SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace “eh wallahi Mama kallo nake”.

Tace “asha kallo lafiya bari in je saloon da kitso in dawo”.

Yace “to Mama ta ki dawo lafiya”.

Tace “Allah yasa”.

Ficewa tayi,shi kuma yaci gaba da kallon sa.

Samha ko na d’akin ta kwance tana tina nin Baban ta yau kwanan ta biyar kenan rabon ta dashi yanzu bawan da take son gani sai shi ,Mik’e wa tayi tafito falo da niyar in taga Mama ko Salman zata ce tana so taje gida,tana ko fitowa ta hango shi kwance kan kujera k’arasa wa tayi ta zauna one sitter tace “Yaya sannu da hutawa”.

A hankali yad’a go kai ya dube ta ya amsa atak’ai ce da “lafiya”.

Tace “Yaya”.

Shiru yayi mata kamar bai ji ba.

Atinanin ta baiji ba ta kuma cewa “Yaya”.

Cikin kakkausar murya yace “lafiya kike ta Kiran sunana kamar naci miki bashi.”

Shiru tayi ta duk’ar da kai bata kuma cewa komi ba.

Jin tayi shiru ya k’ara duban ta yace “ina jinki akwai damuwa ne?

Tace “dama sonike ka kaini in ga Baba na”.

Mik’ewa yayi ya zuba mata ido kafin yace “in kin ganshi mi zakimai?

D’agowa tai da sauri ta zuba mishi wani kallo.

Ganin kallon da take masa ne yayi saurin kauda kansa gefe tare da cewa “ban amin ce ba ba zaki ba”.

Wani k’ulu-lun bak’in ciki ne taji yazo mata k’afon zuciya ya toka re ma ta, mik’ewa tayi ba tare da ta kuma ce masa komi ba ta wuce d’akin ta.

Da ido yabita sai kuma yaji tausayin ta yaka ma shi.

Ita ko tana shiga ta kife kanta kan gado tana jin wani bak’in ciki bata san-san da hawaye masu dumi suka zubo mata ba,kanta taji yawani sara mata dafe wa tayi da hannu biyu tana rintse ido,take wani zazzab’i ya rufeta.

Shiko koma wa yayi ya kwanta yaci gaba da kallon sa,amma zuciyar shi na gareta yanda ya ta kalle shi da yanda ta mik’e ta tafi d’akin ta sai yawo yake masa a k’wak’wal wa da kuma idosa sam kallo ma ba fahimta yake ba mik’e wa yanufi d’akin ta ahankali ya tura k’ofar ya shiga zama yayi gefen gadon yana duban ta yace “Sister don Allah kiyi hakuri ki tashi ki shirya in kai ki”.

Ko d’agowa batayi ba ta dube shi balle yasan ta jishi.

Yace “kinji kitashi kishirya kin yi banza dani kamar da dutse nike magana”.

Nan ma shiru tayi ko motsi batayi ba.

Shiko ganin yana rok’onta tayi banza da shi yasa yaji ran shi ya b’aci a zuciyar shi yace lallai yarinyar nan nizatai ma raini don taga ma nazo in da take lallai zaki gane kuran ki.

Itako yun k’urin mik’ewa tayi don ta haye saman gadon ta kwanta taji jiri ya kwashe ta luuuuuuu zata zube a k’asa.

Saurin taro ta yayi tafado ajikin shi jin jikin ta yayi zafi saida yaji gaban shi yace dummmm

Ji da tayi bata fad’i k’asa ba yasa tayi saurin bud’e ida nuwan ta, ido cikin ido sukayi tsawan dak’ik’a suna ma juna kallon-kallo, saurin jaye idon ta tayi tare da yun k’urin k’ara mik’ewa ta tashi daga jikin sa dafa gadon tayi ta rarrafa ta haye taja blanket ta rufe jikinta tare da lumshe ido.

Shiko ji yayi jikin shi duk ya mutu duk wasu jijiyoyin jinin dake jikin sa sun daina aiki.

A cikin wata iriyar murya da ko ita kant bata san tana dashi ba tace “ka tashi kafitar min a d’aki bani son ganin ka acikin idon kasan zaka takura min me yasa karaba ni da mahaifina ka hanani ganin shi don haka ba’abin da zaka ce min ka mik’e kawai kafita.

Jiyayi zuciyar shi tamai zafi da nauyi azuciyar shi yace, lallal yarinyar nan nizata fad’awa magana har dawani in tashi in fitar mata a d’aki ba laifin ta bane nawa ne ashe bata da kunya haka, baisan ashe maganan dayayi ba a fili yayi ta.

Jiyayi tace “eh aidole kace banda kunya tunda karaba ni da mahaifina burinka yacika”.

Cikin tsawa yace “keee tou ya isa haka dalla”.

Banza tai dashi bata kuma cewa komi ba ta k’ara jan bargon ta rufe har kanta.

Tsaki ya yi ya juya yafita rai b’ace, d’akin shi ya wuce direct yafad’a kan gado take yaji haushin kansa yakeji da har ya tsaya yarinyar nan nafad’in masa magana be bubbgeta ba lallai taga gadon kwanan shi…….
[11/21, 7:16 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

           ????????????????????
                 ????????????







       *SAMHA*

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Story nd writing by
Khadeejatou Muhammad

Dedicated by ummaima Aliu wannan page din nakine gaskia inajin dadin comment din ki Allah yabar zumunci

Page 2⃣7⃣

Bissimillahi Rahmani Rahim

Lubabatu kuwa tana shiga d’akin mom tafad’a kan gado tana ta riskan kuka,wayar ta ta fiddo a cikin jakar ta ta danna number Dad d’in ringing biu ya d’auka a lokacin yana hotel shi da wata budurwan sa sun gama masha’ar su yana kwance shek’ek’e tsirara yana d’aga wa yace, “Daughter ya akayine?

K’ara bud’e baki tayi tana ihu.

Take hankalin shi ya tashi ya mik’e zubur yana fad’in, “Daughter ke da uban waye hajiya ta tab’a ki ko to wlh ki gaya mata ranta zai yi mummunan b’aci tunda tasaki kuka wallahi tabaki hak’uri tun kafin inzo gidan nan”.

Cikin kuka tace,”Dad ba ita bace”.

Yak’ara harzuk’a yace,”tou d’an gidan uban waye ya tab’a ki bai san ko ke ‘yar waye bane?

K’ara fashe wa tayi da kuka tace, “Dad yace bai sona ka aura min shi please Dad ina son shi”.

Yace, “wane d’an iskan ne yace baya son ki bai san ke jini na bace?

Tace ,”Dad yasani mana”.

Share hawayen ki ki fad’a min d’an gidan uban waye?,yau-yau d’in nan sai ya aure ki”.

Share hawayen ta tayi da bayan hannu kafin tace,”Dad Salman ne d’an gidan maragayi justice Sulaiman D’ingyad’i”.

Sai asa nan ya kwantar da murya yace, “kijira ni nan da awa d’aya za kiji labarin d’aurin auren ku”.

Take taji wani farin ciki ya mama ye ta tace,”yauwa Dad shi yasa nike alfahiri dakai komi nike so sai kamin dan Allah kayi sauri kaji”.

Yace,karki damu yanzun zan fita daga office in tafi inje in sami uwar tasa da anyi azahar za’a d’aura”.

Tace, “yauwa Dad d’ina I love u”.

Yace, “luv u too my baby”.

Datse wayan tayi tana murmushi jin dad’i.

Shiko Alhaji Labaran yana kashe wayar ya mik’e ya maida kayan shi bai bi ta kan budur wan ba balle yayi wanka ya tsar kake jikin shi keys d’in motor shi da wayoyin shi ya kwasa yayi waje.

I tako budurwan da ido ta bishi tare da jan tsaki ta k’ara gyara kwanciya sabida kud’i sati ya biya mata d’akin.

Shiko Alhaji Labaran yana fita inda ake ajiye motoci ya nufa ya fad’a motor sa ya mata key ya fice daga cikin hotel d’in,kai tsaye kasuwa a wuce da kanshi yaje wajen yan goro da sweet hu-hun goro biyu ya siya ya sa a motor, kai tsaye Wamako super market ya biya ya siyo sweet kwali bakwai ya zuba su a bayan motor d’aga waya yayi yafara kiran abokan sa yana shaida musu da azahar akwai d’aurin auren y’ar sa da azahar da d’an gidan maragayi justice Sulaiman D’ingyad’i a k’ofar gidan justice d’in, tuk’in yake direct gidan su Salman ya nufa a k’ofar gidan yayi parking mai gadi na zaune yafito ya k’arasa inda me gadi yake ba sallama balle gaisu yace, “me gadi yimin sallama da Hajiya Lailah”.

Me gadi banza yayi dashi saima k’ara volume d’in radio dake hannun sa yayi yana saurare.

Ran Alhaji Labaran ya b’aci yasa hannu zai wafta radiyo.

Me gadi yayi sauri wafce kayan shi.

Dai-dai lokacin Mama ta qaraso a motor ta parking tai ta fito da sauri ta k’arasa kusa dasu tana fad’in, “lafiya miyake faruwa?

Alhaji Labaran ya dube ta cikin fad’a yace wanan me gadin baida mutunci ace kamar ni ina masa magana amma yayi ban za dani sai ma ya k’ara volume d’in radiyo”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button