sai kinbar d’akin na karu…..

Bata kai da k’arasa wa ba Gwaggo ta bata naushi abaki tare da fin cike rigar ta tana ta tura ta da k’arfi ta fad’in timmmm a k’asa ta maida k’ofar ta k’ulle.

Larai ko da baki yagama wankewa da jini gashi ta tureta ta fad’in kan hannunta wani wani azaba taji ya ziyar ceta dakyar ta mike ta lallaba tashige d’akinta tana tsine ma Gwaggo.

Gwaggo ko datakoma ciki ya tambaye ta waye cemasa tayi bata ga kowa ba addua tayi masa ta tofa masa ta gyara masa bargo tace masa saida safe ya kwanta ya huta,bayi ta shige ta d’auro alwala don gabatar da nafila koda tafito har bacci ya kwashe shi murmushi kawai tayi ta d’auke dadduma tashimfid’a
[11/21, 7:14 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

      ????????????????????


              ????????????

????SAMHA ????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Written by
KHADEEJATOU MUHAMMAD

DEDICATED BY
BASAKKWACE FAMILY

Page 2⃣3⃣

Bissimillahi rahmani raheem.

Bud’e ko’far tayi fuska d’auke da murmushi.

Shima murmushi yake mata bashi hanya tayi ya shige ta koma ta datse k’ofar.

Inna Larai ko acikin wa’yanda suka zo kallo wasu daga ciki suka taimaka mata don kai Zainab wajen d’auri.

Gwaggo ko duban Salman tayi da yake aje basket d’in abinci tace “Ina ‘yata?nagan ka Kai kad’ai”.

Murmushi yayi yana zama kafin yace “ni baza ki tambaye ni ba sai ‘yarki na lura daga ke har Mama juyamin baya kuke da niyar yi akan wancan yarinyar”.

Dariya Gwaggo tasa kafin tace “Salman ai tini mun dena yayin ka jibeka k’ato da kai kaƙi aure ka zauna sai ka gama tsufa a gari wallahi zanje in sami Hajiya ta shirya muje k’auye a ne moma cikin dangi a d’aura ma”.

Tsuke baki Salman yayi tare da turo baki.

Itako Gwaggo mai za tayi inba dariya ba.

Mik’ewa yayi zai tafi.

Da sauri Gwaggo ta mik’e ta ta kamo hannun shi tana fad’in haba Salmanul farisy wasa fa nike ma waya isa yaje k’auye yama aure ai ba’a haifi matar ka ba ‘yar k’asar saudiya ce”.

Shima dariya yafara.

Ganin ya fara dariya Gwaggo tace “to dawo ka zauna mu gaisa”.

Koma wa yayi ya zauna a inda ya tashi yace “Gwaggo ina Baba?”.

Washe baki Gwaggo tayi tace “Salman sai kabari mu gaisa ko”.

Tsuke baki yayi kafin yace “antashi lafiya Gwaggo”.

Gwaggo ta amsa da “lafiya k’alau,ya Hajiya da d’iyata Samha?”.

Salman ya amsa da suna lafiya,ya bak’unta?”

Gwaggo murmushi tayi ta amsa da “lafiya”.

Salman ya ce Gwaggo ina Baba?

“Bai tashi ba “cewar Gwaggo.

Salman yace “ok ga abincin kunan ni zan tafi in ya tashi ki gaishe shi zan dawo kawo muku na rana”.

Had’e fuska tayi kafin tace “Kai Salman kaki yaye ni niba yarinya bace da za kace za’a ringa kawo min abinci in zaka aiko min da kayan abinci ka aiko min toh don ba zama nazo yiba aljanna nazo nema” tak’ara she maganan tana me tsuke baki.

Abin dariya yaso ya bama Salman sanin halin Gwaggo ta iya kwakkwad’e shi yasa ya shan ye dariyar kafin yace” to Gwaggo za’a kawo insha Allah anjima in Allah ya kai mu”.

Murmushi tayi tace “ko kaifa Allah yayi albarka”.

Mik’ewa yayi tare da fad’in “Amin Gwaggo ki gaida min shi inya tashi kuma ki kula min dashi sosai”.

Harara wasa ta galla masa kafin ta ce “kaki yaye ni wai ahaifi mutum gaban ka yazo yana ma iyayi”.

Dariya yayi tare da cewa “nidai na wuce”.

“Toh ka gaida Hajiya”.

“Zataji” ya amsa a tak’ai ce, sa kai yayi ya fice ita kuma ta shige uwar d’aki.

Tuk’i yake hankalin shi kwance dai-dai kwanar gidan su wata motor tazo tasha gaban shi.

Saurin taka burki yayi jikake k’iyyyyyyyyyyy………

Kuyi
Hak’uri da wannan
[11/21, 7:14 PM] Sumayya: ????????????????????????????
????????????????????
????????????
????

      ???? *SAMHA* ????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira }.

????G. W. A????
GASKIYA DOKIN ƘARFE ????????

Writing by
khadeejatu Muhammad

Dedicated by My lovely kakus

PAGE2⃣2⃣

Bismillahir Rahmanin Raheem.

Washa gari da sassafe Inna Larai ta fito ta zauna k’ofar d’aki ba sallah ba salati balle wanke fuska,turo d’auri tai gaba gabakin nan yayi tsororo kamar na aunty baby sabida bige mata bakin da Gwaggo Dije tayi ga hannu ya isheta da zogi har ya tasa,k’ura ma k’ofar d’akin su Baba tayi ido jira take su bud’e tafara bala’i har takwas tayi shiru tsaki tai tamik’e ta nufi bayi ko buta babu.

Gwaggo Dije ko da asubah fari ta tashi tayo alwala tai nafila tarik’a addu’o’i ,sai da taga saura minutes biyar afara kiran sallah kafin ta mik’e ta nufi bayi ruwan wanka ta had’a ma Baba ta zuzzuba turarukan wanka fitowa tayi taje inda yake kwance zama tai bakin gadon ahankali tafara d’an bubbuga filon tana fad’in “malan! malan!! ahankali yafara bud’e idanuwan sa ya sauke akanta.

Gwaggo Dije murmushi ta sake masa tare da fad’in “ankusa kiran sallah bari inyima wanka da alwala kafin ashiga sallah”.

Gyada mata kai yayi batare da yace komi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button