SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi tayi tare da fad’in, “Alhaji Labaran kayi hak’uri,ta dubi me gadi tace kai kuma me yasa kayi haka?
Megadi yace,”baimin sallama bane shiya sa”.
Ta dube Alhaji Labaran tace, “kayi hak’uri yawuce mushiga daga ciki,ta dube me gadi tace Baba me gadi bud’e get d’in”.
Bude musu get d’in yayi Dad d’in Lubabatu yafara shiga sai ita cike da mamakin miya kawo Alhaji Labaran gidan su dagani ba alkahairi ya kawo shi ba parking yayi itama tayi parking jagora tayi mai har d’akin bak’i kafi ta wuce ciki ba kowa a falon d’akin Salman ta shiga ta ganshi kwance yayi ruf da ciki ya na danna waya alamar chart yake sallama tayi ta shiga.
Salman d’agowa yayi ya kalle ta tare da aje wayar ya na tashi yana zama yace, “wa’alaikumusalam, Mama kin dawo?
Tace, “eh Salman sai yanzu wallahi kaje d’akin bak’i muna da bak’o ku gaisa”.
Yace, “bak’o kuma Mama?
Tace, “eh ta amsa da shi a ta kaice,tana me juyawa ta bar d’akin.
Bin bayan ta yayi da kallo , mik’ewa yayi shima yabi bayanta.
I tako Mama kitchen taje tace masa buwar yar aikin su ta kai ma bak’o abin motsa baki, kafin ta wuce d’akin ta aje jakar tayi da ma yafi ta shiga toilet, ruwa ta watsa ta fito.
Shiko Salman da Sallama ya shiga falon bak’in
Dad din Lubabatu bai ansa ba illa washe baki da yayi yana k’are masa kallo.
Salman ma kallon sa yake cike da mamaki don shi bai ma san shi ba bai taba ganin shi ba,wani ban gare na zuciyar shi yace kila abokin mahaifinka ne,kujera ya samu ya zauna kafin yace,”barka da zuwa”.
Dad din Lubabatu yace,lafiya k’alau,kai lallai Daughter ta iya zab’en miji nima kayi min kamar ka kamar mahaifin ka”.
Salman ko kan shi d’aure wa yayi.
Dai-dai lokacin Mama ta shigo bayan ta Aa’i me aiki ce da tiren abin motsa baki,ijewa tayi ta fita.
Mama tasa mu waje kusa da Salman ta zauna tace, “sannu da zuwa Alhaji ga kayan motsa baki ka tab’a”.
Washe baki yayi yace bashi ya kawo ni ba Hajiya Lailah a k’oshe nike nazo ne akan maganan auran y’ay’an mu”.
Mama ta kalle Salman,shima ita yake kallo dukan su kan su a d’aure.
Mama tai k’arfin hali tace, “wasu y’ay’an Alhaji?
Dariyar su kalan ta y’an duniya yayi kafin yace d’an ki da y’ata Lubabatu ta kira ni tace min ta naso in aura mata d’an ki ko kuma in ce d’an mu, shine naga amatsayina na abokin uban shi na isa in zab’a masa mata shiya sa na zo in fad’a miki don in fita hak’in ki na matsayin uwa yanzu haka ana shiga sallah azahar za’a d’aura nasiyo komi goro da sweet suna motor na ni zanba da kud’i sadaki, ya kika ce ne Lailah?
Salman ko da tunda yafara magan ya zuba masa ido kamar Tv yana masa kallon mahau kaci wanda kan sa ya zare.
Mama ko cike da mama kin rashin hankali irin na Alhaji Labaran take kafin ta dubi Salman tace,”Son dama kuna soyayya da y’ar shi ne?
Murmushi Salman yayi da yafi kuka ciwo yace,” Mama mizan yi da y’ar shi ban son ta bazan aure ta ba”.
Alhaji Labaran ko afusa ce yace,” wallahi Lailah dake da d’an ki baku isa ba sai ya aure ta bari ku gani”.
Mama ko mik’e wa tayi rai b’ace tace, “Labaran bafa ka isa ba d’ana bazai aure ta ba tunda ba ya so baka isa kamai dole ba”.
Dad d’in Lubabatu ko mike was yayi yana gwada Mama da hannu yace,” haka kika ce?
Tace, “eh haka nace”.
Yace, “tou zaki gani na isa da d’an abokina”.
Fita yayi fuuuuuuu yayi waje lokacin anfara Kiran sallah.
Mama kallon Salman tayi yana zaune kamar an dasa shi tace,my Son kar kasa da muwa a ran ka bai isa ba tunda shi ba dan gina bane balle na Baba ka”.
Murmushi yayi da yafi kuka ciwo yace, “Mama kibar ni dasu kawai bari inje inyi sallah”.
Tace, “tou ta shige ciki cike da mamakin Alhaji Labaran.
Salman ko a bayin falon yayi alwala yafita da ma-makin sa da ya fita waje yaga layin su cike da motoci harda y’an jarida rabawa yayi ya shige cikin masallacin loakacin an tada sallah, ana ko idar da sallah yaji liman na bada sanar wa akwai d’aurin auren,Salman ko bai yi yunk’urin tashi ya fita ba yana jiran yaji dawa za’a d’aura auren.
Yana zaune yaji anfara d’aurin aure yaji wani nafad’in ni Alhaji Saminu naba ma Salmanu aure d’iyata Lubabatu akan sadaki naira dubu d’ari biyar lakadan ba ajalan ba”.
Dad din Lubabatu ko shine a matsayi mahaifin Salman shine me karb’an aure.
Salman kotake yaji wani dum-dum-dum ya mik’e afusace.
Tou gashi dai an d’aura auren Salman da Lubabatu kubiyo ni dan ji ya zata kaya
Shin Salman zai ansa aure koko nidai nace ya ansa kawai don sun dace.
Mrs Basskkwace
[11/21, 7:17 PM] Sumayya: ????????????????????????????????
????????????????????
????????????
????
*SAMHA*
®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }
???? ```G•W•A```????
GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????
Story nd writing by
Khadeejatou Muhammad Basheer Basskkwace
Dedicated by GASKIA WRITING ASSOCIATED
Page 2⃣8⃣
Bissimillahi Rahmani Rahim.
Dad d’in Lubabatu ko shine a matsayi mahaifin Salman shi ya an sa auren.
Salman ko take yaji wani dum-dum-dum yayi K’arfin halin mik’e wa duk da jirin da yake gani ida nuwan sa sun rine sun yi jaaa sabida tsana nin b’acin rai ya k’ara sa in da liman ke tsaye ya an sa speaker yayi gyara murya yace,” ni Salman Sulaiman D’ingyad’i na saki Lubabatu Labaran saki uku sabida ban san Baban ta ya aura min ita auren dole amatsayin shi na abokin mahaifina to banaso akai kasuwa”.
A lokacin Dad din Lubabatu yayi waje sai washe baki ake abokanan sa sai taya shi murna suke yan jarida na d’auka kai tsaye ake nuna wa jama’a sai ji yayi Salman na magana.
Kallon-kallo aka fara yi kowa da abin da yake aiyana wa a ran sa.
Shiko Alhaji Labaran take yaji wata zufa ta keto masa wata kunya ta ziyar ce shi wacce bai taba ji ba a duniya borin kunya ya fara da mazurai yayi cikin masallacin yana nuna kan shi da yatsa yana fad’in, “Salmanu ni zaka tozar ta ka kunyata a gaban jama’a agaban yan jarida da abokai na”.
Murmushi Salman yayi ya tako ya k’ara so har inda yake tsaye yace, Alhaji Labaran waye kai me kake tak’ama dashi da zaka zo kai tsaye rana tsaka ban tab’a ganin ka ba baka tab’a gani na ba,don kawai ka zama abokin mahaifina sai kazo kamin hawan k’awara ka aura min tambad’ad’d’an y’arka wanda ko a ca-ca na ciyo ta sai nayi ca-ca na maida ta nidai Salman yanuna kan shi da yatsa yace, nafi k’arfi y’ar ka har abada, kuma aure ban yi akai kasuwa” yana gama fad’a yasa kai ya rab’a ta gefen shi ya fice.
Shiko Alhaji Labaran tsaya wa yayi kamar an dasa shi.
Mutane ko kowa kus-kus yake yi kowa na tofa albar kacin bakin shi.
Yana fita y’an jarida sukayo kanshi da tambayoyi.
Shiko bawan da ya amsa mawa ya rab’a wa yayi ta cikin mutane ya shige gida yana shiga hara bar gidan ya sauke wata iriyan ajiyar zuciya.
A’ban garan Lubabatu kuwa tana gama waya da Baban ta tafito falo ta zauna kan kujera ta dau remote ta kunna tv ta shar liberty tv sabida akwai shirin da zata kalla karfe d’aya da rabi bayan an gama labarai ganin annuno wajen wani d’aurin aure daga ganin wajen k’ofar gidan su Salman ne yasa farin ciki ya mamye ta nan take taga an hasko mata Salman a zaune acikin masallaci yayi zaman yin sallah a lokacin Alhaji Saminu ke bada auren ta Dad din ta na Kar b’a wani ihun farin ciki tayi.
Dai-dai lokacin Mom dinta ta shigo falon tana fad’in lafiyan ki kuwa Luba?