A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL
Mallama Rabi tunda Hajiya Munawarra ta fara magana taji wani irin farinciki da sanyi na ratsa zuciyarta Dan adduarta kenan kullum Manal ta koma d’akinta,Dan tana tausayinta sabida ‘yayenta ba k’aramin tsangwamarta suke ba kamar tayi mata kuka wani sa’in har Dan dai dai dai Affan ya rainata baya girmama ta yanzu,tunda yaji abinda ta aikata,babu Wanda zai kaita farinciki indai Manal ta koma d’akinta Dan har gara ace Yusuf ne yake wulakanta ta akan wulakancin da yay’enta suke mata,murmushi Mallama Rabi tayi tace ” ba komai tace babu komai Hajiya Allah ya k’ara kad’e fitina Dan an b’atawa juna sai dai Hakuri kawai,Manal dake zaune kanta a sunkuye wani irin farinciki ne ya ringa ratsata Dan burinta aduniya kafin ta koma ga mahallincinta bai wuce taganta a d’akinta ta nemi yafiyar mijinta ba,ta gyara kuskuren da tayi abaya,tasha alwashin ko wane irin wulakanci Yusuf zai mata zata jure Dan koma mai ya mata ita ta jawo,ahaka suka d’an tab’a hira Hajiya Munawarra ta umarci Manal taje ta had’a kayanta Dan tare zasu wuce,su Hanif ne suka tayata shirya kayanta,duk da kayan bawani masu yawa bane,Dan mallama Rabi ce ta didinka mata,Mallama Rabi har bakin mota ta rakasu tana yiwa Hajiya Munawarra godiya,tana yiwa Manal addua,ahaka suka ja mota suka tafi, Su Hanif sun saka Manal a tsakiya sai labari suke bata.
Sai da aka b’alla gate d’in gidan suka shiga Dan babu mukulli ahanun Manal,har Palo Hajiya Munawarra ta raka su manal, ta zauna tana jiran Driver da ya tafi d’auko welder Dan agyara gate d’in,sai wajen k’arfe takwas ta bar gidan bayan ta gama yiwa Manal dogon nasiha,Manal kuwa bayan ta rakata ta dawo,ahankali ta shige d’akin Yusuf ta kwanta a kan gadonsa ta lumshe ido tana tunaninsa,hawaye na zubo mata,take ta tuna duk abinda ya faru aranar da zata bar gidan kuka taci ta gode Allah tana tsinewa su Hajiya kaltume,atakaice tare suka kwana da yaran barci tayi mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali,rabonta da barci irin wanan tun kafin tafara cin amanar Yusuf.
Washegari su Hanif basu je makaranta ba tare suka taya Manal gyara gidan,su Hanif sai murna suke yi,Manal zage dantse ta k’ara yi wajen bawa yaranta tarbiyya da gyara gidan aurenta,ahaka tasamu sati biyu da komawa gidan,duk da kullum a cikin fargaba take Dan batasan ya zasu kare da Yusuf ba in ya dawo ya sameta a gidan.
B’angaren Yusuf kuwa hankalinsa ne yafara tashi daya ga inya kira Hajiyarsa bata d’auka Abu kamar wasa sati d’aya da kwana biyar kenan rabonsa da yaji muryar yayansa,duk wata hanya da zai bi Dan an had’a shi da Hajiya Munawarra ta waya, Hajiya Munawarra ta toshe nan da nan hankalinsa ya k’ara tashi Dan yasan this time around Hajiyarsa ba k’aramin fushi tayi dashi ba,shirye shirye ya fara yi na tafiya kano,inda yasa ranar Sunday zai taho kano,ranar Sunday kuwa da sassafe ya taho kano,aranar da Manal ta cika sati biyu da kwana d’aya da komawarta gidansa,gidansu yayi niyyar wucewa direct da ya iso kano,amma ganin agajiye yake likis yana bukatar yayi wanka ya huta kafin ya nufi gidansu ne yasa ya d’auki hanyar gidansa.
Gobe zan gama insha Allahu kuyi maneji da wanan
[10/14, 6:56 PM] Sadnaf: ???? S????N????DIN GROUP
Written by
???????? SADNAF????
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
A short novel based on true life story
Page 65-70
????????????????????
ALHAMDULILLAHI RABIL ALAMIN,ALHAMDULILAHI ALLAH ABUN GODIYA ALLAH NA GODE MAKA DAKA BANI IKON KAMMALA LITTAFIN ????S????N????N????DIN GROUP,DAN IKONKA NE BA NAWA BA,YA RABBI KA DUBENI DA IDON RAHAMA DUK KUSKUREN DA NAYI AWANAN NOVEL D’IN ALLAH KA YAFENI NAYI NE DAN NA FADAKAR,NA WA’AZANTAR NA KUMA TSORATAR DA MATA DA SUKA TSINCI KANSU A RIN WANAN HALIN,ALLAH MASU YI KA NUFESU DA SHIRYA ,MU KUMA KA TSARE MANA IMANINMU MU FI K’ARFIN ZUCIYARMU AMEEN????????
NOTE WLH TALLAHI A GASKE WANAN LABARI YA FARU,EXACTLY YANDA AKA BANI NA RUBUTA,ABINDA NA D’AN KARA KADAN NE WACCE TA BANI LABARIN ALLAH YA TSARE TA YA GANAR DA ITA GASKIYA BATA KAI GA FAD’AWA HALAKA BA,KUMA BASU RABU DA MIJINTA BA,DAN HAKA BABU YANDA ZAN RUBUTA MANAL TA RABU DA MIJINTA DAN NAGA WASU SUN FARA KIRANA SUNA MUN TEXT DA BAI KAMATA YUSUF YA MAIDA MANAL BA IDAN NAYI HAKA SAKON DA NAKESO NA ISAR BAI ISA BA,KO D’AYA INASO KU GANE WANI ABU MANAL BATA KAI GA AIKATA ZINA BA,KUMA TUN KAFIN ASIRINTA YA TONU TA FARA NADAMAR ABINDA TAYI,ALLAH NE YAYI IKONSA YUSUSF YA GANI DAN TA NEMI YAFIYARSHI,KUMA YUSUF BASHIDA HAKKINTA,KO A IYA NAN NA TSAYA SAKON DANA KESO NA ISAR YA ISA GA WAYANDA SUKA TSINCI KANSU A IRIN WANAN HALIN ,DAN NASAN AKWAI MATA DAYAWA DA SUKE CIKIN WANAN MASIFAR DAN YANZU GROUPS YA YAWAITA IDAN BAKA FAD’A IRIN WANAN DA HAJJA KALTUME TA BUD’E BA ZAKA FAD’A NA ‘YAN LESBIAN DAN ABUN YA ZAMA RUWAN DARE SAI DAI FATAN ALLAH YA SHIRYESU YA GANAR DASU GASKIYA
WANAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA DUK WACCE TAKE KARANTA A SANADIN GROUP DA K’WARIN GWIWAR KU NA SAMU NA KAMMALLA
AUNTY SIS????BANI DA ABINDA ZANCE MIKI SAI DAI NAYI MIKI ADDUAR FATAN ALHERI ARAYUWARKI BUKATUNKI NA ALHERI ALLAH YA BIYA MIKI COS SAMUN IRINKI YANZU A ALUMMA SAI AN TONA KINA BADA GUDUNMAWARKI SOSAI TA FANIN RUBUTU WANDA AL UMMA ZASU KARU SU AMFANA ALLAH YASA MUTUWA CE ZATA RABAKI DA DADDYN SULTAN ONE LOVE❤❤❤❤
BAN MANTA DAKU BA
????HARTY
UMMI AISHA JINJINAN BAN GIRMA GAREKU
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS ,LOVE YOU OLL FROM THE BUTTOM OF MY HEART YOU GUYS ARE DOING A GREAT JOB ,UP UP UP UP PURE MOMENT OF LIFE WRITERS YOU GUYS SHOULD KEEP D FIRE BURNING,HATERS ARE OUT THERE TAKING PANADOL ON BEHALF OF YOUR HEADACHE, PURE MOMENT FORWARD EVA BACKWARD NEVA ,PURE MOMENT I CAN’T HRT YOU LESS
STRONG PEOPLE ALWAYS FORGIVE AND FORGET,WEAK PEOPLE ALWAYS FIND ONE WAY OR THE ODER TO REVENGE BE STRONG????????
Parking yayi,ya fito daga motar dan ya bud’e gate d’in gidan,ga mamakinsa sai ya ga k’ofar a d’an bud’e,tura k’ofar yayi cikin tsananin mamaki ya shige,ahankali ya fara bin ko ina da kallo yana nufar palon, kamshin turaren wuta ne ya ringa dukan hancinsa,da d’an Sauri ya k’arasa palon,su Hanif ya hango a zaune suna kallo mamaki ne ya k’ara rufeshi,ya kira sunan Hanif a tare suka juya da sauri,suka nufi Inda yake aguje,rage tsayinsa yayi ya rungumesu gabad’aya wani irin farinciki da nutsuwa na ratsa shi,Dan rabon da yaji irin wanan farincikin tun kafin Manal ta ci amanarsa,
Manal da tana gama shiryawa kenan,bayan ta fito daga wanka,tana sanye da wani doguwar Riga na material ya d’an yi mata yawa sakamakon ramewar da tayi,fitowa tayi Palo hanunta rik’e da Qurani dan duk safen asabar da lahadi su kanyi tilawa ita da su hanif,zuwa inda suka tsaya,daga nan sai ta k’ara musu,cak ta tsaya gabanta yayi wani irin fad’uwa data hango Yusuf rungume dasu Hanif,kamar cewa akayi Yusuf ya d’ago suka had’a ido da Manal,shima gabansa fad’uwa yayi,ya zame su hanif daga jikinsa ya mik’e tsaye yana kallonta,Manal sunkuyar da kanta tayi,gabanta na cigaba da fad’uwa Dan bata San ma’anar kallon da Yusuf ke mata ba,Yusuf d’auke kansa yayi daga kallonta,ya nufi d’akinsa shi ba bak’inciki ba shi ba farinciki ba,Manal bayansa tabi da kallo har ya shige d’akin,hawayen dake k’ok’arin zubo mata ta mayar da sauri, ta kalli su hanif tace su fara tilawa kafin ta zo,ta nufi d’akin Yusuf gabanta na mugun fad’uwa,Yusuf yana shiga d’akinsa ya lumshe idonsa sakamakon wani kamshi da ya bugi hancinsa d’akinsa a gyare yake tsaf gadon nan a liliye,a gafen gadon ya zauna yafara tunanin yanda akayi Manal ta dawo ba tare da shi ya je gidansu ba,turo k’ofar da Manal tayi ne yasa ya d’ago ya kalleta,Manal kuwa tayi sauri ta sunkuyar da kai tana murza hanunta,so take tayi mishi sannu da zuwa amma bakinta yak’i bud’uwa,Yusuf kau da kansa yayi yace “wa yace ki dawo alhalin ba ni nace ki dawo ba”?