ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

  Shiko mallam lawal koda dare ya tsala Azeema bata dawo ba,haka inna ramatu tazo kansa tanata jaraba wai Azeema bata dawo ba,tatafi gantali kuma wai nan matar aurece,hartana cewa bataga amfanin wannan Auren ba,shisshigi ba kwarjini,sai Tusa kai suke ana gwasalesu,shidai yana jinta kanzil baicemata ba,saboda yana da tabbacin Azeema na gidan goggo kuma yasan darene yayi Suwaibar tahanata dawowa,juyamata baya yayi dole datagaji ta hakura tayi Shuru Tunda bai Tankata ba.

     **************

Da Asuba bayan Aliyu yadawo daga sallar Asuba ya shiga wajen goggo yana fadamata yasamu kiran gaggawa daga bariki General ne ke nemansa da kansa,sabods haka zai zo yakoma ammh yafadamata bazai dadeba wannan karan zai dawo,fatan alheri tayimai kafin Surabu agurguje yagama Shirin saboda sauri ko karyawa baiyi ba,ya dauki hanyar kaduna,har yatafi Azeema bata sani ba,don bayan ta idar da sallar asuba takoma ta kwanta Shikenan sai barci ya kwasheta bata farkaba sai wajen Takwas saura,nan ta farka tana salati ta mike ta fito falo nan ta tarar da goggo na sharan capet din dake falon,saurin karisawa tayi ta karba tana Fadin”Haba goggo gani cikin gida saiki hau shara da kanki..”Sakarmata tsintsiyan tayi tana fadin”Na kyaleki kiyi barcinki ne,nima Fitan gadanga ne yasa nafara sharan..”Da kallo Azeema tabi goggo dashi sai ta samu kanta ta tambayan “Ina yaje Goggo..? Goggo tace”Eh ya koma kaduna wai yaasamu kiran gaggawa,yanzu bai dade da tafiya ba..”Shuru Azeema tayi taciga ba da sharanta bayan ta gama tayi mooping din dakunan duka,tana gamawa goggo tasa ta shiga wanka bayan Ta fito suka karya,lokacin har goma ta wuce,tarasa mkranta yau sai dai gobe in Allah yakaimu,Bayan sungama komai Goggo tasa hijabi ta rufo gidan suka nufi gidansu Azeema.

  Inna na madafi taji sallamar goggo Fitowa tayi tana binsu da wani kallo daga ita har azeemar”Karkace kai goggo tayi tana fadin”Mun tashi lafiya Ramatu..”Dakyar Inna ta amsa da cewa!Lafiya..’daga haka tajuya takoma ciki goggo bata damu ba tace”Ga Azeema jiya wajena ta kwana dare yayi na hanata dawowa,ina mallam din yana ciKi..”? Mallam lawal daya fito daga bayi yace”Ina nan Suwaiba ina makewayi ne,naji shigowarki sannu da zuwa..”Goggo ta amsa “Da yauwa mallam,dama Azeema na rako jiya tayi dare sai ta kwana wajena..”Dan dariya Mallam yayi kafin yace”Toh inbanda Abinki suwaiba ai Azeema takuce gabadaya koma komawata tayi wajenki gabadaya ai babu matsala..”Gyada kai goggo tayi kafin tace”Hakane…”Azeema ce ta duka tana gaida Mallam lawal ya karba yana tambayanta yatakwana,ta amsa da lafiya kalau,tashi tayi ta shiga dakinsu nan ta iske Azeeza tatafi mkranta tayi mamaki sosai saboda sam Azeeza bata son mkranta,goggo ko daganan tayima mallam lawal sallama takoma gida,inna ko ko tak batace ba,kamar mai ciwon baki har mallam lawal ya Shirya ya fice batacema Azeema komai ba,kawai tana kallonta ne tana Tunanin yadda zata chanzamata kammani cikin hanya mafi sauki,sai kawai ta yanke shawaran tayi bakan sai ankwana biyu sai ta dauki matakin da zata dauka.

________________

  *Masauratar Garin  Agadez*

  “”Wai babana meke damunka ne,kaki bari Asaka malamai cikin wannan laluran taka,suzo kayi musu bayanin yadda kake gani amafarki kila in andace su gane me hakan ke nufi ammh sam kaki kuma GIMBIYA RAZEENAH Tafadamin baka bar mafarkan ba yanzu ma kamar yafi nada..”Takarishe cikin nuna Abun ya dameta.

Jin Abunda Ummah mai babban daki tafadane da sunan data ambata yasa dagowa yana zabgama gimbiya Razeenah harara,itako ta kauda kai ko ajikinta,yana zaune kusa da kafafunta itakuma tana zaune kan wata kujera mai kyau da tsari irin na gidan Saurata su duka biyun suna sanyene da alkaybbu masu kyau da tsari,Kasan kuma wani capet ne daya malale dakin kowani lungu kuma dauke da Tuntu irin na gidan Sarauta,agabansu kuma shake da wani kayatattacen Faranti dauke da kayan Ruwa ma”ana Fruit.

  Kallonta yayi yana Fadin”Kibamu waje zanyi mgana wa Ummata..”Yafada kai tsaye mikewa tayi kafin tace”,Afito lafiya Ranka ya dade..”,Ta fada tana gyara zaman alkyabban jikinta kafin ta fice,yana binta da harara lokaci daya ya dawo da kallonsa kan Ummah kafin yace”Don Allah Ummah kedaina daukan mganganun yaran chan akaina,ni basan ciwon kaina bane? kokuwa Sinfini sanin mezanyi ne,kuma mganar mafarki ko na malamai don Allah Ummah kibar mganar nan,bafa Abunda yagagari Allah koma miye insha Allahu inaji ajikina yakusa bayyana..”Yafada yana jinjinamata kai,Rausayar dakai tayi xatayi mgana yayi Saurin cewa”Don Allah kibar mganar nan Ummah,kuma kidaina basu Fuska in suka kawo miki ita,duk wacce acikinsu nake takuramawa in tana barci to ki fadamusu kada wacce takara bina Sashena don ba gayyatarsu nayi ba,bankuma ce Dole azo ba Atoh..”Yafada da alamar ya fara hasala

Jinjina kai Ummah mai babban Daki tayi kafin tace”To ai Shikenan duk basai takai ga haka ba,Allah ya bayyanamana koma miye..”Da Amin ya amsa kafin ya mike yana fadin”Zani Fada Ummah yau sarkin garin Dossso zai kawomin ziyara zamu tattauna wata mgana ne nidashi..”gyada kai Ummah tayi kafin tace”Toh Allah ya taimake ka Allah tsone idon makiya akanka babana..”Da Amin yayi ta karbawa Kafin ya fice daga makeken falo,yana Fitowa dogarai na kofar Shigowa suka yimasa rumfa suna masa barka da Fitowa,basu barshi kowa ya gansa ba, suka Rufesa da riganansu har ya shige fada ya zauna,kafin afara gabatar da Abubuwan mulki kamar yadda aka saba akowacce safiya.

    ………………………………

_Gombe_

  Bayan Sati  daya da Faruwan Abunda ya faru,Yau din takama Asabar ne,Tun safe Azeema tatashi da wanki danata dana babanta sai na inna Ramatu,wannan karon kam bata dauko na Azeeza ba,domin har aranta ta gane Raini ne kawai ke karuwa matukar tana cigaba da bautama Azeeza,Sai da tagama wankin Tas tana shanya Azeeza da tashinta kenan daga barci ta fito tana mutsika ido ko sallah batayi ba,taga Azeema tacika igiyoyi da shanya ammh kaf babu kayanta daki takoma taduba ma”adanar kayanta taga ko kala daya Azeemar bata dauka ba,Afusace ta fito daga dakin tana fadin”Wai ke Adda Azeema kwanan nan mekike Nufi dani ne..”?tafada bayan ta tsayamata agaba kerere,kuma duka hannuwanta takama kugu dasu,ko kallonta Azeema batayi ba,saima tacigaba da shanyarta,Ganin haka yasa Azeeza ta fusata Tanufi kayan da Azeemar ke shanyawa duk ta rikito dasu kasa kuma tasa kafa tataka tana fadin”Kinajina ina miki mgana kina min banza,yanzu ai ina fatan kin jini ko,sai na kara fatali da sauran ne..”Tafda tana wani mata banzan kallo,Azeema dake bin kafan Azeeza da kallo daga sama har kasa taga yadda tayimata da kaya,Ranta in yayi Dubu ya baci ashe haka Azeeza ta rainata bata sani ba,bata gama mamaki ba Azeeza ta sanya kafa tayi Fatali da sauran kayan dake botiki daya rage bata shanya ba,Tana fadin”An kara zubarwa sai ki…”Ji kake Tas!Tas!Azeema tadake tsaye ta zabgama Azeema marika masu lafiya dama da Hauni,wanda saida Azeezan Ta wuntsila bakinta ya fashe da hanci Dago kanta tayi bakinta bude tana kallon yadda Azeema ke huci saboda bacin rai cikin kakkusan murya tace”Ni sa”arki ce Azeeza,ashekarun haihuwa nawa na baki? kodon kinga ina kyaleki bana tanka miki to ba tsoro bane wlh gudun mgana ne,ammh Tunda nagane baki da mutumci ballatana kunya yanzu mukafara dani dake acikin gidan nan..”Tafada kafin taDuka tana kwashe kayanta Ranta bace kamar tayi kwallah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button