SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushin mugunta taimata .
Amsa sallama Salman yayi ,tare dawucewa yasamin kujera yai zaman sa ya lumshe ido.
Cikeda fara’a hajiya tace mata kishigo mana sannu da zuwa, gawaje ki zauna .
Kujera tasamu tazauna taushin kujeran saida tasa ta lumshe ido, bin falon take da kallo .
Sannu baiwar Allah.
washe baki tai yauwa “sannu hajiya”.
Duban Samha tai datake tsaye kamar mutum mutumi,tace “Samha kawo ma bakuwa ruwa”
Toh tace tai kitchen Jikinta asanyaye,azuciya ta take tinanin miyakawo inna nan gidan.
Afalo ko hajjiya tadube Larai,tace “baba ban ganekiba?”
fara matsan kwalla tai.
Hajiya ware ido tai tace “lafiya baba kike kuka”.
Dole inyi kuka hajiya ,wannan yarinyar me aikin ku yar kishiya tace yar iskace ita bata da aiki saibin maza ga shaye shaye ,shiyasa nazo infad’a maku ku koreta karta lalata muku yara harbidan mace take suna lalata, tafad’a tana k’ara fashewa da kuka
Daidai lokacin samha tafito kitchen.
Kofin dake hannun yafad’i ruwan ya zube,wasu hawaye masu d’umi suke bin fuskanta
Salman koh idonshi alumshe yake yana sauraran abin da take fad’a .
Hajia kalon wani raini kallon baki da hankali tai mata , adak’ile tace “toh Munji mun gode”
Inna larai koh cewa tai “dan Allah kukula dayaranku wallah batamuku su zatai nima saida. Tatab’a nemana ,tanayi tana matse k’walla”.
Kuka mai sauti Samha tafashe dashi tare dafad’in……..
yawan comments yawan typinga
comments.
share
vote
[11/21, 2:19 PM] Sumayya: ????????????????????????
????????????????
????????????
????
????SAMHA????
®????GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai barinta,burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}
NA
Khadeejat basakwace
Wannan page nakune
Masoyan wanan littafi,Allah yabar qauna.
Page 7
Bissimillahi rahmani raheem
Yana xuwa yace da ita yafita daga d’akin,a tsakar gida suka had’u kallon -kallo sukai ma juna,cike da mamaki take kallonsa aranta kuma tana tunanin me toh yakawo shi gidan nan,shiko murmushi yamata ,had’e da wani kallo ya fice,k’ofar motor ya bud’e kafin ya koma cikin gidan inda ya barta tsaye nan ya kuma isketa wuce ta yyi ,itako da ido ta bishi cike da mamaki .
D’akin ta nufa sa hannu yai ya d’ago shi cak kamar jariri yayo waje dashi, Laure koh bud’e baki da hanci tai tana kallonshi toh ina xai kai shi.
Yazo zai gitta ta,aiko ta damko rigarsa, tana fad’in ina xaka kaishi,ancema yana buk’atar temako ne ka maidashi,cikin daga murya take maganan.
Hada rai yayi tare da mata wani kallo,cikin tsawa yace sakemin riga karki shafamin datti.
Da saurin ta ta sake shi,saboda yana yin shi ya tsorata ta sai da taji cikinta ya katsa.
Wucewa yayi dashi waje,Samha dake bakin k’ofa tana ganin ikon Allah,itama tabi bayanshi ,munafuka algunguma kawai Larai ta fad’a tana galla mata harara.
Bayan motor ya k’wantar dashi ya gyara masa k’wancia ya rufo murfin motor,dai-dai lokacin ta fito,gaban motor tabude ta shiga,lokacin shima harya shiga,asbitin barau dikko ya nufa,kafin ya k’arasa ya d’aga wayarsa ya kira abokin sa Dr da a asbitin yake aiki,koda ya k’arasa basu sha wuya ba,wajen ganin likita,likitoci ukune suka rufa akansa suna dudduba sa.
Tsawon 1h,30munites kafin likitocin suka fito,Dr Abbas ne ya dube Salman fuskar shi d’auke da murmushin da ako yaushe be yankewa,koda kua cikin bak’in ciki yake baxa ka iya ganewa ba,saboda shi ma’abocin faraa ne ako da yaushe.
“Yace yasa me shi a office d’inshi,bayan shi Salman yabi,itako Samha tana xaune kan wani benci ta rafka tagumi tana tinanin nin halin da babanta yake ciki.
A cikin office d’in Dr Abbas ne xaune kan kujeran sa,yayinda ya nuna ma Salman wajen xama,shima xama yayi yana fuskan tarsa,haryanxun murmushine a fuskanshi,gyara xaman farin gilashin da ke manne a fuskarsa yayi.
Salman ne ya katse sa da fad’in ya me jikin?
Jiki da sauki Alhamdulillah, garin yaya yai mugun fad’uwar da ya jawo masa mutuwar barin jiki, gashi jinin sa a koda yaushe hawa yake k’ara yi.
Salman ne yai ajiyar xucia tare da fad’in.
“Wallahi nima ban san garin yaya ba,mahaifin mai aikin gidan mune,yau take fad’a mana halin dayake ciki shine nace mata muje kaisa asbiti a dubashi,amma bansan komi game da ciwon sa ba”.
“Allah sarki”.
Dr Abbas yace .
“Allah yabamu lada, dakai da kakawo shi,da mu da muka duba shi”.
“Ameen”. Salman ya amsa masa dashi.
“Am mun mai duk wata taimako yanxu haka ammai allurar bacci yana bacci,saide ba’a son hayaniya a inda yake,banda xuwa gaishe- gaishe ,sannan kuma in yaji sauki ya d’an murmure kwana biu,xaku rinka kai shi asbitin44 arinka masa gashi,don akwai yuwuwar xai mike”.
“Toh shikenan insha Allahu xanyi k’ok’ari”.
Cewar Salman.
“Allah ya k’ara masa lfy”.
Dr ne ya fad’i haka.
“Ameen”.Salman ya amsa dashi,nan sukai sallama ya mik’e ya fita.
Inda ya barta nan ya isketa ta kura mawaje d’aya ido,sam bata san ma ya dawo ba,kura mata ido yayi yana naxarinta,daga bisani bubuga gefen bencin yayi.
Firgigit ta dawo daga dunia tinanin da tatafi,murmushi ta kakalo tare da fad’in.
“Harka daw”?.
Bin ta da idanuwa yayi,tare da kare mata kallo,a hankali ya furta.
” Tunanin mi kike haka”.
“Bakomi”. Ta fad’a a tak’aice tace,tana mai sunkuyar da kanta.
Wayar shine da tai k’ara ya katse shi daga maganar da xaiyi,fiddo wayar yayi daga aljihu ganin me kiran sa yasa shi yin murmushi bai d’aga ba harsai da ya katse……….
Alkalamin me gwanjo????????
[11/21, 2:19 PM] Sumayya: ????????????????????
????????????
????????????
????
????SAMHA????
®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai barinta,burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}
Na
Khadeejatu muhammad(mrs basakwace)
Wannan page din nakane,mahaifina Allah yaqara maka lfy danisan kwana Ameen????
Page 6
Kuka mai sauti Samha ta fashe dashi, tare da fad’in.
“Haba Inna minai miki?, Inna bakison ki ganni cikin farin ciki,koh ina burin ki ki b’ata ni”.
Inna larai kuwa cigaba tai da matsan k’walla tana fad’in. “Haba Samha tsofai tsofai dani kike k’aryatani, eye nice xan miki k’arya ba laifin ki bane kinsha a nono”.
Hajia sororo tai tana nazarin maganar Inna Larai don ita sam bata.yarda da ita ba daga ganinta muguce,katseta tai da fad’in,. “Baba muji mun gode kinji saiki tashi kitafi ,tunda nija abinda ya kawo ki amma ban d’auka ba sai bayi bin cike.”
Waro ido Inna tai,tare da fad’in. ” Haba hajiya nifa kishiya uwarta ce nina rik’e ta tun tana shekara bakwai uwarta ta rasu tabarta ni kad’ai xan iya fad’a miki hal…….!”
Ya isa kitashi kiwuce akace mungode ,Salman ne ya fad’a idonshi lumshe danshi ko son ganin matar bayayi tunda ta shigo yaji ya tsaneta, don yasan mahimmanci sallamane kawai ya amsa,dabadan haka ba ko sallamar bai ansawa.
K’ara magana yayi yace.
“Zaki fita ko bazaki fita ba,saina sa anzo anmin waje dake?”.
Tashi tai jiki na rawa Tai hanyar fita,saida takai bakin k’ofa ta juyo ta dubi inda Samha take tsaye kanta akasa tana sharan hawaye,harara tagalla mata.
Sai caraf a idon Hajia,
Hajia ko mamaki take wannan wani irin matace ballagaza mara hankali.
Shiko Salman a zuciyarsa tunani yake dama wannan rayuwar yarinyar nan take da matar baban ta shiyasa kullum yake ganinta tana hawaye inta zauna ita kad’ai.
Hajia ce tace “Samha”.
Jajayen idanuwan ta ta d’ago tare da fad’in Na’am .