SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

SAMHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hada rai Dr yayi shi adole yayi fushi,”shikenan baba tunda ni baka daukeni amatsayin yaronka ba da zanma Samha kyauta ku nuna bakwaso.”

Salman ne yaja tsaki tare dacewa “malan ka ishemu dalla kabar mutane su wuce ban hanya,mutun sai surutu kamar ya haɗiye radio,mtsuuuuu.”

Murmushin dole yayi yamatsa daga jikin motor yana faɗin” Allah ya huci zuciyar ka aminina.”

Salman koh buɗe murfin motor yayi yafaɗa yatada motor,hararan Dr yakuma yi tare da fadin “parrot kawai.”

Dariya Dr yasa tare dacewa “ba komi nide zankira ka kabama Samha wayar musha hira.”

Salman baice komi ba yayi gaba.

Dr koh murmushi yayi dan yasan halin abokinshi bai cika son magana ba,juyawa yayi yanufi office dinsa.

Tuki yake suna hira da baba saida yabiya dasu chicken republic yasayi take away kafin suka kama hanyar gida,adaidai ƙofar gidan sukai parking ita tafara fita miƙa mata key yayi cike da mamaki take kallonta tace “mai zanyi dashi.?”

Salman yace “daki zaki bude kwashe ledojin nan ki shiga dasu.”

kwasa tayi bata ƙara cewa komi ba tai cikin gida a tsakar gida ta iske Inna Larai tana hada wuta yaqi ci cike da fara’a tai sallama

koh ansa mata batayi ba illa harara da ta galla mata tare da jan tsaki .

murmushi kawai tayi don ta kwana dasani baza ta ansa taba”sannu inna da aiki.”

a fusace tadago tace” ke “tana gwadata da ɗan yatsa” zanci uwarki kika qara ko kulani mayya kawai kurwata kurrrr ,kin cinye uwarki yanzun kin kama ubanki Allah baibaki saa ba yamutu ba shine zaki dawo kaina toh li’ilafi wallahi.”

Daidai lokacin Salman yashigo dauke da Baba,yaji duk zagin da yake mata kallonta yayi da take tsaye yace “ba kofa nace ki bude ba kika tsaya?”

Turus tai ganin dakinsu yanda takoma juyowa tayi tazuba masa manyan idanuwan ta.

hada rai yayi “zaki bude ko kallo na zaki tsay yi.?”

ƙarasa wa tayi jiki a sanyaye ta budesai da gabanta yafadi ganin yanda dakin su yakoma.

Baba ma haka cike da mamaki yake kallon shi.

shiko kauda kai yayi kamar baisan sunayi ba,direct parlour yashiga dashi akan tsadaddan kujera ya ije shi ya zaunar dashi.

Daga Baba har Samha kallon ɗakin suke,kuka Baba ya ya fashe dashi sabo da murna.

da gudu ta qaraso inda Babanta tariƙe masa hannu tana hawaye itama tace “Baba dan Allah kadena kuka banson ganin hawayenka “tanayi tana goge masa hawaye……..

kuyi manage bakwa comments sosai.
[11/21, 7:10 PM] Sumayya: ????????????????????????????
????????????????????
????????????
????

      ???? *SAMHA* ????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira }.

????G. W. A????
GASKIYA DOKIN ƘARFE ????????

Writing by
Mrs basakkwace khadeejatu

wannan page naku ne SAMEEHAT FANS GROUP ina matukar jin dadin comment dinku inkun gadama kuba mawasu su karanta in kungadama kurike abun ku ku daya Allah yabar k’auna Ameen.

PAGE1⃣4⃣

Bismillahir Rahmanin Raheem.

Da gudu ta k’araso inda babanta ,ta rik’e masa hannu tana hawaye itama tace “baba dan Allah kadena kuka banson ganin hawayenka”.
Tana yi tana goge masa hawaye.

Shima sa hannunsa da yake aiki yayi yafara sharemata nata hawayen yace “Samha wannan hawayen bana komi bane illa na farin ciki ban haifa Salman ba amma ya temake mu yakaini asbiti sannan yagyara min muhalli dame zan saka masa”.

Shiko Salman yayi kasak’e ya had’e hannaye a k’irji ya zuba masu ido cike da tausayi yace “Baba kadena kuka nayi maka ne don Allah badon komai ba,kuma banaso inji kalamar godiya daga bakin ka”.

Samha da Baba zuba masa ido sukayi cike da mamakin hali kalan nashi,tun balle Samha da ada take ganin shi kamar yafiye girman kai da wula’kanci yanxu ko taga ne ba haka bane ashe haka yake da kirki.

Ledan abinci da yake gefe ya d’auko ya zo ya zauna gefen Baba ya dube Samha yace.” D’auko plate a kitchen da cokoli”.

mik’e wa tayi tai hanyar bedroom ta d’auka nan ne kitchen d’in.

Cewa yayi “kenan zaki shiga da hannu ya gwada mata”.

juyowa yayi cike da kunya ta nufi inda ya gwada mata kitchen din yahad’u komai na ciki pink da blue ne komai antsara shi inda yakamata inda taga anjera plate d’in ta nufa tad’auko tasa hannu taciro cokali tad’auraye a inda aka tanadar dan wankewanke kafin tafito takawo mai har k’asa ta durk’usa ta aje cike da ladabi.

Ledan ta bud’e ta juye abincin shikafa ce daf duka da kaza agefe sai k’amshi yake tashi da tiriri,mik’a masa tayi ya amsa.

ya dubeta yace “haka ake kawo abinci ba ruwa ko drinks”.

sunkuyar dakai tayi tamik’e tanufi kitchen firiza ta bud’e taga ruwan gora masu yawa da drinks kala -kala rasa drinks din da zata d’auka tayi,rufe ido tai tasa hannu ta d’auko d’aya tana bud’e wa taga frashyo milk ne murmushi tayi ta d’au ruwan takoma falon ta ije agaban Salma.

baice mata komaiba saida ya gama ba ma Baba abinci kafin yace.

“Keko za’ayi k’azamar gida wlh ,zaki kawo ma mutane abu ba’a cikin plate ba sannan babu kofi kina nufin gorar za’a sa masa abaki”.

shiru tai ta sukuyar dakai cike da kunya ta nufi kitchen din a karo na uku azuciyarta ko cewa take shide wannan akwai sa aiki ba’a masa gwaninta samm,d’aukan kofin tai da plate saida ta d’auraye kafin tafito ta kawo ta ije masa ta koma d’ayan kujeran tai zamanta ta sunkuyar da kai tana wasa da zoben ta.

shiko ganin haka tab’a baki yayi ya bud’e gorar yaxuba masa ruwan yabashi yasha saida ya isheshi yamai alama daya cire kofin,cirewa yayi yadauko freshyo d’in zai bud’e Baba yace masa”a’a Salmanu bashi haka kabari sai anjima.

maidawa yayi ya aje ya kwantar da kanshi jikin kujera ya lumshe ido tsawan lokaci kafin ya bud’e yafara tattara kayan,alama zai kai kitchen.

da sauri tamik’e tana fad’in yi hakuri yaya bashi inkai.

shiko ko kallonta baiyiba ya aje yakoma ya zauna ya lumshe ido.

Tatttara kayan tayi takai kitchen sauran abincin ta zauna taci akan kujeran da tagani aciki sai da ta k’oshi ta d’aga gorar ruwan ta kwankwad’e kafin tamik’e takai kwaninkan wajen wanke- wanke tabud’e fanfo tafara wankesu ta maida kowanne mazaunin sa gorinan ko ta watsa su a kwandon shara da ledan da akasayo musu abinci .

Afalo ko Salman ne ya dube baba dayake zaune yayi shiru yace ” Baba nayi maka wani karambani ban fada maka ba dan Allah karka d’auka da wata manufa nayi saide don taimako”.

katse shi Baba yayi dacewa Salmanu koh miye kayi zanyi farin ciki dashi matukar bai sab’a ma addini ba,fad’amin Salmanu yaran kirki Salmanu baka laifi awajena.

Jim yayi na d’an lokaci kafin yayi murmushi shiru yayi kamar me nazarin wani abu.

Baba yace “haba Salmanu tunanin mu kake kafad’a min kawai koma miye zan karba da hannu bibbiyu.

murmushi Salman yayi kafin yace wani kyauta nama baba Allah yasa zakai farin ciki.

murmushi baba yayi yace “Salmanu na gode na gode nasan kowani irin kyauta kamin me kyaune da nagarta Allah tayi albarka.

“Ameen baba banson godiyan nan baba,jimmm yayi kadan kafin ya sunkyar dakai yace baba AURE na k’ara maka.

Gwallo ido baba yayi dajin wannan bazatan.

dai_dai lokacin Samha tasawo kai cikin falon tatsaya waje d’aya ta daskare cikin rawan murya tace AU..AUU..AURE kuma yaya……..

yawan comment dinku yawan typing d’ina,
[11/21, 7:10 PM] Sumayya: ????????????????????????????
????????????????????
????????????
????

      ???? *SAMHA* ????

®☄
GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍
{ Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira }.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button