ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

 Azeeza wajen Goggo Ta nufa itama ta duka tana rokonta dagota goggo tayi tana fadin”Dukkanku ya”yana ne,babu wanda na ware acikinku,Allah ya hada kanku..”Suka amsa da Amin nan fa su Azeeza aka share kafa akayi kari mai lafiya kafin goggo ta rakasu zuwa bakin Titi su hau Daidaita Dari biyar Goggo taba Azeema tace suyi kudin Abun haawa zuwa da dawowa sauran kuma suyi kudin Tara dashi,murna sosai sukayi suna ta mata godiya har suka kulema ganinta tana Faman daga musu hannu,acikin keken napep din ma sai Hira Azeeza kema Azeema itako dayake bata da yawan mgana mirmishi kawai take mata sai ko eh ko A”a..Azeeza bata damu ba,dama komai sai Abun Ahankali juyawa tayi tana kallon gefen Hanya kafin tayi wani bazawarin mirmishi tace” Dis is juz d begining..Yanzu wasan ya fara Adda Azeema kinyi kuskure babba wajen yarda dani ganinan zuwa cikin Rayuwarki domin na wargazata…”,Tafada tana cije baki har saida Taji zafi alebenta.

  

       *Comment,share,and vote…*

       *Janafty…,*

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

*I dash d whole page for u my Rival..????…HUWAILATU????????popular Name MISS ZERK..ga page dinki nan,karki wani damu Ana tare,dama aie Abun Uwargida na Amarsu ne…..*????????

            *Chapter 13*

    

    ———————Rayuwa Tana ta gudu kamar yadda muke cinye Lokaciinmu da kwanakinmu Aduniya,suke gangara suna Neman karewa,masu imani ne da masu tunawa da zasu mutu kadai suke Shiga Tashin hankali in suka Tuna hakan,ammh akasin haka ko ajikinsu To hakan ce Tafaru da Azeeza Domin koda da wayewar gari, bata taba Nadamar ko jin Abunda take Shirin Aikatawa baida kyau ba,ko taji zuciyarta ba dadi in Tayi Tuni da Cewa Azeema yar”uwanta ce.

  Duk wata hanya da Azeeza zatabi ta Shigema Azeema da goggo tayi,yanzu sun bata dukkan Amanna,gidan take Wuni,sai dare take komawa gida,tare suke komai da Azeema kamar wasu yan biyu,inna Ramatu kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu,Saboda sabbin halin Azeeza tafito dashi shiko Mallam lawal Abun yayi Mai dadi don Azeeza tazo ta rokeshi gafara kuma ya yafemata Yana ta sakamata albarka,Inna Ramatu Abun ya Daure mata kai sosai kuma tayi tambayan Duniyan nan Azeeza tayi mata banza bata mata wani bayani ba,kuma bata yarda ta fadamata Abun da ke Ranta ba ko alama daga ita sai Allah kadai suka san Abunda ta binne Aranta.

  Duk Zuwan da Azeeza take gidan goggo bata taba katarin,ganin Azeema Shashen na yaya captain ba,wanda Abunda take ta jira kenan,kullum sai dai su Tare dakin goggo susha hiransu,yau dai kam Tayi sa”a domin tana Rafka sallama atsakar gidan Azeema ta daga labulen Shashen gadanga tana fadin”Azeeza Shigo nan..”Tafada kai tsaye tana mata mirmishi Ran Azeeza yayi sanyi jikinta na Rawa ta nufi Dakin Tana washe baki,bude mata kofar Azeema tayi tana fadin”Yau goggo barci ke cinta,Har na dawo,bata sani ba shiyasa na Shigo nan don kar na dameta..”Dariyan yake Azeeza tayi tana fadin,”eh gaskiya ne…”Tafada tana bin makeken falon da kallo,wanda yaji lafiyayyun Royal chair,idonta wurgawa kawai yake tana karema Falon kallo,Azeema ce ta Kalleta tace”Zauna Azeeza bari na kawo miki Ruwa kinci Abinci? tatambayeta girgizamata kai Azeeza tayi ta kasa mgana saboda wani hoton gadanga data gani bisa wani tebur din glass,dake chan jikin bango,kyam tayi ma hoton tana kallo,itako Azeema bata lura ba kichen Ta nufa tana Fadin”Bari na dafa miki indomie..Nima ita nagama ci yanzu..”ko jinta Azeeza batayi ba hankalinta yatafi ga hoton Yaya captain,A hoton yana sanye da wasu fararen kayan hatta cambos dinsa fari ne, safa ma haka,acikin wani fili ne akayi hoton kamar dai asansanin horarwa ce,yayi tsalle yana dariya aka dauki hoton,Azeeza saboda shauki batasan sadda ta karisa kusa da hoton ba ta saka hannu ta dauki Frem din tana kallo,hannunta ta sanya tana shafa hoton sai ga Azeema ta fito tana fadin”Yanzu zata nuna na zuba miki,yunwa ba dadi..’Tafada tana karisawa kusa da ita.

Saurin waskewa Azeeza tayi tana fadin”kinga hoton danazo kallo Adda Azeema Allah yaya captain yayi kyau sosai ahoton nan..”Mirmishi Azeema tayi kafin ta amshi hoton tana fadin”Gaskiya yayi kyau kam..”Tafada itama tana kallon hoton kafin ta ijiyeshi inda yake,Talabijin din dake dakin ta kunna tana fadin”Muyi kallo Azeeza mu rage zaman Shuru..”Yake Azeeza tayi kafin tataho ta zauna tana satar kallon bedrooms din dake jere Shuru ya biyo baya Azeema ita hankalinta na wajen kallo yayinda Azeeza ke saka yadda zata fara dakan Ruwan Cikin Azeemar batare data sani ba.

  Zuwa chan wata dabara ya taso mata sai tayi Farat tace”Adda Azeema nace ba..”,Dagowa Azeema tayi kafin tace”mekike son Fadane Azeeza..? Yar dariya Azeeza tayi kafin tace”Wai nace yaushe yaya captain zai dawo ne..? Kai tsaye Azeema tace”Wlh bansani ba Azeeza..”,Wani sanyi ya Shiga zuciyar Azeeza murna ya cikata sai ta barsa,lokaci daya ta bata rai Tana fadin”Toh meyasa Adda? bakwa waya ne..”?Jin Abunda Azeeza tacene ya sata Dagota kanta tama Azeeza kuri da ido,sai taji kunyan cewa basa waya..Cikin in ina tace”Eh..Armm..Munayi mana..’Tafada kafin tayi zaraf ta mike tana fadin”Bari na dubo miki,kila yanzu Ta isa yi..”Tafada kafin ta fada kichen,Tana Shiga Azeeza ta buga kafa tana fadin”yes…Komai na tafiya kan Tsari..”Take fada tana dariya Sai ga Azeema ta fito dauke da filet wanda ta zubo indomie aciki sai Lemon cway data daukomata ta kawomata nan Azeeza Ta share kafa ta warba tana ma Azeema hira wanda Rabin hira duk na dakan Ruwan cikinta ne,itako Azeema bata ma iya maida mata amsa sai dai tayi mirmishi ko ta gyada kai,wai Azeeza harda tambayanta ya lbrin Ni”ima Saboda mamaki sai da Ta bude baki tana kallonta,harda cemata wai ta mike tsaye don tagane yaya captain haryanzu yana Son Ni”imar,Rike baki Azeema tayi tana auna kankantar shekarun Azeeza ammh tana mganar manya,sai kuma mganar data Fada ta tsaya mata arai…Sam bataji dadin Jin Abunda Azeezar ta fada akan Yaya captain yana Son Ni”ima haryanzu ba, Batasan dalili ba,sai taji duk zuciyarta babu dadi..Lura da haka da Azeeza tayi sai tayimata sallama takoma gida ammh Ranta Fes Domin tayi hakane ta tusama Azeema tsanar yaya captain koma tana Sonshi ta cire Tunda zuciyarsa na ga wata..Kuma taga alamun Nasara kodaga yadda Azeema tachanza Tun lokacin dataji mganar…

________________

  Ta Sauka daga keken napep kenan Tabashi kudinshi Ta nufo kofar gidan Kamar a Mafarki taga wani kamar gadanga zaune bisa bayan motarshi Jabir na tsaye agefe,dukkansu suna sanye da Riga da wando,wandon blue ne sai Rigar Farace kafafunsu sanye cikin booth,Kowannensu hannushi dauke da wani ubansu agogon Fata na kamfanin Rado,Fuskarsu cike da Annuri,Hannayensu dauke da gorunan Ruwa suna kurba,Da hanzari Goggo ta karisa Gadanga ne ya fara hangota da hanzari ya diro daga motar yana cema Jabir”Ga goggo chan ta dawo..”Yafada yana karisawa gareta,Maida kallonsa Jabir yayi inda goggo ke tahowa tana ta washe baki,dariya yayi yabi bayan Gadanga..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button