SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

It kuma mikewa tai ta hau gadon tada ga kan baba ta zare pillow, jinginar da pillow ajikin bango tai kafin ta tallafo shi ta zaunar dashi.
Ido ya zuba mata yana mamakin k’okarin ta,matso da kujeran yayi ya daibo tuwon ya kai masa baki.
Kawar da kai baba yayi tare dafadin “dan Allah kabata ta bani dawai niyar tayi yawa haka.
“Haba baba miyasa bakaso inbaka in sami lada kodan ni ba d’an kaba ne?
Murmushi yayi yace “aa wlh ai kaima d’ana ne ,kawai dai na ga d’awai niyar tayi yawane.
“Toh bude baki in baka.
Budewa yayi yana bashi yana ci yaci sosai don yaji dad’in tuwon dan atunanin shi zaice tunda yake bai taba cin tuwo me dad’in saba.
goran ruwan Gajere water yadauko ya bude ya tuttula masa akofi yabashi yasha,sai da yasha me isarsa kafin ya cire kofin.
“Allah yama albarka kaida iyayenka.
“Ameen baba.
KHADEEJATU MUHAMMAD
[11/21, 2:21 PM] Sumayya: ????????????????????????????
????????????????????
????????????
????
???? *SAMHA* ????
®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍•
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira }.
????G. W. A????
GASKIYA DOKIN ƘARFE ????????
Writing by
Mrs basakkwace khadeejatu
PAGE1⃣1⃣
Bismillahir Rahmanin Raheem.
Goran ruwan gajere water yadauko yabude,tuttula mass ruwan ruwan yayi a kofi yabashi yasha,saida yasha ruwan me isarsa kafin ya cire kofin.
“Allah yama albarka kai da iyayen ka,cewar baba.
“Ameen baba,Salman ya amsa dashi.
Yau tsawan sati d’aya malan Sale na kwance a’ asibiti,
hakata kasance,Samha ke kwana da baban ta a’asbiti,kullum Salman ke kawo musu abinci,safe da rana da dare,kuma kullum shike ba ma mahaifin Samha abinci,suyi hira, shakuwa tashiga tsakanin su sosai, kasancewar ya watsake sosai,Hajiya Mahaifiyan Salman ma tazo taduba shi harso biyu,godiya yarinka mata kamar zai cire baki , ta nuna masa batason godiya komai mutum yayi yama kansa ne.
yau suke sa ran sallama,kuma gashi tun safe yau Salman bai zoba Driver ne yakawo musu abincin safe da na rana,ita tazauna ta ciyar da mahaifin ta sunayi suna hiran karamcin mutanan nan ,ba abin da zasu sakamasu dashi sai addu’a don basu da abin da zasu basu.
Niko danake gefe nace baga Samha ba ka aura mashi ita shine kabiya su halaccin da sukai maku.
A ban garan Salman koh tun lokacin da yakai mahaifin Samha asibiti,yakira masu aikin gini suka rusa ban garan baba dawani daki na kusa da shi akafara sabon gini.
Inna Larai koh dawa Allah yahada ta inba dashi ba,masifa zagi da cin mutunci,baitaba daga kai ya kalle ta,abin ba matukar mata ciwo hakan da yakeyi,masu aikin ma masifa take masu,dayake Salman yace dasu ko me zata masu karsu tanka ta ,shiyasa basu tanka ta.
a kwana hudu sungama komi,dayake yasakar musu kudi,company suka zo suka shirya furniture din dakin ba qaramin kyau dakin yayiba ya tsaru sosai,inkana dakin saika rantse ba’a kwarababben gidan nan me zagaye da langa langa kake ba.kofar dakin ma abin kallo ne.
Inna Laraiko ta k’ulu iyakan mak’ura,jitake kamar ta sheke shi ya mutu tahuta,aida y’arta Zainab yafi dacewa dakin bawannan k’axamin rakwabbaben tsohon ba da shegiyar y’arsa ba,gashi yau kwana Zainab bakwai bata gida ko kud’in kashewa bata dashi ga ba abinci da zataci dole yau tafita makwafta ko bara tayi taci.
Tana zaune ta rafka tagumi a kofar daki tana ta saka da warwara,abin duniya duk yamata yawa.
“Asaalamualaikum,Salman ne yashigo gidan bakin shi d’auke da sallama bayan shi ko Malan habu da driver ne dauke da k’aton akwati,wuceta sukai bawanda yamata magana kasancewar Salman ya gargad’e shi dakar ya tanka ma kowa.
kallon tsana tabishi dashi tare da tofar da miyau.
Shiko ko kallo bata isheshi ba,ciro key yayi a aljihu ya bud’e kofar yashiga yayi Malan Habu yabishi abaya.
A falo yamasa umurnin da ya iji akwatin yad’auko sauran ijewa yayi yafice ,zama yayi kan dayan daga cikin lafiyayyun kujerun da suka qayata falon.
Kuyi
manage
Da wannan
[11/21, 2:22 PM] Sumayya: ????????????????????????????
????????????????????
????????????
????
???? *SAMHA* ????
®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍•
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira }.
????G. W. A????
GASKIYA DOKIN ƘARFE ????????
Writing by
Mrs basakkwace Khadeejatu
Wannan page nakine aunty umaimah inna matukar jin dad’in comment d’inki ,in kin ga dama kibasu su karanta in kin gadama kirike kayan ki ke kad’ai ,Allah yabar qauna Ameen.
PAGE1⃣2⃣
Bismillahir Rahmanin Raheem
A falo ya masa umurnin da ya ijiye akwatin ya d’auko sauran, ajjewa yayi ya fice,zama yayi kan d’aya daga cikin lafiyayyun kujeran da suka k’ayata falon,lumshe ido yayi yana sauke sanyayyar ajiyar zuciya.
Malan Habu drive sai da ya gama kwaso akwatinan kafin yace.
“Oga nagama shigowa dasu”.
Daga masa hannu yayi ba tare daya bud’e ido ba yace.
“Ka jirani a motor”.
“Toh”. Ya amsa dashi yasa kai ya fice.
Tsawan lokaci yana zaune idon sa alumshi tinawa da yayi yabarsu a’asbiti kuma Dr Abbas yakirashi yace ya sallame su yasa yayi saurin mik’ewa ya fara jan akwatin yana shigar dasu bedroom d’in,saida yashigo dasu duk hud’u kafin ya fiddo da kayan ya jera a wardrobe.
zaro ido nai cike da mamaki ganin duk yawan akwatinan nan duk kayan baba ne bana Samha,rik’e baki nai nace toh ita kuma Samha fa?
Kude cigaba da bina zakuji ya za’ayi da Samha,zataci gaba da zaman gidan ne ko a’a.
Sai da yaga ya shirya komi kafin yafito ya kulle d’akin yanufi waje.
Dai-dai zai fita itakuma zata shigo yauma kama kullim kusan zance shigar yau kusan tafi ta kullum,sanye take cikin riga da wando rigar ko cibinta bata rufe ba sai wani wando pencil kan nan yasha kitson gashin doki kala hud’u fari,jaa,bulu,dame ruwan bula kai ko kallabi babu,kafan nan sanye dawani takalmi me tsinin gaske,taunan cingam take kamar karuwa k’as,k’as,k’as, kawai kake ji.
Saura kad’an ta bigeshi yayi saurin jada baya cike da k’yama yake kallonta.
Itako zuba masa ido tayi kamar zata cinye shi.
Kara had’a giran sama dana k’asa yayi yasha kunu yace
“Lafiya kiban hanya in wuce”.
Kaucewa tayi amma bata bar kallon sa ba har yafice.
Wucewa yayi fuuuu cike da haushin ta,tunani yake toh waye wannan a gidan nan,daga ka fad’a yayi alaman ohoo.
Itako cikin gida ta fad’a tana kwala ma Inna Larai kira
Larai! Larai!! Larai!!!
A sukwane tafito tana d’aura zani naneman fad’uwa,tana fad’in.
“Lafiya yar albarka”.
“Waye shi”?.
Ta tambayeta
“Wa kenan”.
Amsa ta bata
“Wanda yafita”.
“Ohhh tsinanne yaronan,ashe kike nufi baki lura da sauyi a gidannan ba.
kalle-kalle tafara zuba masaban ginin da akai ido tareda fadin
“Amarya za’a akawo gidan nan,ina kucakar nan da me dattin hula”?
Uhm ta taba baki tare da fad’in bawata amarya d’akin Sale ne da shegiyar yarsa.
K’ara gwalo ido tayi “kina nufin shiya masu?
“ko shakka babu.
“toh waye shi?
“Wanda take aiki gidan sune,wayasani koh yagama lallata tane.
“Aikam biri yayi kama da mutum.
Inna Larai tace “kin ishe ni da tambaya kamar yar jarida nide kizo kibani kud’i yunwa nake ji.
“Ke kenan kullum maitan kud’i bakya gajiya da bani bani mushiga ciki”.
Ta k’are maganar tana k’ok’arin shiga d’aki
Shiko direct asbiti suka nufa yana shiga ya iske su zaune suna hira da murmushi ya k’arasa kusa da gadon ya duka har kasa yace
“Tuba nike baban mu”.