SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Salman da ya tsira masa idanuwan shi cike da ma-makin ya sauke ajiyar zuciya.
Shiko Muhseen sai huci yake kamar kumurcin maciji.
Salman ko ma-maki Abbas yake da haka suka sai abin da suka fito saya kowa da abin da yake sak’awa.
Dr ko sai kai da komowa yake a tsakiyar office d’in sa yana tinanin wato shi su Sha-ago suka yau dara zaiyi maganin su Kuma wallahi sai sun biya shi kud’in shi.
Samha ko da k’yar aka la-lashe ta ta tashi tashi ga wanka bayan ta fito ta gabatar da sallah la’asar kafin ta zauna Sumayyah ta fara d’an d’ara mata kwalliya.
Suma su Salman suna can suna shiri yayin da Muhseen yana zaune yana cije-cije sai kumbura yake sabida ranshi ya b’aci tun d’azu yak’i sake wa da kowa sai d’acin rai yake.
Salman ne ya kamo hannun shi ya fito da shi waje ya dube shi da kyau yace, “Muhseen miye damuwa ka?
Muhseen ya galla masa hara-ra yace,”wai kai kana sane wancan mahaukacin yana neman rayuwan ka amma ko a jikin ka”.
Murmushi yayi kafin yace, “Muhseen in kaga abu ya faru da mutun muk’addiri ne daga ubangiji don haka kar ka damu dashi ina tare da Allah”.
Muhseen ya k’ara galla masa hara-ra yace,”in kai ka k’yale shi ni ban k’yale ba kaduba dattijon da yasa aka kashe wanda beji ba be gani ba ya maida matan shi zaurawa,ya maida Y’ay’an sa marayu wallahi bazan barshi ba sai ya gane kuren sa”.
Shiru Salman yayi yana tinanin maganan Muhseen gaskiya ce,dafa kafad’a shi yayi yace,”naji Muhseen dole ad’au mata ki akan sa kabari mugama bikin nan musan yanda zamuyi”.
Muhseen yace,owk koma wa ciki sukai don cigaba da shiri.
K’arfe takwas dai-dai aka kawo motoci don d’auka wa’yan da za suje dinner,nan mutane suka fara shiga motor ana tafiya dasu.
Amarya ko tana zaune daga ita sai Sumayya suke zaune.
Wayar ta ne yayi k’ara ta duba sunan Salman ta gani tai picking bakin ta d’auke da sallama,amsawa yayi yace,ta fito,owk kawai tace.
Duban Sumayyah tai tace yana waje, k’ara gyara ta tayi ba k’ara min kyau tayi ba doguwar riga ce a jikin ta milk colour, chocolate colour d’in gwaggro ne akanta sai ta kalmin ta shima chocolate colour ba kyauwun da tayi ba’a cewa komi saide ace mashaallahu.
Fitowa sukai mutane suka nufi hara gidan wata motor me bala’in kyau da shek’i k’iran Benz milk colour.
Salman da ya hango fitowa su yayi saurin b’alle murfin motor ya fito ,shima cikin shigar riga da wando da malum-malum na material milk colour,da takalmi sa chocolate colour da hulan kansa ma haka sai murmushi ya ke don bak’ara min kyau tayi masa ba.
Itama kallon sa take tana murmushi don ya mata kyau sosai-sosai.
Bud’e mata k’ofa yayi ta shiga ta zauna,kafin yashiga.
Sumayyah gidan gaba ta shiga inda Muhseen yake zaune shike tuk’awa.
Salman rungumota yayi ya matseta ajikin shi sosai sunaji saukan numfashi juna nan su.
Muhseen ne yayi gyara murya.
Salman ya dube shi yace,”kai banson rashin mutunci ai mata-ta ce bawanda ya isa ya hanani ta’ba ta ehe”.
Sumayyah tace,”nidai kar ai abin kunya gaban k’anwan ka ehe”.
Salman yace,”inayine sabida ku in kun ji haushi kuma kuyi auren”.
Muhseen yace, “very soon in fad’a ma naso in riga ka shigar sauri kamin kawai”.
Dariya su ka sa banda Samha da duk kunya ya rufe ta sabida rik’on da Salman ye mata.
Wuri yayi wuri wajen ya cika tamk’am ba masa ka tsinke duk inda ka wulga mutane-ne kamar k’asa zuwan ango da amaryan shi kawai ake jira,can na hango.
Umaimah Aliyu, Jikanyar Hajiya, Lipton girl, Ummiey boko,Sumy,Queen Bilkisu, Innaro,Me Gwaza Zee Kwaila,Leat Lady,Hajiya Zainab,Sakina,Mom khaleed, da y’an Samha fans, Gaskiya written fans one nd two,Matarka ko Matata fans,izzar sarauta fans,Sis Naajaart fans,Abdurrahaman Don fans Sareena fans,Gidan mijina fans,Ummu Nabeel fans group.
Da dai sauran su sai rawa sukeyi masu yin selfies nayi,zuwan ango da amarya ne ya sa kowa ya koma wajen zaman shi ka fin MC ya basu umurnin shigowa……!
Sai Monday in Allah yakaimu
Inna Barar adduan ku fans
[11/23, 8:08 PM] Sumayya: ????SAMHA????
WRITTEN BY MRS BASAKKWACE
DEDICATED BY SAMHA FANS GROUP
Page 51
BISSIMILLAH RAHAMANI RAHIM
_???? shigowa sukayi cikin takun k’asaita gefen amarya k’awayen ta,gefen ango abokanan sa,suna tafiya suna d’an taka rawa kad’an-kad’an.
Ita ko Samha tafiya take ahankali kanta a k’asa yayin da hannunta na sak’ale a hannun Salman.
Takalmin dake k’afar ta sabida tsananin tsinin sa yasa zata tur gud’e, ta tafi luuuuuu har ta sadak’ar zata fad’i ta jita akan jikin mutum ya rungumota tsam ajikin sa.
Take wajen ya d’au tafi masu musu pic’s sai d’auka sukeyi kala-kala,don yanda sukayi ba k’ara min style ya bada ba.
Bud’e idanuwan ta tayi ta sauke akan k’yak’k’yawan fuskan shi,wani yerrr taji ajikin ta.
Saurin d’auke idon ta tayi,shiko Salman sungumo ta yayi a k’irjin sa ya fara tafiya da ita.
Itako lumshe idanuwan ta tayi sabida kunyar abinda ya mata cikin taro duban jama’a.
Wajen ko ihu ya d’auka da tafi.
Inda aka tanadar musu don su zauna nan ya aje ta,kafin shima ya zauna.
Sunkuyar da kai tayi kamar muna fuka.
M.C ko sai wasa ango da amarya yake.
K’ara harbin da suka fara jine a haraban wajen ya tashe hankalin kowani al’umma dake hall d’in.
Samha ko wani rik’o tayi ma Salman kamar zata shige cikin jikin sa.
Mazan dake wajen ne wasu daga ciki sukai saurin fita haraban wajen suga meke faruwa.
Da mamaki na ina fitowa wa zan gani
Dr ne hannun y’an sanda sun rik’e shi suna duka shiko sai cewa yake ku sake ni inje in kashe shi in yaso ku kashe ni daga baya dukan mu mura sa ta.
Kowa tsayawa yayi carko-carko suna alhinin abinda ya faru.
Muhseen ne ya fito da saurin shi ya k’ara sa inda police suke rik’e da Abbas,yana ganin shine,bai tsaya wata-wata ba yasa hannun ya wanka masa mari.
Wani k’ara Abbas ya sake tare da yin yunk’urin fisge kanshi aiko d’an sandanan ya sami kan bindigar da suka k’wace a hannun sa ya kafd’a masa a k’eya.
Aiko ya fad’i luuuuuuu yayi ƙasa sumam-me.
Aiko suka kwashe shi kamar shara suka watsa a motor.
Salman rungume da Samha a k’irjin sa tana kuka yafito dai-dai lokacin da aka sa Abbas a motor.
Cike da ma-maki take kallon Dr girgiza kanshi kawai yayi ya d’auke ta cakk ya wuce motor ya aje ta,da zai fito ta rik’e shi sosai tace, “please ka tsaya wallahi ina tsoro”.
Murmushi yayi ya shafa mata fuska yace, “Baby zan sallame bak’i ne,kinsan mun tara mutane”.
Bata ce masa komi ba illa sakin hannun shi da tayi,fita yayi ya kulle k’ofar.
Ko mawa yayi inda ilahirin mutanan hall d’in sun fito harabar wajen,kutsawa yayi inda Muhseen ke tsaye yana ta masifa kamar zai ara baki ya ja hannun sa gefe.
Muhseen yace,”lafiya Malan wallahi bazan k’yale wanan d’an mahaukaciyar ba yanzu da badin munsa police ba da ya kashe ka ya kashe ta ya kashe duk me k’aran kwana anan” yana maganan yana huci kamar kumurcin maciji.
Salman ajiyar zuciya ya sake,tare da cewa,” Muhseen nide yanzu ka sallami kowa please”.
Muhseen yace,”ai dole ma sallama kowa sabida wanga tsina-nne yazo ya tada mana hankali amma Allah ya isa wallahi”.
Salman bece komi illa kama hannun sa yayi suka koma wajen mutane, zuciyar Salman ba’a bin da take sai zafi da suya,kasa magana yayi.
Police ko tada motor sukai zasu wuce.
Muhseen yayi saurin k’arasawa ya tsaida su yace,yallab’ai ka aje min shi sai nazo,sa hannu yayi ya fiddo rafad d’ari biyar-biyar ya mik’a masa,bai jira me zaice ba ya juya ya wuce wajen bak’in su.