SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Girgiza kai yake mata alaman ba haka bane.

Taci gaba da magana a cikin kuka tace, “Salman karka manta kafin Baba na ya baka ni amana yabaka baice kaci zalina ba,amma gashi tun ba’aje ko ina ba ka fara cin amana zan koma in fad’a mai cewa wanda yaba ma amana be can-cancin abashi amana ba mugune azzalumi ne kuma ina so kasani yau d’in nan basai gobe ba zan bar muku gidan ku donni na gaji da zaman ta kura mik’ewa tayi ta sauka akan gadon hijjab d’in ta ta d’auka tasa kafin ta bud’e wardrobe ta d’au kaya ta nufi toilet don ta canja.

Shiko da ido ya bita ya kasa cewa uffan yasan duk abin da ta fad’a ba laifin ta bane nashi ne kuma gaskiya ta fad’a.

K’aran bud’e k’ofar bayin ne yasa shi saurin d’aga kai ido biyu sukai.

Tawani watsa masa harara kamar idanuwan ta zasu fad’o ta je inda takalman ta suke da zura wani plat shoe fari ta zo zata fice.

Da sauri ya dira akan gadon ya rik’o mata hijjab.

Cikin tsawa tace, “sakeni dalla malam”.

Sa hannu yayi ya d’auketa da wata gigitaciyar mari.

Wasu star-star ta gani suna wuce mata ta ido.

Saurin dafa kuncin tayi hawaye d’aya nabin d’aya.

Shiko sai huci yake kamar maciji.

A zuciye tasa hannu ta bige hannun sa daga rik’on da yayi ma hijjab d’inta ta juya zata fice.

Saurin jawota yayi,juyowar da zatai ta fad’o kan jikin shi……….!

..kuyi manage.
[11/21, 7:20 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

           ????????????????????
                 ????????????
                         ????

????SAMHA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Story nd writing by
Khadeejatou Muhammad

Dedicated by aunty baby( babykwaila)ummu hanashi,maman Adnan, Neaty lady,Hafsat musa,ummu nabeel,Jikanyar me audiga, Gwazas,Innaros etc don ban iya zayyano ku Allah ya bar kauna I love u lodi-lodi

Page 3⃣3⃣

Bissimillahi Rahmani Rahim.

Yace, “a’a Mama ina da magani zansha in kwanta da na yi bacci zande na ji”.

Dr cike da tausayi ya mik’e ya nufi inda yake yana cewa,”sannu abokina”.

Yace,”yauwa na gode”.

D’akin shi ya shiga kai tsaye kan gado yaje ya kwanta.

Mama da Dr suka shigo suna masa sannu.

Da kyar yake amsa wa sabida yanda zuciyar shi take bugu kamar zata fito fili.

Mama tace,”ina ka aje maganin?

Drawer ya gwada mata da hannu.

Da sauri ta bud’e ta ciro ledan maganin ta balle,kafin ta d’auko ruwan da tagani kan center table ta bud’e murfin ta zauna kan gadon ta tallabo shi ta bashi,sha yayi ya koma ya kwanta ya rufe ido.

Dr yace, “Mama asbiti yakamata mutafi fa naga yana jin jiki”.

Cikin muryan ciwo yace,”a’a kubar ni tukunan ciwon kai ne kawai”.

Dr yace,”Allah ya k’ara sauk’i”.

Mama tace,”Ameen”.

Fitowa sukai don su bashi ya d’an rintsa.

Samha tai saurin taran Mama tace, “Mama ya jikin nashi?

Tace, “da sauk’i ya samu bacci ciwon kaine”.

Tace,”Allah ya k’ara sauk’i”.

Tace “Ameen,kitashi kibi Dr ya kaiki karki kai magariba banson dare awaje”.

Tamik’e cike da kunya jin Mama tace” “ta bishi tace,Mama da Yaya ya kama ta muje ya tafi kawai in Yaya yaji sauki yakai ni”.

Mama tace, “tou shikenan ki hutar da shi ai”.

Dr ko da beso haka ba yaso suke be tare yai ta ganin ta hakanan, jiki ba k’wari ya dubi Mama yace, “Mama bari in tafi zuwa anjima zandawo in ga jikin nashi,Allah ya bashi lafiya”.

Tace, “Ameen, Allah yakai mu ka gaida Hajiya ka”.

Yace,”zataji insahaallahu”.

Yadube Samha dake tsaye kai a katsa yace, “madam Samha ba rakiya?

D’agowa tana murmushi tace, “eh sai anjima kawai zance ma”.

Yace, “tou shikenan Allah yakaimu”.

Mama tace, “ke Samha baza’ai haka ba sabida ke yazo sannan ki k’i raka shi aiko sai kin raka shi”.

Sunkuyar da kai tayi tare da cewa,”tou Mama”.

Fita yayi ta bi bayan sa har wajen motor sa ya jingina da jikin motor ya zuba hannaye sa a aljihun sa ya zuba mata idanuwan shi sai murmushi yake.

Itako duk’ar da kai tai k’asa don ba k’ara min kwarjini yake mata ba.

Acikin wata irin murya yace,Samha kina sona?, nayi miki?,zaki aure ni?

Sa hannuwan ta tayi ta rufe idon ta sabida kunya .

Ya k’ara wani maraice murya yace, ”d’an Allah baby karkice bak’ya sona, bazan iya ba in babu ke wallahi”.

Shiru tayi taka sa cewa uffan sabida wani kunya sa take ji.

Ya k’ara kashe murya yace, “Baby dan Allah ki min magana kinji, ko sai nayi miki kuka ne zaki amince Dani?

Saurin d’ago kai tai karaffff idanuwan shi akan nata kallon-kallo sukai ma juna na y’an dak’ik’a,itace tai saurin kau da kai yace,”kinji please”.

Tace, “Yaya nifa ban san me zan ce maka ba”.

Murmushi Dr yayi kafin yace,”Baby kice nima ina sonka ,kayi min, zan aure ka”.

Gwalalo ido tayi tana kallon shi kafin ta ta’ba baki tace,”ni de bazan ce ba wallahi,ni katafi zan shiga ciki”.

Murmushi yayi da iyakan sa fuska yace,”tou shikenan na gode, mi zan kawo miki in zan dawo?

Ta’ba baki tayi tace, “banson komi naka”,bata jira abin da zai ce ba ta juya tai ko mawa ta ciki.

Da ido yabita son ta karuwa yake a cikin zuciyar shi komi nata burge shi yake.


B’an garan Baba kuwa sauki ya fara samuwa don Gwaggo Dije tana kula dashi sosai kamar sun shekara talatin da aure,yau kwana biyu kenan da Salman ya turo driver ya d’auke shi ya kai shi 44hospital wajen Dr da Dr Abbas ya had’a su dashi ya duba shi kuma ya tabbatar zai Mik’e in aka maj gashi,anyi masa gashi kuma an samu nasara yanzun haka in ka tsungule shi a hannun yana jin zafi,sab’anin da da be jin komi koda yanka wajen zaai bazai jiba yanzu ko Alhamdulillah yana ji kuma yanayi kamar zai motsa.

B’an garan Inna Larai ko da y’arta k’afa taki saida ta komar da ita aka k’ara kar ya k’afar aka d’aura sabuwa,duk tabi ta rame tayi bak’i gashi kud’i su duk ya k’are dan ma kawayen ta na zuwa duba ta suna kawo mata abubuwa,samari ko babu me kiranta duk wanda ya kira yaji ta karye ba ya k’ara kira.

B’an garan Lubabatu ko yanda take jiya iyau ko motsi batayi tana kwance kamar gawa, hankalin Dad d’in ta ba k’ara min tashi yayi ba haka Mom dinta,suna zaune duk sunyi jigum-jigum a hankali tafara motsa k’afar ta Mom ce ta ankara da hakadm jiki na rawa ta mik’e tace, “Alhaji wallahi tafara motsi kalla kafar ta”.

Duban shi yakai gare ta yaga k’afar na motsawa da gudu yafita yana k’wala ma Likita Kira karo suka ci da Dr Habeeb.

Saurin matsawa Dr Habeeb yai yana tambaye shi lafiya?

Kasa magana yayi illa nuna masa d’akin da Lubabatu ke kwance yayi.

D’akin ya nufa yaga Mom akanta ta rungumota.

Yace, “Hajiya lafiya me yafaru?

Mik’ewa tai tace, “Dr kalla k’afan ta yana motsi wallahi”.

Duban sa yakai ga k’afar yaga tana motsa su murmushi ya sake tare da d’aga hannu sama yana Mik’a godiya ga Allah yana fad’in, ” Alhamdulillah Allah mun gode ma”.

Duban su yayi yace,” kijira ni awaje.”.

Badon sun so ba suka fita musamman Dad d’inta.

Dr Habeeb yafara dud-duba ta,aikam cikin ikon Allah tafara bud’e idon ta ahankali harta gama bud’e wa nunfashin ta na fita da k’arfi ,akan Dr Habeeb idon ta ya sauka kallon rashin sani take mai juyawa tazo yi wiyan ta ya k’age ta kasa saman silin d’in ta k’ura ma ido kamar me nazarin wani abu take abin da ya faru yafara dawo mata tiryan tiryan kamar yanzu abin ke faruwa saurin rintsa idon ta tayi tana jiyo muryan Salman sanda yake cewa (ni Salman Sulaiman D’ingyad’i na saki Lubabatu Labaran saki uku)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button