SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dr daya ga haka allura ya ja ya mata ahankali numfashin ta yafara dai daita.

Duban shi ta k’ara yi cikin da shashiyar murya tace,” Likita ina Dad?

Yace,”suna waje da mahaifiyar ki”.

Shiru tayi na d’an lokuta kafinta tace, “Likita dan Allah kamin allauran mutuwa”.

Gwalalo ido yayi waje ya han game baki ya wani daskare awa jen take jijiyoyin jinin jikin shi suka tsaya cak.

Tace, “don Allah Dr kamin zan mallaka maka komi dake gareni in har kamin haka”.

Duban ta yake duba me cike da mamaki kafin yace,”baiwar Allah me yayi zafi haka da zakija min azumi sittin,anya kina da imani?

Murmushi tai da yafi kuka ciwo tace, “Dr na roke ka don Allah kami”.

Jimmmm yayi kafin yace, “zan miki amma ba yanzu ba”.

Tace, “sai yaushe?

Yace, “in lokacin ki yayi”.

Tace, “Dr yanzu ma lokacina yayi ai”.

Ya girgiza kai tare da cewa aa sai nan gaba” k’ara jan allura yayi ya mata ko second biyar baayiba ta fara lumshe ido alaman bacci, murmushi yayi ya fita daga d’akin.

Da sauri Dad ya tarbe shi yace, “Likita ta tashi?

Fuska dauke da murmushi yace,” eh Alhaji har munyi magana,amma namata allura ta koma bacci don naga kamar ba acikin hayyacin ta take ba”.

Cike da farin ciki Dad yace, “dagaske kake Likita ko kwantar mana da hankali kake?

Yace,”ai bazan maka wasa ba Alhaji kutayi mata addu’a inshallah zata sami lafiya” yana kai wa nan yai gaba abin sa.

D’akin suka shige isketa sukai sai bacci take.


Samha ko tana shiga ciki d’akin ta tai direct cike da tunanin Dr da ma-makin ta taga mutum kwance kan gadon ta waro ido tayi cike da mamaki a zuciyar ta tace,ba ance yana bacci ba tou miya fito dashi ya kwanta min a gado,tsinkayar muryan shi tayi.

Yace,”keeeeeeekina wasa dani ko sabida baki da kunya a gabana kike ce ma wani gardi Baby?

Murgud’a mai baki tayi tare da turo baki.

Yaci gaba da fad’in to wallahi koda wasa naji kina soyayya wallahi sai na karya ki mara kunyar k’arya kawai”.

Ta’ba baki tayi tace,”ka kakkarya d’in mana in ban yi soyayya da shiba da kai zanyi koko kai zan aura,ba izinin ka nike jira ba tun da Mama ta amince na amince da shi ina son shi kuma sai na au…….

Bata kai ga k’arasawa ba taji an fin cikota ta fad’o kan mutu had’e baking sau yayi da nata ya na wani irin tsotsa cike da mugunta.

Itako mutsu-mutsu take tana so ta k’wace kanta amma ta kasa don yamata mugun rik’o ga azaba ya dame ta.

Shiko mahaukaci kissing yake mata cike da mugunta.

Hawayen dole take sabida tsananin azabar da lips d’in ta suke mata,mamayan shi tayi ta gantsara masa cizo a halshe……..

Washeeeee

Asheeeee
Hannuna ????????????????????????????
[11/21, 7:20 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

           ????????????????????
                 ????????????
                         ????

????SAMHA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Story nd writing by
Khadeejatou Muhammad

Dedicated by ummaima Aliu,Jikanyar Hajia,Kamshi,sakina,Hajia Zainab,Zee, first born,da sauran ku kuna da yawa midwife comment d’inku ina jin dad’i shi Allah yabar kauna

Page 3⃣2⃣

Bissimillahi Rahmani Rahim.

Saurin jawota yayi juyowar da zatai ta fad’o kan jikin shi,wani yarrrrr yaji ajikin sa.

Ita ko sai k’ok’arin k’watan kanta take amma ta gagara don ya rik’e ta gam a jikin shi.

Du bara ya fad’o mata sa bakin ta tayi ta gan tsara masa ciwo.

Azaba yaji har k’wak’wal warsa saurin sake ta yayi.

Tabud’e k’ofa ta fice da gudu.

Tazo zata bud’e k’ofar falo ta fice taji tayi karo da mutumz,saurin d’agowa tai don kanta ya bugu karaffff suka had’a ido dashi.

Murmushi yasake mata wanda ya k’ara ma fuskar sa k’yawu.

Itama bata san-sanda murmushi ya k’wace mata ba.

Jiyayi gaba d’aya da muwar da yake da mun sa ya wuce bashi.

Ko mawa baya tayi alaman ya wuce.

Shiko kafe ta da ido yayi kamar zai cinye ta ya tako a hankali har inda take tsaye be ce komi ba illa kallon ta da yake bai ko kauda ido.

Ita ko ganin irin kallon da yake mata yasa taji zuciyar ta na dum-dum-dum.

A hankali yace,”Baby Samha ba gaisuwa ne?

A kunya ce tace, “an wuni lafiya Dr” cikin wata siririyar muryan da ko ita kanta bata san tana dashi ba.

Murmushi yasake idon shi akanta yace, “lafiya k’alau my Baby”.

Wani dogon tsaki da suka ji an sake yasa su duk saurin kallon inda tsakin yafito.

Salman ne tsaye ya nad’e hannaye kan k’irjin sa ya had’e giran sama da na k’asa.

Murmushi Dr Abbas yayi yace,”kai d’an iska ashe kana nan ma?

Yace,”ina zaka sani tunda kasa yarinya k’ara a gaba kana wani kashe mata murya” mtsuuu tsaki ya Kuma jaa.

Murmushi yak’ara saki yace, “tou ina ruwan ka ba sabida kai nazo gidanan ba sabida ita nazo”, ya juya yana kallon ta yace,”ko Baby na?

Itama d’aga idon shi tayi cikin nashi tace, “eh Baby na”.

Take zuciyar Salman ta buga dum-dum-dum tare da jin want jiri zai kwashe shi,saurin zama yayi tare da lumshe idanuwan shi yana sauke ajiyar zuciya.

Samha ko ganin yana yin shi ya sauya yace tai wanin murmushi sabida komin banza ta ‘bata masa tace, “Baby Bissimillah ga waje zauna in kawo ma ruwa da abinci”.

Yace tou Baby kujera ya samu ya zauna ya hard’e k’afa d’aya kan d’aya.

Ita kuma ta nufi kitchen minti kad’an sai gata da jug da cup ta aje a gaban shi ta tsiyaya masa sai da ta d’an duk’a kafin ta bashi.

Idon shi na kanta yasa hannu ya ya ansa yana me sake mata murmushi.

Ita ma ta mayar masa tace,”bari in kira ma ka Mama ku gaisa”.

Yace,”tou Baby na”.

Juyawa tayi ta nufi d’akin Mama.

Shiko da ido ya bita.

Salman ko bak’in cikin duniya yau yaji shi a ciki a zuciya shi yace,lallai yarinya nan a gabana take ce ma wani Baby lallai yasan maganin ta.

Mama ce ta shigo bayan ta Samha ce fuskar ta d’au ke da murmushi tace,”lale-lale ga Likita bokan turai a gidan mu”.

Murmushi yasake tare da zamo wa kan kujera yace, “Mama ina wuni”.

Tana zama tace,lafiya k’alau bokan turai” , yasu hajiyar ka?

Yace, “lafiya k’alau Mama”.

Tace, “yau ka tina da abokin ka ne kenan?

Yace, “a’a Mama nazo gaishe kine da neman iri”.

Tace,ina godiya Likita sosai wallahi aika yi zumunci”.

Yace, “Ameen Mama”.

Sunkuyar da kai yayi yace, “Mama”.

Tace, ” Na’am Likita”.

Ya k’ara sunkuyar da kai k’asa yace,”Mama d’an Allah nazo neman izini ne wajen ki zan rink’a zuwa wajen Samha ina son ta da aure”.

Mama ko take taji wani farin ciki ya lu-llub’e ta ta fad’ad’a fara’a ta tace,amma de Likita naji dad’i kuma nayi farin ciki,Allah ya tabbatar da Alkhairi wallahi na baka izini Allah yasa ayi muna a raye”.

Yace,”Ameen Mama na gode sosai”.

Tace ba godiya tsakanin mu kai da ita da Salman duk d’aya kuke awaje na, Allah ya muku albarka”.

Yace,”Ameen Mama”.

Salman ko jiyayi kamar an zuba mishi garwa shi a cikin zuciya,ji yake kamar ya tashi ya fita amma kar Mama taga kamar akwai wani Abu zuciyar shi.

Mama duban shi tayi tace, “my Son lafiyan ka kuwa?, wai miya hanaku tafiya ne?

Ahankali yace, muryan sa harwani sark’ewa yake yace “Mama zamu tafine Abbas yazo”.

Tace,”owk yayi”.

Ita ko Samha cike da mamaki take kallon shi ashe ya iya k’arya.

Mik’ewa Salman yayi ya nufi hanyar d’akin shi.

Mama tace, “a’a kazo ka kaita mana”.

Bai juyo ba yace, “Mama wallahi bazan iya tuk’i ba Abbas yakai ta kaina ciwo yake min”.

Da sauri ta mik’e tana fad’in,” ashhha sannu Salman”,ta k’ara sa inda yake tsaye ta rik’o hannun shi taji hatta hannun shi yayi zafi tace, “ko Likita ya duba kane?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button