SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Samha ta murmushi tace,”nice Inna,bari in hura miki wuta”.

Da kallo ta bita,ita ko Samha k’ok’arin hura mata wutan take……..!

GASKIYA COMMENT DINKU YA MIN KASA ZAN DAKATA DA TYPING DAGA YAU????????
[11/23, 8:04 PM] Sumayya: ???????????????????????? ????????????????????????????????????
????????????????????
????????
????

???? SAMHA????

WRITTEN BY
Khadeejatou Muhammad Basskkwace.

4⃣3⃣

Dedicated by
HAJJAJU ,WANNAN PAGE DIN NAKINE KE KADAI DON JIN DADIN KI LUV U LODI-LODI

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM

Hura mata wutan tayi saida taga ya kama kafin ta mik’e ta dube Inna dake tsaye soro-ro cike da na daman abin da tayi mata abaya.

Tace, “Inna mi za’a d’aura?

Inna ta washe haure tace, “bashi zan d’aura dankali ne zan ta fasa mana”.

Samha tace,kawo in d’aura Miki,bata jira mi zata ce ba ta nufi d’akin ta don d’auko wa,tana d’aga labule taji wani abu ya bige ta da sauri ta dawo baya tana toshe saurin to she hanci tace,”Inna ‘bera ya mutu miki a d’aki ko baki ji bane?

Inna tafara matsan k’walla tare da cewa, “ba b’era bane k’afar Yayan kine ya la-lace”.

Gwalalo ido tayi tare da wangale baki kanta taji ya d’aure mata ta k’yar ta iya cewa,” bade Yaya Zainab ba?

Inna tace,”ita kuwa Samha” nan ta kwashe labarin abin da ya faru ta zay-yano mata.

Samha ko shar’ban kuka take cike da tausayin y’ar uwan ta.

Driver ko ya zuba musu ido yana rik’e da leda ahannu.

Inna ce ta kula dashi tace,”ba tare kuke da wanna ba?

Samha duban shi tayi da idanuwan ta dasuka kumbura suntum tace,” kawo ledan kaje ka jirani a motor”.

K’ara sowa yayi ya aje mata ya fice.

D’aukan ledan tayi tace ma Inna tana zuwa, d’akin su ta nufa saida ta k’wank’wasa k’ofar, Gwaggo Dije tazo ta bud’e mata ganin itace yasa ta fad’a-d’a fara’an ta hanya taba ta tawu ce ciki.

Saida ta zauna kan kujera kafin ta gaida Baba da yake kwance kan 3 sitter.

Cike da fara’a ya amsa dajin dad’in ganin yanda ta koma ta murje tayi kyau tayi fresh abin ta.

Mik’ewa yayi ya zauna yace, “yana ga idon sun yi ja kuma sun kumbura?.

Gwalalo ido Samha tayi tare da sakin baki tana kallon shi cike da mamaki tace, “Baba na kaji sauk’i ashe har kana motsa jikin ka amma ban sani ba”.

Cikin sakin fusaka yace, “Y’ata jiki Alhamdulillah had’uwar mu da wanan yaro Salmanu alkhairi ne,yate make ni sosai-sosai bansan da me zan saka masa ba”.

Tace, “Allah sarki Allah ya saka masa da mafi-ficin Alkhairi”.

Yace,”Ameen”.

Gwaggo ce tafito kitchen d’auke da k’aton faranti ta dire mata a gaba tana fad’i, “lale-lale idon ki kenan Samha”.

Murmushi tayi tace, “wallahi ko Gwaggo ina taso inzo Allah bai ban iko ba sai yau”.

Gwaggo tace,”haka lamrin ubangiji yake komi sai ya baka iko,ya kika baro Hajiya kusan kullum sai munyi waya”.

Tace, “lafiya k’alau take,ga sak’o tace in baki tayi maganan tana me mik’a mata ledan”.

Ansa tai tana du bawa.

Itako Samha duban Baba tayi ta ta’ba fuska kamar zatai kuka tace,”haba Baba shine ko awaya baza’a fad’a min ba kullum da tinanin ka nike kwana nike tashi, addu’a ko ba fashi”.

Washe haure yayi yace,”yi hak’uri y’ar Baba yayanki ne yace kar afad’a miki ya fiso kiga bazata”.

Tab’e baki tayi jin yafad’a Salman ne ya hana afad’a mata tace,”aikam gashi naga ba zata ko”.

Gwaggo tace,”baki sha ruwa ba ,ga Kuma abinci”.

Murmushi gefen baki tayi tace,”bazan sha ba kema ina fushi dake da kuka b’oye min”.

Dariya daga Gwaggo har Baba suka sa,ita ko ganin abin da sukai mata yasa ta tashi fuuuuuuu wai tayi fishi wai zata wuce.

Baba yayi saurin ja wota ta fad’o jikin shi, y’ar k’ara ya saki tare da cewa,”zata b’alla min k’afa”.

Gyara zama tayi a kan k’afar na shi tace,”anan ma zan zauna”.

Gwaggo Dije tace, “d’aga min k’afar miji karki karya min shi ki bar ni da jinya”.

Murmushi tayi tace, “Gwaggo ashe kin karya Yaya Zainab kuma ba’a dace d’aurin ha k’afar ta la-lace sai wari yake”.

Gwaggo tace, “wallahi kuwa abu beyi dad’i ba nima dana gani banji dad’i ba ,in Allah yakai mu gobe zan kaita asbiti aga yanda za’ai da k’afar”.

Samha cikin tausaya wa tace,”Allah sarki wallahi taban tausayi sosai,ki duba yanda Inna ta dawo kamar ba ita ba,don Allah Gwaggo ko-kod’ad’d’un kayan kine ki tema ka mata dasu,gashi fa dan kali zasu ci da dare nan gashi duk sankara ya kama shi”.

Baba da sai yanzu yasa baki a maganan su yace,”maganin Larai kenan yanzu ta fara ganin ishara,kuma kema Dije ban amince kikai ta asbiti ba inta mutu ban da asara”.

Samha dake kan k’afar Baban ta tayi rashe-rashe ta sauka da sauri ta sunkuce farantin da Gwaggo ta kawo mata abinci tai waje dashi,da ido suka bita sun san tabbas Larai zata kai mawa.

Gwaggo ta dubi Baban Samha tace,”haba Malan dan Allah kayi hak’uri kamaida komi ba komi ba komai ye zafi maganin shi Allahi,balle Ahalin yanzu komi ya wuce sai labari”.

Ya nisa idon shi akan ta yace,”to shikenan Allah ya baki ikon temakon su Allah yabaki lada Khadeeja ayanzu nasan nayi dacen mata”.

Tace,”ameen”fuskan ta dauke da murmushi.

Samha ko koda tafito a tsakar gida taga Inna Larai tana ta fama da haya k’i tace,” Inna kashe wutan ga abinci kizo ku juye”.

D’agowa Inna tayi ta dubeta d’auke da k’aton faranti ta taho jiki na rawa ta ansa washe haure tayi tace,na gode Samha Allah ya miki Albarka Allah ya jik’an Maman ki”.

Da sauri ta amsa , sabida taji dad’i addu’a da Inna tai ma mahaifiyar ta kuma yaune karo na farko da taji Inna tayi ma mahaifiyar ta addu’a.

Inna d’aki tashiga ta d’auko langa da kwanon sha ta juye abincin kafin ta juye sanyayyar zob’on dake jug d’in se addu’a take kwararo ma mahaifiyar Samha.

Samha ko d’aukan faranti tayi ta koma d’akin su.

Sallama tayi tashiga bata jira an ansa ba tace, “Gwaggo don Allah ki rik’a basu abinci in kinyi”.

Gwaggo tace,”tou ko zaki dawo nan ne ki rink’a da fawa kina Basu”.

Murmushi tayi tace,”eh mana Gwaggo nifa rabuwa da ku dole ne”.

Gwaggo tace,”gashi Kuma zakiyi aure ki d’auke su ku tafi tare,kinga sai kifi kula dasu ko”.

Ya mutsa fuska tayi ba tace,komi ba saide hummm da tayi tasa mu kujera ta zauna ta lumshe idanuwan ta.

Gwaggo dariya tasa tare da cewa,” wai it’s kunya ai na gano ki, k’ila ma ke kika matsa ma Yaya Lailah kina son auren”.

Mik’ewa tayi tace, “Baba zanje gidan Hajja Ganah gyaran jiki”.

Yace,”tou adawo lafiya ki gaishe su”.

Tace,”zasuji”.

Bata kalle Gwaggo ba ta fice,wai ita tayi fushi.

Dariya Gwaggo take mata,tare da cewa aje adawo za’a iskeni ai”.

Ficewa tayi daga k’ofar d’akin Inna ta tsaya ta sa hannu a jakan ta tace,” Inna lek’o gashi wuce wa zanyi”.

Gwaggo da sauri ta lek’o kasan cewar zainab tana bacci tace,”gani har zaki tafi?

Tace,”eh wallahi zani wani wajene”.

Mik’a mata kud’i dake hannun ta tayi tace,”gashi kusai omo kuyi wanki kisai tiraren wuta Kirin k’a sawa a d’aki”.

Inna ta ansa tana godiya da y’ar k’walla ta.

Samha ko ficewa tayi, driver na ganin ta dasauri ya taso ya bud’e mata k’ofa ta shiga ta zauna kafin ta rufe ya zagaya mazaunin shi ya tada motor suka bar unguwar.

Legislative suka nufa wani gida suka dosa had’uwar shi yakai had’u wa hon yayi me gadi ya wangale masu get ya shiga a haraban gidan yayi parking in da yaga anayi parking motoci fita yayi ya bud’e mata ta fito.

Ciro wayar ta tayi a aljihu ta dubo number Mama ta kira ta tace mata tazo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button