SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ganin wayar Mama kan kujera yasa shi saurin mik’a hannu ya d’auka contact ya duba aiko yana cikin diba wa yaga My Daughter da sauri ya copy number ya sa ga wayan shi ,ya maida mata wayar inda yake yakoma nesa da kujeran ya zauna, mik’ewa yayi ya nufi d’akin shi yana shiga ya fad’a kan gado saving number yayi ya rubuta (MY NISFU HAYAT) ajiyar zuciya ya sauke.

Danna kira yayi ringing wayan yake har ya katse ba’a d’aga ba.

Itako lokacin Hajja Ganah tana koya mata yanda zatai magana da mijinta da yanda zatai tafiya,Hajja Ganah ce tace,mata karta d’aga sai ya kuma kira.

Shiko tsaki yaja ganin bata d’aga ba da har yayi kaman bazai kuma kira ba amma ya kasa saida ya kuma kira,nan ma ba d’aga ba har ya soma cire rai da za’a d’auka sai da ta kusan ka tsewa kafin ta d’aga.

Ji an d’aga yasa shi sauke ajiyar zuciya.

Itako da ga can b’an garan kashe murya tayi tare da lank’wasa murya tace, “Assalamualaikum warahamatullahi wa barakatuhum”.

Shiko jin saukan dad-d’an muryan ta saida yawani lumshe ido tare da jin wani na tsuwa ta ziyar ce shi,a sanyaye ya amsa mata da,” wa’alaikumusalam”.

Ta kuma kashe murya tace,”ango na kasha k’amshi ya kake”.

Yace,”lafiya k’alau nike” kina ina ne?

Saida ta kalle Hajja Ganah taga mi zatace,alama tai mata da hannu tafad’a masa inda take.

Aiko nan ta fad’a masa inda take.

Yace,”mata tou yana zuwa anjima da dare”.

Tace,”tou my Nurul K’albi”.

Sallama sukai ta kashe wayar.

Ajiyan zuciya ya sauke sai kallon wayar yake yana murmushi.

Itako tana sauke wayar ta ta’ba baki ta aje gefe.

Ta dube Hajja Ganah tace, “Mami wai yana zuwa anjima”.

Hajja Ganah tace,”tou sai ki shirya shiga kitchen” .

“Tou” tace mata.

Aiko anayi Sallah magrib ya wuce gidan Hajja Ganah yana zuwa me gadi ya bud’e masa get ya shiga yayi parking ya fito direct cikin gidan ya wuce,sabida yasa ba zuwa Mama na aiko shi falon ya shiga kai tsaye ba kowa a falon ya sami kujera ya zauna wayar shi ya fito ya danna number ta.

Ita ko Samha lokacin tafito wanka tana zaune tana tsara kwalliya da Sumayya ta koya mata,wayar tane ye k’ara kallo guda tayi mai taja gajeren tsaki,taci gaba da abun da take.

Wane kiranne ya k’ara shigowa d’auka tayi ta Kara a kunne tace,” Assalamualaikum”.

Jin muryan ta saida ya lumshe idanuwan shi kafin ya amsa da,” wa’alaikumusalam,ina falo”.

Tace,”owk” ata k’aice ta kashe wayar.

Cigaba tai da kwalliya ta saida ta gama ta ciro wani red material da ratsin fari ta saka d’inki riga da sket ne sunyi mata ciff gashi sun fito.

    Koni dana dubeta sai da nice tubarakallahu mashaAllah. 

D’aurin da tayi ya anshe ta sosai-sosai ba k’ara min kyau tayi ba takalmi plate shoe tasa fari.

Shiko yana zaune falo duk ya k’osa ta fito ya ganta dai-dai lokacin Sumayya tashi ganin shi zaune ya k’ura ma waje guda ido yasa ta cewa,”ango-ango tuna nin mi kake saura kwana biyune fa”.

Murmushi yayi yana duban ta yace,”Sis Sumy manyan k’asa ba’a ganin ku sai ancika form”.

Murmushi tayi tace,”Kai Bros sai kace wata kai yanzun ma abin da yasa muka ganka arha sabida zuciyar ka na nan ne”.

Yace,”haka dai kika ce ai nafiki kirki”.

Dariya tayi tace,”Bros baka da dama”.

Wuce wa tayi tace,”ina zuwa Bros”.

Yace,”tou ki sauri na shanyu na kusa bushe wa” .

Dariya tai ta wuce kitchen tasa me aiki ta kawo masa abinci da drinks kafin ta fita.

D’akin da Samha take ta nufa zata tura k’ofar kenan ta ga an bud’e k’ofar .

Gala-la Sumayya tayi tana kallon Samha.

Samha ko ganin kallon da take mata yasa ta rab’a ta gefen ta zata wuce.

Cafko hannun ta tayi suka sa dariya.

Sumayyah tace,”Sis kin ganki kuwa lallai yau in Salman ya ganki rud’ewa zaiyi”.

Samha ta d’aka mata dundu da wasa tace,”kefa kin fiye zolaya”.

Tace,”wallahi Sis ba zolaya”.

Ta’ba baki tayi ta wuce d’akin Mami ta wuce direct akan gado ta isketa tana waya zama tayi kan kujera tana jiran Mami ta gama wayar.

Sumayyah ce ta shigo tana dariya.

Lokacin Mami ta aje wayar tana duban Samha tace ,”Mashaallahu kin to kyau Samha”.

Samha ko duk’ar da kai tayi k’asa.

Mik’ewa Mami tayi ta d’auko wasu tiraruka ta zo ta kuma feshe ta dasu nan take wani k’amshi mai sanyi ya garwaye d’akin.

Gyara mata tsayuwan gyalen da tasa tayi kafin tace,mata taje tana zuwa.

Mik’ewa tayi ta fice, Sumayyah na bayanta sai surutu take mata amma taki ko kula ta.

Shiko k’amshi da ya juyo yasa shi lumshe idanuwan shi dayin wata San yay-yar ajiyar zuciya…………!

Manage please.
[11/23, 8:05 PM] Sumayya: ????????????????????????????????????
????????????????????
????????
????

????SAMHAA????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍????
{ Gaskiya d’aya ce daga k’inta sai b’ata burinmu mu fad’akar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}

    ```????G•W•A????```

GASKIYA DOKIN K’ARFE•????????

Written by khadeejatou Muhammad Basskkwace

Dedicated by KHADEEJATOU .S. DOGARAI(LIPTON GIRL)
wanga page nakine kadai my everlasting inkin so ki basu su karanta,inko kin gadama kihani su don wolle sabida farin cikin ki d’ai naishi

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Hip!
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Hip!!
???????????????????????????????????????? ????????????????????????????????????????????????????????
Hip!!!
????????????????????????????????????????????????

Appy birthday day to u my blood pressure Lipton Girl☕????

On dis day is our lovely sister was born mashaAllah.I’m so thankful bcoz I was blessed with golding Queen, Princess, Teacher,Aunty, Doctor, Friend nd a role model like u.celebrate ur birthday with maximum happiness! U always deserve d best, Sister on dis day I wish you oll d Albarka nd khairi of Allah on u nd yours families…..may he protect from oll d shairin in dis duniya nd hereafter.Allahumma Ameen Appy birthday KHADEEJATOU S DOGARAI(Lipton Girl☕)????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Bissimillah Rahamani Raheem

Page4⃣7⃣

__????Shiko k’amshi da ya jiyo yasa shi lumshe idanuwan shi dayin wata sanyayyar ajiyar zuciya.

Shigowa falon tayi kanta duk’e cikin muryan ta me sanyi da taushi tace, “Assalamualaikum”.

Bud’e idanuwan shi yayi yasauke kan k’yak’k’yawa fuskanta,take yaji miyo d’in bakinshi ya k’afe,inda yakasa ko k’wak’k’waran motsi illa tasbihi kawai da yake azuciyar shi.

K’arasa tayi tazauna gefen sa dayake two sitter yake zaune,suna juyo numfashi juna k’amshi tiraren ta da nashi da suka had’u ,sai suka bada wani sanyay-yar k’amshi me kwantar da zuk’atan masoya.

D’agowa tayi ta dube shi idon su karaffff ya tsark’e,take dukan su sukaji wani bak’on alamari ya ziyar ce su.

Da kewa tayi ta sakan mai sanyay-yar murmushi tare da cewa,”barka da zuwa Angona uban Y’ay’ana”.

Shima bai san-sanda murmushi ta su’buce mai ba yace,”yauwa Amaryata,kingan ki kuwa kin zama kamar awanke hannu ata’ba”.

Murmushi tayi daya k’ara ma fuskanta k’yawau kafin tace,”ai everlasting ban kaika ba ko kad’an,kangan ka kuwa?

Lumshe idanuwan shi yayi yace, “ki dena zolayata da cin fuskan ya isa haka mana”.

Murmushi tayi tace,”aikai ke zolayata”….!

Shigowa Sumayyah ne yasa ta tayi shiru.

Aiko tana shigowa ta fara musu tsiya nan take ta shiga camera wayar ta ta fara musu pics.

Shiko Salman sai style yakeyi Kuma yanda suke ba k’ara min kyau sukai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button