ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

Itako Azeema mamakin Azeeza ne ya cikata,ita yaushe take cewa su hau mashin sau biyu fa suka taba hawa,yau din ma babu abun hawa ne,wannan din ma dakyar suka samu Shiyasa suka hau su biyu,ammh ji Abunda take fada,bata samu zarafin mgana saboda yadda gadanga ke hararanta yana jifanta wani dirty look,itako Azeeza bayan Azeema takoma tana leke Farinciki Duk ya cikata burinta daya yanzu Shine Ya kifkifama Azeemar mari.

    *Comment share,vote…*

    *Janafty…*

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*I Dedicated dis page to u guyzs KHADIJA CANDY NOVELS..(mama)❤,BENEFICIAL WRITERS????,JANAF NOVELLA ????1and2,ALIYU GADANGA FANS 1,2,3 and REAL LADINGO FANS???? Tanque all For u Hot comments Sakallahu Filjannah HABIBATIES*????

       *Chapter 14*

  Yana karisawa kusa da mai mashin din ya dunkule hannu ya tokare mai hanci da baki lokaci daya yasaka hannu ya matsemai baki,jinin daya Fito daga bakinsa da hancinsa sai da ya sashi ya hadiye kafin ya sakeshi,baya yayi kamar zai Fadi saboda yadda yaji kansa yayi Aliyu yasaka hannu ya taroshi yana fadin”mekace ne dazu? dan maimaitamin banji dakyau ba…”Yafada yana kallonsa,mai mashin daya sha wuya yakalli Fuskar gadanga zuwa hannunsa yaga yadda Naman jikinsa ke jida saboda Fushi ai bakinsa na Rawa yace”ban..bance komai ba yallabai..”Wani killer smile Aliyu yayi kafin yace,”Next time kakara dauko mace daya ma,ba biyu ba zaka ga yadda zanyi dakai..”mai mashin yace”Bama zan kara dauka ba yallabai wlh maza kawai zan koma dauka..”good..”inji Aliyu kafin yajuya yana Fadin”oya Sauka daga kan mashin dinka ka dauketa bisa kanka karka sauke har saika bar layin nan..”Sororo mai mashin yayi Tsawa ya dakamai ai da gudun hanzari ya daga mashin din da hannu bibbiyu ya wuce yana waige Jabir dake gefe yana waya Tikar dariya kawai yake,yana ba budurwan Nasa lbrin Abunda ke faruwa,su ko su Azeema Tuni suka Shige gidan goggo suna Rawan jiki,Da goggo ta tambayesu Azeema kasa mgana Tayi Azeeza ce ta maida bayani Yadda akayi Dariya goggo tayi tana fadin”Banda Abun gadanga miye na Sauke Fushin kan mai mashin,..”Abun yaba Azeeza mamaki yadda lbrin yaba goggo Nishadi,suna cikin maida mganar ne sai gadanga ya shigo yana Shigowa kai tsaye Azeema ya nufa sai da yazo gabanta kafin yace”Ke…”Dago kanta tayi kafin tayi Saurin sadda kai,Nunata yayi dayatsa yana fadin”ke babban banza ce ashe bansani ba,..To dis one wil be d last time dazanganki bisa mashin din wani kato,daga yau ki dinga hawan Keken Napep tunda na lura sakarcin naki gaba yake ba baya ba..”Yafada kafin ya juya,Galala goggo tayi tana kallonsa itako Azeeza kamar ta kurma ihu saboda murna baki goggo ta rike kafin tace”toh wayace maka Azeema na hawa mashin,Toh na tabbata rashin Abun hawa ne,bata da zabi ammh Azeema bata hawa mashi yo Allah na tuba inamatake zuwa balle ta dinga hawa mashin…”Cak ya tsaya kafin ya waigo yana kallon Azeema yadda take kuka hawayenta na diga Tsausayinta ya kamashi maida kallonsa yayi kan Azeeza nan da nan Tayi wiki wiki da ido tsuramata ido yayi yana nazarinta,itako Tuni jikinta yahau mazari Abunka ga mara gaskiya,takowa yayi zuwa gabanta yana karemata kallo kafin yace”Ke…”Dago kanta tayi tana wani kifta ido matse goshi yayi kafin yace”Ni sa”an wasanki ne.. ? Shuru tayi tana Raba ido tsawa ya dakamata kafin yace”Nace  ni sa”an wasanki ne..? da sauri Azeeza ta girgiza kai tana ja da baya,Wani tsawan ya dakamata kafin yace”Oya get out..Wannan yarinya wlh idonta na kama dana mayu,”Yafada yana kallon goggo ai da hanzari Azeeza ta fice ko waigo dariya takama goggo sai da dara gimtse Fuska Aliyu yayi kafin yace”Wai don Allah goggo meyasa kika sakarma wannan yarinyar Fuska ne,nifa banyarda da ita ba sam,idonta namin kama da na munafukai ne wlh..”Rausayar dakai Goggo tayi kafin tace”Toh mai gani hanji kai kowa bai maka ba,toh ko dole ka sota Tunda kana Auren yayarta..”baiyi mgana ba kawai ya fice cike da takaichin yadda goggo takasa Fahimtarsa sai yana ji ajkinsa tamkar yarinyar Tafi Azeema iya Duniyanci da wayau bayaso wani Abu yafaru agaba…

  Goggo ita tayita lallashin Azeema har tayi Shuru ammh takasa daina jin Haushin kanta da mamakin Azeeza,itako Azeeza kwana tayi takaichi da bakinciki domin yaya captain yazo ya Rusata mata komai ammh ba komai yanzu tasaka kafa babu gudu babu ja da baya,bayan mangariba Jabir ya shirya Shida gadanga suka wuce Gra domin haduwa da budurwan ta jabir wacce suka hadu ta waya,ba laifi yarinyar tana da hankali da kunya babanta dan kasuwa ne,yarinyace bazata wuce sa”an Azeemar ba itama SS2 take a babban sakandiri Abun na jabir yaba Aliyu mamaki yadda yaga yana wani Rawan kafa agaban yarinya saboda Haushi mota yakoma yana game awaya Don yaga lalacewar na Jabir yayi yawa.

..

  Sai pas ten suka dawo,koda suka dawo Goggo da diyarta tuni sun dade da kulle shashensu Sun kwanta suma basu bi ta kansu ba Aliyu ya kargame kofar gida suka fada shashenshi domin kwanciya,Abunda yabama Aliyu mamaki Jabir suna shirin kwanciya ya dasa waya da yarinyarnan kamar wani namamajo Ko gajiya basuyi Haushi yakama Aliyu ya fice daga dakin ya Shiga dayan bedroom din ya kwanta,nan yaga kayan Azeema da kayan kwalliyarta wadanda goggo ta siyamata,tsayawa yayi yana kallon kayan yana wani Tunanin yama Rasa ta ina xai Fara Taimakama rayuwar yarinyar don ya lura tana bukatar wani akusa da ita,Bata da sakewa ko kadan,bata da sani kan komai,shibaima san meke damunta ba,kullum kai asunkuye ko kuma ka ganta tana kuka,ada yana tsausayama kansa na Rashin cikakken Asali ammh yanzu yafi tsausayama Azeema Domin ita tana da uban ammh maraici da rayuwar Rashin yanci ya dabaibaye Rayuwarta uwa uba bata taso tare da kowa ba,Shiyasa wautarta tayi yawa,kwana yayi yana Tunanin mafita da yadda zai bulloma al”amarin.

    ***************

Washegari da Safe da wuri Azeema ta Shirya domin wucewa mkranta Bayan ta karya ta zauna tai zuru tana jiran ko Azeeza zata biyo mata su Tafi ammh Shuru goggo na lura da ita bata dai mata mgana bane ta tsayane taga iya Gudun Ruwanta zata fasa zuwa mkrantan ne saboda Azeeza bata biyomata ba ko yaya ne? Tana nan zaune Aliyu yayi sallama ya Shigo dakin goggo jallabiya Mai Ruwan Tokace ajikinsa,Tanajin sallamasa tayu zumbur ta mike tana mazurai Sau daya ya kalleta yakauda kai kusa da goggo ya isa yazauna ya gaisheta amsawa yayi yana Riko hannunta Da hanzari Azeema ta duka tana gaisheshi a dakile ya amsa kafin ya kalleta yace”Goggo metake jira bata tafi mkranta ba 7:30 fa ya wuce..”Kallonta goggo tayi kafin tace”Yauwa gwanda da Allah ya kawo ka gatanan,tambayeta nima Tundazu naga ta Shirya ammh ta nemi waje ta zauna bansan metake jira ba..”Sunkuyar dakai Azeema tayi Aliyu zai yi mgana kenan Jabir ya Shigo dakin Shima yana Sanye da jallabiya baka yana ganin Azeema ya washe baki yana Fadin”Ah ZEEMA kin tashi lafiya..”Dan Rankwafawa tayi tana gaisheshi Ansawa yayi cikin sakin Fuska yana fadin”Lafiya lau Zeema ya mkranta hop dai ana maida hankali..”Gyada kai tayi cikin kunya Gadanga dake zaune yayi Wuf ya mike yana fadin”Ke muje..”fuska ba walwala kallonsa jabir yayi kafin yace,”Toh miye nawani cewa kuje naganeka bakin ciki kake don ta dan Rankwafa dazata gaidani ko? hararansa Aliyu yayi kafin yace”Eh..”Adakile Akarkace Jabir ke kallonsa kafin yace”Dalili..? ko kallonsa Aliyu bai yi ba yabi bayan Azeema data fice da Sauri har zai Fice ta waigo yana fadin”kaji dan Rainin wayau ni dana rakaka zence jiya Budurwanka tama gaisheni ne,kunata rawan kafa ko Tunawa dani ai bakayi ba..”Yafada yana dariyan keta kafin ya fice Baki Jabir yakama lokaci daya yana Sosa kai goggo dake zaune gefe tace”Au zence kukaje jiya ko? to ai Allah yakamaku ja”irai..”tafada Tana dariya Sosa kai kawai jabir yake kafin yayi Wuf yafice yana fadin”Goggo ma gaisa da Rana.”Yar dariya goggo ta sakeyi kafin tace”kai Jabiru da gadanga bansan wanda yafi wani Shegantakaba..”Take fada kan tatashi ta fada kichen domin ta kwaso musu Abun karinsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button