SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mama ko tana barin gidan su Samha kai tsaye gidan k’anin Baban Salman ta nufa nan take sheda masa Salman ya samu mata,ba k’ara min farin ciki yayi ba bata baro gidan ba saida suka tsaida ranan da zaije neman aure.

Dr ko tun ran da yabar gidan su Salman bai k’ara lafiya ba sabida damuwar da yashiga ba kad’an ba in kagan shi sai ka tau saya masa,wani abokin shi ya sashi gaba yana tambaya shi miyake faruwa da k’yar ya fad’a masa.

Kallon shi yayi yace, “banza nekai ni akwai macen da ta isa ince ina sonta tace bata sona,tini zankai ta gidan Malan Nura ya samin ita a allon k’arfe dole tabi ni duk inda nike wallahi”.

Dr sakin baki yayi yana kallon shi kafin yace,” kace wallahi zai shawo min kanta”.

Yace k’warai kuwa binka zata rink’a yi kamar bindi………!

Touuuuuuu fa fans kuji shawaran da abokin Dr yake bashi kubiyo ni don jin yazata kaya…..
[11/23, 8:04 PM] Sumayya: ????????????????????????????????????
????????????????????
????????
????

????SAMHAA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍????
{ Gaskiya d’aya ce daga k’inta sai b’ata burinmu mu fad’akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}

    ```????G•W•A????```

GASKIYA DOKIN K’ARFE•????????

Written by khadeejatou Muhammad Basskkwace

Dedicated by FAD’EEMATOU MUSTAPHA(aunty Baby)MRS ZAKS,MRS ALIYU (MARUBUCIYAR IZZAR MULKI),MOM HANASH,SUMMY,NEAT LADY,ME GWAZA,INNARO,JIKANYAR ME AUDIGA,KHADEEJATOU S DOGARAI(LIPTON GIRL☕)DA SAURAN KU DAYAWA-DAYAWA

Page4⃣0⃣

Bissimillah rahamani Raheem

Baba zama yayi gefen Salman fuska d’auke da murmushi.

Shima Salman d’in murmushi yake,tare da cewa, “ina wuni Baba?

Baba ya dube shi yace,”lafiya k’alau Salmanu,yasu Mama ka da k’anwan taka?

Yace, “suna nan lafiya Baba ita tama aiko ni wajen ka”.

Baba yace,Allah sarki ,”Allah yasa alkhairi ne”.

Yace,”Ameen,Baba ya k’arfi jikin ka?

Baba yace,” Alhamdulillah,Allah yayi maku albarka”.

Yace,”Ameen thumma Ameen Baba”.

Shiru sukai na minutes kafin Baba ya k’ara duban Salman yace,”ya akayi Salmanu kace an aiko ka kuma kayi shiru?

Sosai k’yayar shi yake,kamar wanda yayi k’arya yace,”Dama tace gobe su kawu zasu zo wajen ka”.

Baba fara’a shi ta k’ara fad’a-d’a yace,”Allah sarki Allah ya kaimu Salmanu”.

Gwaggo Dije ma cike da fara’a tace,”Allah ya nuna mana”.

Sunkuyar da kai yayi cike da kunya,kasa cewa yayi Ameen.

Inna Larai ko zuba ma y’ar ido tayi kamar sabuwar mayya ta ke cin abinci, kafi ta kyafta ido ba komi a kula Zainab ta cinye.

Baba ko fira suka sha da Salman har yamma kafin ya musu Sallama ya wuce.

Lubabatu ko ita da Dr Habeeb soyayya kawai suke sha kamar baza’a mutu ba.

Samha zaune take kan kujera,Mama ko tana k’asa zaune tsifa take ma Mama sunayi suna hira hankali kwance kamar y’a da uwa na gaskiya, bud’e k’ofar da akayi ne yasa su saurin d’aga kai.

Salman ne ya shigo falon fuskan shi ba yabo ba falsa yayi sallama yana me samun waje yana zama,amsawa sukai,ya gaida Mama ta amsa cike da fara’a,kafin Samha ta gaida shi.

Sai da ya fake idon Mama ya galla mata hara-ra kafin yace,”lafiya” atak’aice.

Ta’ba baki tayi taci gaba da tsifar da take.

Hira suke da Mama cikin wasa da dariya,in kin gansu baza kice uwa da d’a bane.

Bangaran Dr Abbas ko sun shirya tiryan-tiryan su tafi gidan Malan Nura,duk da akwai layi amma saida suka jira har layi yazo kansu,suna shiga, Malan Nura ya dube su yace,”me ke tafe daku?

Rabi’u abokin Dr ya fara koro ma Malan Nura bayani.

Nan Nura yafara watsa wuri yana wasu surkul-le tsawan lokaci kafin ya dube su d’aya bayan d’aya yace,”buk’a tar ku ba zata biya ba gaskiya sabida wanan yaron da da tace zata aura akwai rabo me tsanani a tsakanin su”.

Take zuciyar Dr tawa ni buga dummm.

Rabi’u ko cewa yayi,” Malan Nura ba’a bin da za’a yine?

Malan Nura ya k’ara surkul-le sa yace,”akwai in da kud’i”.

Dr yayi saurin cewa,” Malan ko nawa ne zan bada in har zan mallake Samha”.

Malan Nura yace, “nafarko d’an du k’ununa yana buk’atar makahon sauro,kuturun k’uda,rak’uma guda biyu mace da na miji, sai tantabara aure, bak’in sabulu,jar tukunya,gayan kan ‘barawo,kitsen bak’in maciji sai allon k’arfe”

Tunda yafara bayani kallon-kallo sukai da Dr da Rabi’u har saida ya gama zay-yano wa.

Rabi’u ne yace,”tou Malan nawa za’a kashe don mu ba musan inda zamu samo wa’yan nan kaya ba”.

Malan Nura ya d’an mus kuta yace,”million biyu da dubu d’ari takwas”.

Jikin Dr na rawa yace,to Malan an gama bani A/N ka in ma transfer…….!

Comment d’in ku shine k’arfin guywa ta inna ga comment zakuji ni anjima.
[11/23, 8:04 PM] Sumayya: ????????????????????????????????????
????????????????????
????????
????

????SAMHAA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍????
{ Gaskiya d’aya ce daga k’inta sai b’ata burinmu mu fad’akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}

    ```????G•W•A????```

GASKIYA DOKIN K’ARFE•????????

Written by khadeejatou Muhammad Basskkwace

4⃣2⃣

Dedicated by MY ONE ND ONLY ALHAJI IBRAHIM MUHAMMAD,ALLAH YA K’ARA MA LAFIYA DA NISAN KWANA.)

Bissimillah rahamani raheem

Da sauri ta d’ago ta dubi Mama fuska d’auke da ma-maki,wai bikin ta saura kwana biyar kamar anwani gaji da ita,kuma da wannan mugun Salman me fuska biyun,k’ak’alo murmushi tai da iya kan sa fuska tare da cewa,”tou Mama bari in shirya”.

Mama tace,”yauwa Daughter yi sauri,in kin gama shiryawa ina d’aki”.

Tace,”tou”.

Mama fice wa tayi ita kuma ta mik’e ta fara shiri,cikin mintina kad’an ta gama shirin ta, fitowa tayi ta nufi d’akin Mama a zaune ta ganta ka kujera tana waya,gefen gado ta zauna ta na jiran ta gama.

Tsawan lokaci kafin ta sauke wayar duk maganan akan aure sune ,itako har mamaki take yanda Mama ke zumud’in bikin nan.

Mama ta dube ta tace,”harkin fito?

Tace,”eh Mama nafito”

Tace,”to nayi ma driver magana zai kai ki gidan ku zai jira ki kiga ma abin da kike da ganan zaikaiki gidan Hajja Ganah”.

Tace “tou Mama”.

Mik’ewa Mama tayi ta ciro wata waya a caji ta Mik’a mata tace,gashi nan akwai sim card aciki da number na da na Gwaggo Dija da na Salman,akwai kud’i aciki,zamu rink’a waya”.

Tace,”tou Mama na gode Allah yasaka da alkhairi”.

Mama tace,”Amin amma banson godiya nan”.

Murmushi kawai tayi ta mik’e zata fita,tare da cewa,”na wuce Mama”.

Tace, “tou a kwai leda kan 3siter ki dauka ki kai ma Gwaggo Dije, ki gaishe min dasu”.

Tace za suji, da tafito d’aukan ledan tayi ta fito a bakin get ta hango driver ta nufi wajen, ko kafin ta k’arasa ya taso sabida hango ta da yayi.

Dan duk’a wa yayi yace,”barka da fito wa Hajiya”.

Tace,”yauwa”.

Da sauri ya zo ya bud’e ma ta gidan baya,tashiga ta zauna,shima wajen zaman driver yaje ya zauna ya tada motor,me gadi ya bud’e musu get ya fice.

Tuk’i yake ahankali har suka isa unguwar su adai-dai k’ofar gidan su yayi packing,kan tayi yun k’urin ta bud’e k’ofa ta fita ,yayi saurin fita ya bud’e mata k’ofa.

Zuro k’afa fuwan ta tayi waje tayi kafin ta jawo ledan da Mama ta bata ta kawo ma Gwaggo Dije,da sauriya sa hannu ya ansa ledan.

Gaba tayi yana bin ta abaya,da sallama ta shiga cikin gidan.

Inna Larai dake k’ok’arin fura wuta ta d’ago zata amsa,ganin wacce ta shigo yasa ta sandare wa.

Itako murmushi ta sake tare da k’ara sowa in da take tace,”sannu Inna da aiki”.

Kasa ansawa tayi illa kallo da take binta dashi.

Samha tace,”tashi in hura miki wutan”.

Inna Larai cike da mamaki tace, “Samha kece?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button