ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

  Yar dariya Jabir yayi kafin yace”Ba laifina bane Captain,banbin ka bashi ammh akwai mai binka..”Yafada yana shafa sajen Fuskarsa,Shekeke Aliyu ya kallesa kafin yace”Toh waye..? Jabir yayi Saurin matsawa baya sai ga Ni”ima ta bayyana tana sanye da Doguwar riga Baka kirar Armani,tayane kanta da bakin mayafi,kafarta sanye da wani black halfcover,mai kyau da tsari,sai wata karamar jaka,da wayarta dake hannunta,Sake baki Aliyu yayi yana bin Ni”ima da kallo daga sama har kasa,itako Tunda ya fito take kallonsa gabadaya wani soyayyarshi data binne lungu da sako Ya tasomata lokaci daya hawaye suka cikamata ido saboda tsausayin kanta.

 Rausayar dakai Jabir yayi kafin yace”Toh na fita ko? Kai mallam ka bata hanya Ta shiga ciki takanas daga gombe take saboda kai,ko bakomai ka girmama bakonka..”Jabir na fadin haka ya wuce ya barsu nan,Ni’ima dake tsaye batayi gaba batayi baya ba,kallonsa kawai take hawaye suka gangaromata baki na Rawa ta Furta..”Soja..Nah…”,Tafada cikin muryan kuka kafin tatafi da gudu ta fada jikinsa sai kuma ta saki kukan lokaci daya,Ajiyar zuciya Captain ya sauke kafin yayi baya bayan ya sanya kafa ya Rufe kofar takoma Tarufe kanta,hannu ya sanya yana buga bayan Ni”ima lallashi itako Fadi take”Why my Captain? why..? .meyasa zaka barni alokacin danake tsananin bukatarka da burin na sameka? wlh koda da darana daya bantaba samun kwanciyar hankali da barci mai dadi ba Tunda na Rasaka don Allah Sojana kada ka sake gujemin wlh bazan iya Rayuwa baka ba,nasha wahala kafin na sameka…”,Tafada tana kara kamkameshi,tanasakin wani marayan kuka.

  Bambareta yayi daga jikinsa ya isa da ita kan daya daga cikin kujerun Falon ya zaunar da ita,Kichen Ya nufa yaje ya daukomata Ruwa da wani karaminn kofi ya Tsiyayamata mikamata yayi yana kallon kwanyan Idonta,Amsa tayi kafin ta sanya hannu ta share hawayenta,dan kurba tayi kadan kafin ta mikamai,kan Center table din dake Falon ya ijiye kofin kafin ya koma kujeran dake kallon nata ya zauna bayan Ya Dora kafa daya kan Daya yana Fuskarta dago da kanta tayi Tana kallonsa Shiko Remot ya dauka yana sarrafa talabijin din dake Falon.

   “Soja…Nah….”Tafada cikin Rawan murya Dagowa yayi zata kara mgana yayi Saurin dagamata hannu yana fadin”,Kinga nifa bani zakizo kina ma kuka ba,babanki zaki tasa kikatayima Kuka domin shi yasaka alkamashi ya datse halakan dake tsakani na dake…”Ya fada idonsa akanta Raurau tayi da ido kafin tace”, i know buh…”Dagamata hannu yayi kafin ya mike yana fadin”,Ki Adana kalamanki Ni”ima domin basu da muhalli awajena,Ba shakka ada na soki,na kuma so muyi,zama na har abada dake,sai dai kash Tun Ranar da mahaifinki ya watsamin kasa a ido naji kin Fita Raina,ko koda ace banyi Aure ba bazan Taba iya Aurenki ba,…”Yafada kai tsaye 

  Azabure ta mike hannunta dafe bisa kirji tace”,Kana nufin kayi Aure ne my Captain..? Takowa yayi zuwa gabanta kafin ya sanya duka hanuwansa cikin aljihun wandonsa yana fadin”Kwarai ma kuwa ai wajen da mahaifinki yace bazai bani Aurenki ba saboda Bani da uba awajen wani Uban ya wanke yarsa ya bani,kinga ko iya karamci da hallacin yayimin,kuma koda ma ba”ayi haka ba,ni Aliyu bani da burin zama da mace Fiye da daya..So Abunda nakeson fadamiki gwara Tun Wuri kiyi Facing Realiaty Ki cireni Aranki don bazaki taba samuna ba,shawara ta karshe don Allah kada ki kara zuwa gida,ina da mutumci a idon jama”a bana Fatan ki Fusatani har na zubda wannan mutumci…’,Daga haka ya juya zai Shige bedroom dinsa har ya kusa shiga ya waigo yana fadin”Armmm..In kin Fita plz close d door…”,Yana fadin haka ya Shige bedroom ya banko kofa Ransa bace,kawai daurewa yake shiyasa bai Mazgeta ba,ammh azahirin gaskiya haushinta yake daga ita har Dan sandan Ubanta.

Ni”ima ko Durkushewa tayi ta fashe da kuka,kamar zata Shide,Rike kanta tayi tana girgizawa tadade tana durkushe kafin tatashi ta fice daga gidan,Direba ya kawota Jabir na gaban gidansa yana jugging ya hangi Fitowar Ni”,ima Tana kuka Dan mirmshi yayi kafin yace”i know haka zai Faru dama gaskiyan nake so ki sani asauka lafiya..,”Yafada yana dan Dariya,mota ta Shige ta Umarci Direba ya taka mota suje don yadda take jin zuciyarta kamar zata Fashe saboda kunci.

     _________________

 _Gombe_

   Yau kimanin Sati daya kenan da komawar Azeema gidan goggo,Duk wani jin dadi da Kulawa goggo na bata,domin koda ta daukota daga gidansu Kai tsaye shashen Aliyu ta budemata tace mata nan ne dakinki Azeema,ki zauna kijira mijinki har ya dawo..Toh ya Azeema zatayi bata da yadda zatayi sai bin Umarni,Goggo da kanta ta zage suka gyara shashen suka tsabtaceshi,Washegari kuwa Goggo da kanta tadauki Azeema sukaitai kasuwa tayimata siyayyah kaya da Atamfofi da Dogayen Riguna harda masu sikat,sai kayan kwalliya da takamla duk wani Abun gayu dai na mata ta siyamata domin goggo kudi har bata sanin ina zata kaisu,in kawu yazo ya bata,hakama Aliyu,kullum Tarasu take saboda babu Abunda take siya komai na more Rayuwa sun siyamata shi ta mallakeshi,harta ta wajen gyaran kai Sai da goggo takai Azeema aka gyaramata kai aka wankeshi sosai,Ita kanta Azeema tayi Farinciki da Shigarta sabuwar rayuwa,haka Baba Ade tazo tayitama Goggo godiya harda kwallah saboda murnan chanjin Rayuwa da Azeema ta samu kamar yadda Mallam lawal Shima dauke Azeema daga gidan Yafi komai yimai Dadi.

   Goggo batai kasa agwiwa ba,harta girki tazage tana koyama Azeema dawasu kissa,da dubarun yadda zaka jawo hankalin Namiji gareta,kullum bata lbrai take,tare da kawomata kissa kala kala na yadda kishi mai tsafta ya gudana agidan Annabin Rahama Muhammed Sallallahu alaihi wasallam,Tare da kissosin matan sahabbai,ba shakka Azeema na dauka shawarwarin goggo sosai don tana jin dadin xama da ita,Cikin Sati daya Azeema ta chanza kamar ba ita ba, Tuni wa”innan kuraje suka kama kansu dama wahalace ta kawosu,Tayi dan yi kiba taciko uwa uba ga chanjin abinci dana Sutura,Kullum a Sashen gadanga take kwana,ammh adayan bedroom din dake kusa danashi,wanda yake akulle Tana Tunanin makullin dakin yana hannun mai Shi ne,Watarana adakin zasu wuni da goggo watarana kuma A shashen goggo,Tunda Abun ya faru Azeema bata taka gidansu ba,kai ko Fita in ba kasuwar da sukaje da goggo ba,bata taka ko”ina ba,Babanta Kadai suke haduwa dashi in ya fito da safe zai Tafi kasuwa don yanzu yakoma cikin kasuwa da sana”arsa Ssnadin gadanga don shi ya siyamai shago ya koma chan,yanzu hankali mallam lawal akwance yake,Domin Ramatu dai bata da wanda zatayi Fitina dashi Azeema ce kuma ta barmata gidan,daga ita sai yarta suci wainarsu babu babbaka.

Azeeza kuwa Duk iya tsawon kwanakin bata taba Sarara ma kanta da Tunanin mafita ba,tabuga ta buga ammh tagagara samun wata hanyar da zata cima nasara Adaren lahadi zuciyarta tagama yanke shawaran data ke ganin tabbas ita tafi dacewa kafin tafara zartar da komai,so take ta Fara lalata Auren Azeema Tukunnah ta yadda babu wanda zai zargeta da aikata hakan.

  *Monday*

 Monday Tushen Aiki ko bature na tsoron zuwanki,Yau Su goggo su dan makara tashi,kuma yau din ne Azeema zata koma mkranta,koda ta Shirya har 7:30am ta wuce Shiyasa kawai ta dauki jakarta tana cema goggo ta wuce,fada goggo tafara yi tana fadin ya zata tafi bata karya ba,maza ta tsaya ko Ruwan Shayi ta sha,Tura baki Azeema keyi tana fadin”Allah goggo na makara..”Fifitamata shayin goggo keyi Tanafadin”To sai me,yanzu zaki isa ni zan Rakaki har mkrantan in Tsoron duka kikeyi bamai tabaki kina matar soja..’Yar dariya Azeema tayi kafin tayi mgana Sukaji sallama suka karba atare,Daga labulen dakin akayi Azeeza ta bayyana itama jikinta sanye da kayan mkranta ga jakarta ahannu,daga Azeema har goggo da kallon mamaki suka bita,itako sunkuyar dakai tayi kafin tasaka gwiwowinta akasa Tana fadin”Don Allah Adda Azeema kiyi hakuri ki yafemin Duk Abunda nayi miki,wlh Sharrin shedan ne,Ke yar”uwatace danafi so fiye da komai Arayuwata duk inna ce,take zugani ina miki Rashin kunya,ammh bada son Raina bane,ammh yanzu na Tuba,wlh bazan kara jin zugan inna ba,don Allah kiyafemin…”,Tafada tana fashewa da kuka,Kallon Goggo Azeema tayi itakuma ta gyada mata kai,da hanzari ta isa ga Azeeza ta dagota ta Rumgumeta tana fadin”Shiiii..Kidaina kuka Azeeza na yafemiki dama bantaba rikeki Araina ba,Na yadda shedan ne yakeso ya raba tsakaninmu..Bakomai Allah yayafemana gabadaya..”Lamo Azeeza tayi tana wani dan mirmishi kafin ta dago tana fadin”Duk inna…”Shiiii…Kiyu Shuru hakanan ma,karki manta inna fa mahaifiyarkice fata kawai zakimata Allah yasa ta gane itama..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button