SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Keep following but dont forget to comment and share plsss.

Mrs Basakwace✍
[11/21, 2:20 PM] Sumayya: ????????????????????????
????????????
????

????SAMHA????

Na
Khadeejatu Basakkwace

Dedicated by my Qawas Nabeelah Muhammad. Dalhat.

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

   ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Bissimillahi rahmani raheem.

Page- 9NINE

“Dakata cike da tsawa da masifa take magaba,Salman ni kake dangantawa da wannan k’azamar talakan,wulak’antacciya,ni kake cewa yar’iska karuwa toh wallah sai na maida wannan k’azamar cikakkiyar karu……

“Bata k’arashe ba taji saukar mari hagu da dama,take hancin ta jini yafara fita.

“Dafe kuncin ta tai cike da bala’i tace kan uban can,nika mara harka fitar ma jini a jiki,yazakasan katab’o bal…….”bata rufe baki ba taji saukar wani sabon marin.

“K’ara daga hannu yayi zai wanketa dawani marin,Samha tai saurin rik’e hannu,ido ya zuba mata,itama ido ta zubamai,tare da girgiza kai.

Basu ankara ba saide taji saukan abu agoshin ta,wata azaba ce taratsa ta,dafe goshin tai tare da fasa k’ara.

A gigice ya ruk’ota,tare da cire hannun ta da ta dafe wajen,duban sa yakai ga Lubabatu dake tsaye rik’e da takalmi ta na huci.

Dank’ota yai niyan yi tai saurin ja da baya ,don tayi matuk’ar tsorata da yana yinsa da tagani,cire k’afar d’ayan takalmin tai ta kwasa a guje.

Baibita ba k’wafa yayi yakoma kan Samha da take dafe da goshi,rik’o hannunta yayi karon farko kenan da wani namiji yata b’a rik’e mata hannu,shima haka karan farko da yatab’a rike hannun wata mace,dukkansu saida sukaji bak’on al’amari ya ziyarto su.

Saurin janye hannunta tai daga nashi,zuba mata ido yayi,gaba yayi,ita kuma tabishi a baya.

Office d’in Dr yanufa direct tana biye dashi.

Dr Abbas yamike yana duban Samh tare da fadin “aa meyasame ta haka.”

Salman tab’a baki yayi kafin yace” Lubabatu tai mata haka,nan yakwashe komi ya fad’a masa.

Girgiza kai yayi cike da mamaki yace “Allah yasawaka.”

“Ameen”,cewar Salman.

Daidai nan akaturo k’ofa,wata nurse ce tashigo,gaishe da Dr Abbas tai.

Bai amsa ba illa cewa dayayi”kije da ita kiyi mata dressing.

“Ok sir tace,tare da fad’in “kibiyo ni”.

Bayanta Samha tabi don aimata dressing.

Sanyayyar ajiayar zuciya ya sauke,tare da maida kallon sa wajen Dr, murmushi ya k’ak’alo wanda bai kai zuci ba iyakan sa kan fuska”yace wallah Abbas narasa yanda zanyi da mayyar yarinyar nan ta matsamin”.

Dr Abbas dariya ya kwashe da shi tare da fadin “toh ka aure ta.

Harara ya galla masa na wasa tare da fad’in” ashe kai mak’iyina ne ban sani ba”.

Dariya Dr ya ci gaba dayi,tare da gwada shi da dan yatsa.

Tsaki yaja tare da mik’ewa yafice fuuuuuuuu.

Dr koh dariya yayi sosai kamar ME GWAZA???? taga abin dariya.

D’akin da aka kwantar da baba ya nufa,har yanzu bacci yake bai farkaba,zuba masa ido yayi cike da tausayi,lokaci guda yaji k’aunar tsohon ya shige shi ,take yaji k’walla ya cika masa ido ,juyawa yayi yafita,don inyaci gaba da kallonsa hawaye zaiyi.

A reception yakoma ya zauna ya k’ura ma waje guda ido kome yake tinani oho…..
[11/21, 2:20 PM] Sumayya: ????????????????????????????????

    ????????????????????

             ????????????????
                     ????????
                         ????







       ???? *SAMHA* ????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍

{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira. }

     ???? ```G•W•A```????

GASKIYA DOKIN ƘARFE•????????

Written by Khadeejatu Muhammad

Dedicated by Nabeelah bello bara’u

Bissimillahi rahmani raheem

Page 10

A reception ya koma ya zauna ya kura ma waje guds ido,kome yake tinani oho.

Samha ce ta qaraso hannun ta rike da ledan magunguna,goshin ta kuwa anwanke mata ansa plaster, fuska dauke da murmushi ta qaraso wajen shi tazauna daga gefen sa.

Shiko baima san ta tadawo ba ya lula duniyar tinani.

Kula da hankan da tai yasa ta dan bubbuga kujeran,kasan cewar ta karfene zatai qara.

Firgigit yadawo daga duniyan tunanin da ya lula,ganin itace yasa shi k’ak’alo murmushi tare dafad’in “har an gama miki?

Samha ta amsa da”eh harda magun guna suka bani.

Salman cewa yayi “mugani.

Mika masa ledan Samfa tai ya zazzage akan jikin sa ya dudduba kafin ya maida ya mik’a mata.

Amsa tai tarik’e a hannunta.

Mek’ewa yayi tare dafadin”kije ki zauna da baba ni zanje gida inkawo muku abinci,banda kuma surutu,inya tashi kikira Dr ya k’ara duba shi.

mik’ewa tayi itama tare da fadin “toh shikenan,Dan Allah kaba ma mama hak’uri yau ban mata aiki ba kar ta koreni ta cire a’albashi na.

Dariya ta bashi ya had’iye dariyan,saide baice uffan ba yayi gaba.

Binshi abaya tayi jikin ta duk yayi sanyi.

Motor sa yawuce yashiga kafin ya fara dariyan maganan ta ,tada motor yayi yafice daga harabar asbitin.

Itako d’ankin da aka kwantar da mahaifin ta tanufa,tura kofar tayi tashiga kasancewar dakin ba kowa shikad’ai ne Amenity aka basu,kujeran dake bakin gadon taja ta zauna,tsura masa ido tayi cike da farin ciki yau Allah ya amsa adduar ta yakawo mata way’anda zasu taimake mahaifinta,Allah ya musu albarka,Allah ya basu abinda sukeso duniya da lahira,dame zata sakamusu take tinani.

Ahankali yafara bude idon sa tarr akanta.

Ganin yabude ido tamike jikinta harrawa yake sabida tsananin murna,tana fad’in” sannu baba yaya jikin ,bari inkira likita ya k’ara duba ka.

Ruko hijjabin ta yayi yak’ura ma fuskar ta ido tare da fad’in” mai yasameki a fuska?

Dafa wajen tayi tare da d’an yin jimmm,ohhh baba bugewa nayi d’azunan.

K’uramata ido yayi yana nazarin maganar ta,kafin yace ayyya sannu garin yaya haka ta faru?

Dafe goshin ta tayi????????♀ohhh baba kabar tambayoyin nan,bari inkira likita ya duba jikin ka.

Waje tayi batare da tajira mai zai k’ara cewa ba,baa jima ba suka dawo tare da likitan yana gaba tana binsa abaya.

Bakin gadon ya qara sa fuskar nan tashi dauke da murmushi kamar kullum yace “sannu baba.

Ya amsa da”yauwa likita.

“Yajikin naka?

“Alhamdulillah da sauk.

“Allah yaqara sauki.

“Ameen,baba ya amsa dashi.

“Yanzun ina yakema ciwo?

“Ni dama ba inda yake min ciwo,gefe guda na sasaan jikinane dayake min nauyi.

“Ina kenan?

Gefen daman shi ya nuna ma Dr.

Kai hannunsa yayi yana daddana wajen,tsungulin sa yayi amma ko motsi,kamar ba ajikin sa ba.

Daukan file d’inshi yayi yai rubutu,kafin yadube shi yace “baba zaa daura ka kan magani inshaallahu zaka koma kamar da.

“Allah yasa likita.

Murmushi yayi tare dacewa “karka damu kaji baba,ka kwantar da hankalinka.

“Toh likita Allah yayi albarka.

“Ameen.

Ficewa yayi,ita kuma tadawo tazauna kan kujeran ta ruko hannun babanta,murmushi ta sakar masa.

mayar mata yayi shima,tare da fadin “ina yaron da ya kawoni?

“Yaje gida yadawo.

bud’o k’ofar da akayine yasa ta saurin juyawa taga mai shigowa.

Salman ne yashigo rike dawasu had’addun kuloli ahannunsa,mikewa tayi don ta taimaka masa.

Cewa yayi”basshi kawai,aje basket din yayi tare da fad’in” sannu baba kafarka ya jikin?

“Jiki alhamdulillah,nagode Allah yayi albarka.

“Ameen baba,amma bansan godiya nan,ai komin mutum yayi yima kaine,don watarana bakasan wanda zai mana kaba.

“Hakane dan na, ya mamanka da baban ka?

“Lafiya qalau sunce a gaisheka da jiki.

“Ina amsawa.

Kujera yaja ya zauna yadibe Samha dake tsaye yace “sama baba abinci in bashi.

“Toh tace,ta isa inda basket din yake plate tadauka da saving dinsa tuwan faran shinkafa ne da miyar taushe yasha tantak’washi,da dan yawa ta zuba masa,mika masa plate din tai da cibi ,amsa yayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button