SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Taimaka masa tai har cikin bayin fitowa tayi ta cire hijjab d’inta ta koma wanka tayi masa tare da mai alwala kafin ta taimaka masa yafito a kan gado ta zaunar dashi ,mai ta d’auko ta shafa masa kafin ta mik’e taje wajen wardrobe ta bud’e dogon riga jallabiya fara ta d’auko masa da gajeran wando da fanfas d’in shi na manya ta sa mai tayi kafin ta d’auko tirare ta feshe masa jiki dashi kan dadduma ta zaunar dashi.

Shiko binta da ido yayi yanda yaga tana kula dashi ba k’yama balle k’yan k’yami tana zaunar dashi kan dadduma yace “nagode Khadija Allah yamiki albarka”.

Murmushi tayi tare da fad’in bansan godiya nan komi kaga namaka ka cancanci haka ne,kayi sallah kamin addu’a anshiga masallaci”.

Murmushi kawai yayi ya kalla gabas ya tada sallah.

Gwaggo dije ko dayan dadduman ta d’auko ta shimfid’a ta tada nata sallah koda ta idar bata tashi ba saida tayi azkar kafin ta mik’e don ta kwantar da Baba nunke dadduma tayi ta ije kafin ta taimaka masa ta kaishi gado ta kwantar dashi ta nunke nashi dadduman tahada da nata ta kaisu inda ake ajewa,kitchen ta nufa ta ga komi tsaf tsaf ashirya duba store tayi taga ba kayan abinci falo ta koma ta gyara tsaf duk da baiyi dattiba ta kunna tiraren wuta kan kace me k’anshi ya cika d’akin har tsakar gida,koma wa tayi d’aki ta hau gado lokacin Baba har bacci ya kwashe shi jira take bakwai tayi ta buga ma Salmanu kira ya kawo musu kayan abinci don ita bazata amince dana siya ba ko ya rink’a kawo masu na gidan su har tsayawa sati d’aya ai ni nawuce yarinya.

Inna Larai ko koda tafito bayi k’afa duk jurwayen fitsari k’ara zama kofar d’akin tayi ta cuno baki gama.

Larai!Larai!!Larai!!!

Saurin kallon hanyar waje tayi jiyo muryar ‘yarta tana washe jajayen hak’oran nan tana fad’in “na’am d’iyar albarka.”

Dai-dai lokacin tashigo yau ma kamar kullum da ita da arniya ba maraba turus tai don ganin bakin uwatta cikin tsawa tace “Larai wacce ‘yar iskan ce ta duke ki”.

Murmushin takaici tayi tace “bakowa bace illa karuwan ubanki”.

Cike da masifa tace “wa kike nufi wannan kucakar bak’auyiyar yarinyan yau saita ban bance tsakanin aya da tsakuwa” bata jira me Larai zatace ba t nufi k’ofar d’akin bugu kawai take.

Gwaggo cikin bacci taji ana bugun k’ofa bana hankaliba mik’ewa tayi zumbur ta fito jiyo ashar d’in da ake k’undumo wa da kamar bazata bud’e ba sai kuma naga tayi kitchen muciyar tuwo ta d’auko tayo waje dashi bud’e k’ofar tayi bata kula ma da kowaye ba ta finciko ta ciki ta datse k’ofar komawa tayi ta datso k’ofar bedroom d’insu ta juyo kanta tana kallon ta.

Zainab kallon ta take cike da raini tare da fad’in” ke ke kuma waye”.

Murmushi tayi kafin tace “yanzu zaki san koni waye ba baki da tarbiya ba ballagazar uwar ki taturo ki kimin rashin kunya”.

Cike da rashin kunya tace gaki ballagaza wacce tazo d’akin na miji ta tare inba ka…..

Gwaggo d’anko kitson k’arin dokin kanta tayi ta rink’a dukan kafafuwar da muciya ihu take had’e da zagi bakinta yak’i mutuwa.

Itako Gwaggo kamar zigata take sai jibgar ta take.

Larai ko ganin an ja yarta d’aki dagudu tayi waje tana kururu atemaketa zata kashe ta kankace me mak’ofta sun cika tsakar gidan wanda dayawar su gulma ta kawo su sai bugun k’ofar Inna take tana k’undumo ashar kamar zata balla k’ofar.

Gwaggo saida tayi mata lilis kafin ta barta bud’e k’ofar tayi ganin mutane cike da gidan bai dameta ba illa cin cid’o ta datayi ta watso ta waje ko tafiya bata iyayi maida k’ofar tayi ta datse takoma kan kujera tana maida numfashi.

Inna Larai tai kanta tana fad’in “nashiga uku ta kakkarya min ‘yata wayyo ni Larai wannan tsinan yaro yakawo min jaraba cikin gida” wani ihu ta ‘barke dashi.

Masu bata hak’uri sunayi basu zugata sunayi masu Allah ya k’ara nayi.

Dai-dai lokacin Salmanu ya shigo da sallamar sa hannu shi d’auke da basket d’in abinci cike da mamaki yake kallo mutane dayagani cikin gidan suma kallon sa suke gaban shine yayanke ya fad’i ganin mutane k’ofar dakin baba azuciyar shi yace karde ace Baba ya matu da sauri ya kutsa cikin mutane ganin Inna na kuka ga mara kunyar ‘yarta kwance a yashe tanafitar da numfashi awahalce yasa shi sakin ajiyar zuciya.

Inna Larai na ganin shi ta mik’e tayo kanshi ta cakumo shi tana fad’in “Allah ya isa kakawo mana jaraba cikin gida shege tsinan ne Allah ya la’ance ka wlh sai kasan yanda kamin da ‘yata wancan mahaukaciyar da ka auro ma Sale ta karyamin ‘yata ita guda na haifa ita kad’ai ce ‘yata wlh ko wlh a gyara min ‘yata kamar yanda take ko inrama akan Samha”.

Tsura mata kyawawan idanuwan sa yayi yakasa cemata uffan sa hannu yayi ya ‘ban ‘bare hannunta daga jikin shi ya ra’ba ta gefenta zai wuce .

K’ara rik’o mai riga tayi tabud’e baki zatayi wani sabon ashar d’in.

Wani kallo ya watsa mata tai saurin sake shi tare kulle bakin ta.

Sa hannu yayi a aljihun rigar sa yaciri bandir d’in kud’i ‘yan d’ari biyar biyar ya kama hannunta ya dank’a mata su.

Mutanan da sukai carko carko kowa ya zuba masu ido cike da mamaki to waye shi wannan d’in.

ciro wayar shi yayi a aljihu ya dubo number Gwaggo ya latsa kira,ringing biyu ta d’aga,sallama.yayimata tare dafad’in Gwaggo bud’e min k’ofa,bud’e k’ofar tayi fuska d’auke da murmushi……..
[11/21, 7:15 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

      ????????????????????


              ????????????

????SAMHA ????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Written by
KHADEEJATOU BASAKWACE

DEDICATED BY
BASAKKWACE FAMILY

page 2⃣4⃣

Bissimillahi rahmani raheem.

Saurin taka burki yayi jikake k’iyyyyyy afusa ce ya b’alle murfin motor yafito taku yake kamar zai tsaga k’asa.

Dai-dai lokacin itama ta bud’e k’ofar motor ta sakko k’afafuwa waje fuskar ta d’auke da wani mayau darin murmushi.

Kallon-kallo sukai ido cikin ido ganin wacce tamai wannan iya shegen yasa ya k’ara had’a rai kamar bai tab’a dariya ba.

Yace “ke-ke dabba ce ko jaka wa wiya mai ruwan jahilai sonawa nace kifita harka ta amma kin k’iya nace bana so akai kasuwa”.

Wani ma yau darin murmushi ta sake kafin tace ,

“Baby wallahi-wallahi na rantse ma da uban giji bazan rabu dakai ba, bani da miji bayan kai sai na aure ka kaine uban ‘ya’yana,kuma wallahi duk shegiyar da ta kusan ce ka sai na kashe ta”.

Gwalo baki da ido yayi yana kallon ta kafin yace ,

” ah ko shakka babu kinyi kama da mahaukaciya, kin ganni ni Salman nafi k’arfin tamba d’ad’d’a irinki yau kina can gobe kina can kamar me aikin gwam….

Katse shi ta hanyar cewa “haba masoyina kana amin cewa da soyayya ta zan dena duk abin da nike har makaran tar islamiya zan koma”.

Tayi maga nan ne cikin kissa da kisisina.

Dariya ma maganar ta bashi ya kasa rik’e dariya sai da yayi mai isarsa,kafin ya had’e rai kamar bashi yagama dariya ba.

Yace”Lubabatu kenan ko kuma ince lubsy kin raina makan ki wayo wallahi kije kinai mi wanda zaki yaudara bani ba,don ni ba yaro bane kije kinemi yaro kimasa wayo kuma ina me k’ara jan kunne ki akan ki k’yale ni kifita harkata ban sanki-ban sanki ban k’aunar ki” yana kai wa nan be jira abin da zata ce ba ya shige motor sa ya juya ya canja hanya.

Tsayawa tayi sororo wani hawayen bakin ciki taji ya zubo mata masu d’umi jiki a sanyaye takoma motor ta tafi minutes goma kafi ta tada motor ta figeta a guje ta ke tuk’in ikon Allah yakaita gida, horn ta danna da k’arfi me gadi jiki na rawa yazo ya bud’e get d’in bai gama k’arasa bud’ewa ba tayi kansa da motor da gudu yayi gefe,bata k’arasa ba tai parking ko kashe motor batayi ba tafito da gudu tai hanyar falon su tana kuka tana k’walla ma Baban ta kira “Dady!Dady!!Dady!!!Dady nashiga uku bai sona”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button