SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Vote

Share

Comments
[11/21, 2:18 PM] Sumayya: ????????????????????????
????????????????
????

????SAMHA????

By khadeeja muhammad????????????????????????????????

Bismillahi rahmani raheem

Page 3

Dogon tsaki yaja tare da aje wayar yafita wata hanya naga yabida xata sadashi da falon gidan
Dasallama yashiga yasa mu waje daga gefen umman sa ya xauna yana mata murmushi
Itama murmushi tayi masa

Umma sannu da kallo ya firta
Yauwa ta amsa masa cike da kulawa

Katashi kaje kaci abinci kasha magani kaji son

Toh umma

Yace

Daidai lokacin aka kwankwasa kofar falon kafin aka murda akashigo
Da sallama ta tashigo

Sanye take cikin dogon riga ja da farin hijjab batai wata kwallia ba amma tayi matukar kyau

Amsawa sukai baki daya

Umma tafara gaidawa
Ta amsa cike da kulawa

Kafin ta gaida SALMAN

Dagowayyi yadubeta gabanshine yayi wani mugun fadi
Yai saurin janye idonsa daga gare ta ya amsa atakaice
Lfy
Yaja bakinshi yyi shiru
Tare da lumshe idanuwa

Mikewa tai tai kitchen. Don tafara aikin daya kawota

Shiko axuciyar shi tunani yake miyasa akodayaushe inde xai ganta sai gabanai ya fadi

Tsaki yaja akasa makoshin sa tare da mikewa yai dining area

lipton kawai hada yasha yamike yadawo falo inda yatashi nan yakoma yaxauna

Umma ce tadube sa tace kayi mene wai

cike da shagwaba yadibeta yace umma banji yinwa nasha Lipton. Ne kawai

ido ta gwalo????lipton kuma me lipton xaima miyasa wai kai kwata kwata baka san cin abincine wai salman iye

Umma kiyi hakuri xanci anjima

Yaxun nikeso kaci

????kiyi hakuri umma
Anjima xanci sosai

Toh shikenan na hakura

Mikewa yai tare da fadin umma bari inje insha maganin

Toh tace
Allah yasa kar awatsa bayan gado

Murmushi yyi haba umma kamar wani yaro

Nasan haline ai kana gaba da magani

Murmushi kawai yai bece komi ba yasa kai yawuce

Itako SAMHA
Tana shiga kitchen din wanke wanke ta hada tayi kafin tai goge kitchen. Din tas sai kyalli da sheki yake

Jera komi tai inda yake
Kafin tafito falon tafara gyaran shi duk da bawani datti yai ba saida tashare ta goge ko ina ta kunna tiraren wuta ta turare ko ina a falon take yadau kamshi mai dadi

Waje tasamu taxauna ta hutawa tana jiran hajiya tafito taimata sallama ta wuce

Tagumi tarafka tana tunanin mahaifinta tana addua Allah yabashi lfy acikin ranta
Hawayene yaxubo mata dasauri tasa hijjab dinta tana gogewa

Daidai lokacin shikuma yashigo a idon shi tafara goge hawayen

Taba baki yyi aransa yana fadin utakuma wannan lfy take kuka kusa kullun saina ganta cikin halin tinani ko tana hawaye

Taba baki yyi yawuce xuwa kitchen

ku kara yawan comments in kunaso a qara yawan typing.
[11/21, 2:18 PM] Sumayya: ????????????????????????????????
????????????????
????????
????

???? SAMHA????

????????®
ZUMUNCI WRITERS ASSOCIATION
????????

Page 4

Bissimillahi rahamani raheem

Wasa tacigaba dayi da xoben hannunta babanta yasaya mata lokacin yana da lfy

ita sambataga wuce warsa ba

Haryaxo ya gitta ta da roban rua ahannun sa da cup yakoma falo ya xauna tare da kunna tv

Kusan tsawon minutes. 30 kafin hajia tafito

Aa samha har kin gamane

Eh wlh dama ke nake jira inwuce

Tunyanxu xaki wuce baki bari ai abinci kici kafin kiwuce ba

Murmushi tai wanda yaqara fito mata da tsan tsar kyawunta kumatunta ya lotsa hushiryanta ya bayana
Tare da fadin aa wlh umma nagode

Axucia ta koh cewa tai ya xaai in iya cin abinci batare da babana yaciba sam baxan iya ba inban tabbatar ya koshiba

Aa samha na lura dake bakison cin abincin gidan nan tunda kikafara xuwa yau kwana sha bakwai kenan
Ko ruwa so daya kika taba sha

Sunkuyar da kai tai kasa tana murmush

Hajiya. Tace toh tunda kyamar mu kike shikenan ki gaida mamaki

Murmushi takumayi tare dafadin xataji
Sai gobe in Allah yakaimu

Allah yakaimu hajia ta amsa mata dashi

Kama hanyar fita tayi tana murmushi

Koda tafito tafia tai mai dannisa kadan yakaita titi bata jima ba tasamu keke
Tace ma shehu macciddo road

Naira hamsin yace da ita

Dan Allah katemaka min ga arbain

dan jimmm me napep din yyi

Kafin yace kishiga

Nagode tace tare dashiga

Adaidai bakin layin yasauketa

Tamika masa kudin ta tsallaka titi
Shagon yakubu me awo ta nufa

Yanaganin ta ya hade rai
yanajan tsaki

Itako fuska dauke da murmushi ta qarasa
Sallama tamai

Ya amsa ciki ciki

Jikintane yai sanyi dataga yanayin shi tasan ko ta tambaya da wiya ya bata bashi yau tunda yana binta bashi dayawa

Gaisheshi kawai tai
Ya amsa adakile

Murmushi tai tajuya

Tsaki yakuma ja ya binta da mugun kallo

itako kara tsalaka titi tai tashiga layinsu

Tana tafiya kanta a kasa tana tina nin yau mixataba ma babanta inyafara jin yunwa
Ya xatayi dashi idonta yaciko da kwalla tafiya kawai take baa cikin natsuwar taba Tana kallon kasa

Daidai xata tsaklaka kwata sai ga kudi a kasa dubu har uku tsalakwa tai kamar vaxata daukaba

Saiwata xucia tace mata ki dauka mana robonkine Allah yaga xucia ki kina cinkin wani hali

Dawo wa tai ta duka ta dau guda daya tabar sauran awajen ta cigaba da tafia gun wata me abinci ta tsaya
Tasai shinkafa da wake da miya da kifi na two hundred akasa mata ga take away

Tawuce gida cike da farin ciki daidai xata shiga itakuma xatafito

Yauma da daniskan.shigan da tasaba shine ajikinta cingam take tauna kass kasss kasss kamar tsofaffin yan.dunia

Duk kokarin samha taga ta kauce mata amma sai data bangajeta

Ledan hannunta ya subuce Allah yasa abincin bai kife ba

Itako kota juyo tasan ta bige mutun

Samha ko murmushi tai tare da girgixa kai ta duka tadau ledar tai shigewarta

Yauma kamar kullum inna larai da yarta sunyi kaca kaca da tsakar gidan

Girgixa kai kawaitai
Tanufi dakin dayaxama na mahaifinta da ita

A kwance yake yayi dumu dumu da kashi ajikinsa

Daga labule tai tadaura kan kofa

Ta aje ledan agefe
Hijjabin da ke jikinta ta xare tadaura kan kofa

Tanade hannun rigarta

Bokatin tadauka tanufi rijia tajawo rua
Takwo dakin ta aje tadauko baho kafin ta karasa inda yake kwance
Tadagoshi batare da kyama ba.ko kyankyani

Tafara cire masa kayan ta goge masa jiki
Tai kokari ta dagashi tasashi a bahon tawanke masa jiki

Duk abin nan da take da ido kawai yakebinta yana tausayin ta ace a yanshekarunta ita ke dawai niya dashi kamar beda mata

Itako wankemai jiki take koh ajikinta

Tana gamawa ta gyara wajen tadauko shi ta aheshi kan tabarma
Kayan tadauko acikin jaka tasa masa

Kafin ta gyara masa xama ta jinginar dashi ajikin bango

Tamike tadau ruwan taje ta xubar
Tadawo ta daukayan da yabata tafita dasu

bude window tai don iska yashiga dakin

Dauko ledan abincin tai tadwo inda yake ta xauna cike da murmushi tace sannu babana

Shiko ido yaxuba mata. Yana mamakin ko damuwa bbu a fuskarta

Murmushi tai ganin kallon dayake mata tace baba kadena mamaki ace kamarni ina dawai niya dakai
In banma ba waxan mawa
Kayi dawainiya dani tun bansan waye niba
Ksmin wanka
Kamin wanki
Ka goyani babana
ka nemomin abinci kabani abaki
Kabani sitira da wajen kwana
Ka hana inwulaqanta
Kamantar dani rashin uwa
Kaine mahaifina kuma mahaifiyana kamaye gurbinta akomi dayakamata ita xatamin kai kakemin
Miyasa nima baxan rama maka ba
In ban kula dakaiba nima baxan haifi yayan da xasu kula daniba

Komi xan iya maka mahaifina dan in faranta ran……

Banko labulen da akayine
Maganan ta makale mata

Tana duban wanda ta banko kofa

Murmushi tai tare dafadin sann….

Kundun ubanki tafada cikin muryanta mekama da muryan gardimawa wata muryan gardawan ma tafita dadi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button