SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Zo ki zauna miyi”
magana”.
hajia tace.
K’arasowa tai falon jiki a sanyaye taxauna a k’asan capet, kanta a kasa.
Hajia ce ta k’are mata kallo tsawon minutes ,kafin tace “Samha ya kuke da matar nan?”.
“Matar babana ne. Ta bata amsa a tak’aice .
“Ke ina mahaifiyar ki? “.
“Ta zambabu,tun ina da shekara bakwai a duniya”.
Jinjina kai Hajiya tai,tare da fad’in. ” Allah sarki,Allah yaimata Rahma”.
Ameen samha ta amsa dashi.
Mahaifinki yana ina ne?
Yana gida kwance baida lafiya,sai ankwantar antayar.
Allah sarki Allah yabashi lfy .
Ameen, Cewar samha
Miyake damunsa?
Wallahi nima bansani ba ,abin da nasani yaje kama ruwa bayi zaiyi alwalar axahar don alokacin har antada sallah, yana sauri yaxame ya fad’i, tunda ga lokacin bai iya komi, sai de nayimasa.
Zaro ido Hajia tai kina nufin ke ke kula da mahaifin ki matar shifa baki da yayyune ina yan uwanshi,duk alokaci daya ta jero mata tambayimoyin nan?
Murmushi Samha tai wanda yafi kuka ciwo,tare da fad’in.
” ‘Yan uwan babana basa zuwa inda muke ,bama gari d’aya ,mu biyu ya haifa duka mata , Zainab ce babba mahaifiyar ta itace Inna Larai nima ni kad’ai mahaifiya ta tahaifa,har takoma ga mahallicin ta bata tab’a ko batan wata ba bayan ni”.
“Allah sarki,amma bakukai shi asbitiba anduba shi?”.
Tambayar data sake mata kenan.
“Hmmmmmm muna ta abinci,ta ina zamuje asbiti ba,bamu da kud’in zuwa asbiti,wama zaibamu,kullum ina addu’a Allah ya kawo mana d’auki nida mahaifina”.
“Allah ya kawo muku”.
Cewar Salman.
Salman da idonshi ke lumshe yana sauraran su,mik’ewa yayi yace ina zuwa,side d’in sa ya wuce ya d’auko key motor cike da tausayin yarinyar da mahaifinta,duk da baisan labarin su gaba d’aya ba ya tabbatar a mugun yanayi na talauci suke.
Dawowa yai ya iskesu inda yabarsu,Hajiya ta tsuramata ido cike da tausayi.
Magana yayi mata yace.
“Tashi muje mu d’auke shi mukaishi asbiti”.
Kallon Hajia Samha tai taga ta gyad’a mata kai cike da murmushi tace.
“Tashi kuje Samha karki ce komi”.
Mik’ewa tai jiki a santaye tabi bayansa,Wajen da aka tana da don aje motocin gidan ya nufa wata CRV baka ya bud’e ya shiga,da hannu yamata alamar tashigo,bud’e itama gidan gaba tai tashiga ta xauna ,tada motor yai maigadi ya wangale get d’in ,saida ya harba motor kan titi kafin yace mata.”Ina mukayi?”.
Kallon sa tai cikin rashin fahimta,da yaga tai shiru ta zuba masa idanu.
Yace
“Unguwar ku nike nufi”.Sunkuyar dakai tai cike da kunya tace.”K’waru majalisa shehu maccid’o road.”.
“Ina ne haka?, ta ina zamubi bansan wajenba”.
Fara gwada masa hanya tai har suka iso k’ofar gidan kafin tayi magana harya tsaya,packing. Yayi tare da kashe motor.
Ita tafara fita kafin yafito,dai-dai lokacin Zee ta fito daga gidan yauma da shigar ta irin na kullum sai taunan cingam take.
A d’age ta dubeshi ta yatsina fuska ,shiko ko kallon ta baiba ya wuce yabi bayan Samha.
Da mamaki take kallon shi,a zuciyar ta tana tinanin toh wayeshi meyaxo yi gidan su,Tsaki ta ja tawuce inda xata Cike da mamaki,tasa aranta inta dawo zata tambayi Larai waye shi.
Shiko bin gidan da kallo yake yana mamakin mutane ne ke rayuwa anan waje me kama da kufai,bai gama tsinkewa da lamarinba saida suka shiga d’akin,anan mamakin shi ya qaru.
Cike da fara’a ta duba babanta dake kwance gefensa wani kwarababben radio ne yake saurara tace.
” Baba sannu da gida”.
“Yauwa”.
Shi kad’ai ya amsa mata.
“Keda bakone”.
Tambayar da yayi mata.
“Eh Baba, a gidan su nike aiki”.
Allah sarki sannunka yaro.
” Yauwa sannu baba ya jiki?.
“D sauki yaro na gode”.
“Baba asbiti nazo mu kaika, ta fad’a mana halin rashin lafiyar da kake cikine”.
Baba ido ya zuba ma Samha,kafin yace.
” Haba Samha baki tab’a b’atamin rai ba irin yau miyasa xakije kina fad’an sirrin gidanku a waje haba Samha bansan ki da surutu ba”.
“Baba wallahi ba haka bane ba laifina bane”.
Labari Binta da Goggo tai ta bashi ,girgixa kanshi kawai yayi,tare da cewa Allah ya shirya matar nan.
D’agashi tai ta zaunar ta jinginar dashi ga bango ,Salman zuba masu ido yayi har ta gama ,kallon ta takai gareshi, tace kate maka mu mukaishi waje,baxan iya d’aukan shi ni d’aya ba.
Yana zuwa yace da ita ta fita daga d’akin,a tsakar gida suka had’u kallon- kallon sukai ma juna…..
Alkalamin khady????
[11/21, 2:19 PM] Sumayya: ????????????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????
????
???? *SAMHA* ????
®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }
???? ```G•W•A```????
GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????
Written by Khadeejatu Muhammad
Dedicated by Nabeelah bello bara’u
Bissimillahi rahmani raheem.
Page 8
Wayar shi da ta fara ringing ta katse masa maganar da zaiyi.
fiddo wayar yayi daga aljihu yana dubawa,ganin me kiran nasa yasa shi yin murmushi, bai ɗaga ba har sai da wayar ya tsinke.
maida kiran number yayi bugu biyu aka ɗauka.
“Assallamualaikum”
Salman ya furta fuska cike da murmushi.
Banji me na ɗayan ɓangaren take cewa ba, nadai ga sai murmushi take.
“Eh Mama da sauƙi, yanxun haka yana bacci”
cewar Salman.
Shiru ya ɗanyi na wasu minutes kafin yace,
“ok Mama”
nan ya kashe wayar fuskarsa ɗauke da murmushi.
Samha ko tsura mai ido tai taga yayi matu’kar burgeta, yayi kyau da ta ɗauka ya fiye walaƙanci ashe haka yake da kirki.
“kallon fa na mai nene?”
cewar Salman.
Cike da kunya ta sunkuyar da kai tafara wasa da zoben hannunta.
“Miye masabbabin ciwon Baba?”
“Faɗi yayi a bayi sai da nashiga na ganshi kwance ya kasa tashi, dagan shikenan ya kwanta ciwo,shine haryau bai iya fita saidai komi ayi masa”
“Allah sarki,tsawon wani lokaci kenan?”
Ɗan jim tai kamar me tinanin wani abu,kafin yace shekara uku da wani abu.
“Allah sarki,Allah yabashi lfy”
“Ameen”
ta amsa dashi.
Shiru sukayi dukan su na tsawon lokaci kowa da abin dayake sakawa a ranshi.
Wata motor ce tashigo harabar asbitin me launin ruwan toka wato Ash colour, parking tai inda aka tana da dan parking din motoci.
wata yarinya ce tafito acikin motor ga tsawo ga ƙiba, baƙace wulik kallo ɗaya zaka mata ka gano muninta.
wondo da rigane ajikinta duk ya matseta,da ƙyar take numfashi , fuskar ta manne da bakin gilashi????, taci wani uban kitson gashin doki harbaya, kafarta ko takalmi ne me tsinin gaske, cikin kwarewa take tafiyan ta.
Hartazo zata gitta su kamar ance takalli gefenta mizata gani Salman da wata.
gabanta ne yayi mugun faɗuwa, da sauri takara sa wajen idonta ya rufe taƙosa taji wacece wannan ƙazamar yarinyar.
Salman ko ganin ta kawai yayi gaban sa tana huci.
“Honey waye wannan ƙazamar da kuke tare?”
Samha ɗagowa tai tazuba mata manyan idanuwan ta.
Haɗa giran sama dana ƙasa Salman yayi, kamar bai taɓa daria ba,
“yace matatace wacce xan au……”
Wata uwar ƙara budurwan nan tasaki, hakan yajawo hankalin mutane wajensu.
“Wlh Salman baka isaba, baka isa ka aure wata ba bayanni ,ni zaka aura ba wancan ƙazamar kucaka jaka jahila ƴar gidan talakawa”
Murmushi Salman yayi tare da gyara tsayuwa kafin yace,
“da ita dake waye jaka jahila, waye kucaka ƙazama, ke kina nufin zan aurekine, dubeki fa duk wanda ya ganki yaga cikakkar ƴar iska kuma ƴar bariki….”
“Dakata!”
cike da tsawa da masifa take magana.
“Salman ni kake dangantawa da wannan ƙazamar talakan wulaƙantacciya, ni kake cewa ƴar iska karuwa, toh wlh sai na maida wannan ƙazamar cikakkiyar karuwa ………”