ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

Inna Ramatu ita tagasa Ma Azeza jiki tana gasata tana kukan zafi bayan tagama ta shafe mata jiki da Man zafi,hakama Sauran kawayenta,kowa yaji Captain ne,ko ya taso da zafi sai yakoma don ba”a ma Soja wargi,Ballema kowa yasan waye captain kaf,anguwan nan Ansan baya da wasa yaci kaniyarka bawani abu bane awajenka,Azeema ko cikin dakinsu tana kashin dariya domin Ranar tayau ta mata dadi,kota tafito Diban Ruwa tayi wanka daga Azeezar har Inna ba wanda ya Tankata haka ta shige bayi tana dariya,wani Farinciki na Fizganta bata san dalili ba,ammh ko Fuskar captain Tatuna sai taji wani Sanyi ya Shiga Ranta,ita kadai ta Furta. *YAYA CAPTAIN NAGODE*

_______________

Ranar da Aliyu ya taho Gombe Aranar Ni”ima ta dira akaduna,Taji matukar takaichi da Bakinciki lokacin da captain jabir ke fadamata Cewa Aliyu ya taho gida,kuma bayajin zai dawo cikin satin nan,sai sati na sama,Kuka wurjajan Ni”ima takema Jabir kan yabata nombar wayar da zata samu Aliyu,dariya jabir yayi mata yana fadin”Bayajin cewa Aliyu ya chanza layi buh Abu daya yasani cewa ya kulleki ne,da zata tafi yace”Shawara mai kyau karta kuskura taje gombe wajen Aliyu in ma zata dawo ne tabari ya dawo kaduna yayimata alqawarin fadamata,taji dadi sosai Kafin tatafi sai da sukayi exchanging din Phone number,Direbanta ne yakawota Domin karya tayima mami wai zata raka Muneera biki sai yammah zata dawo Shiyasa har ta dawo gida mami batasan ina taje ba.

   *************

  Bayan kwanaki da Faruwan Abun,Azeema tasamu sauki sosai ta bangaren inna da Azeezar ita kanta bamai Shiga harkanta,ko aiki bamai sakata,Ammh dayake Azeemar ta riga ta saba shiyasa bata iya zama,duk Abunda tasan aikinta ne tun safe zata tashi tayi Mganar aikenta kuwa ba”a kara yi ba tun Ranar da Captain yayi mgana in ka ganta waje toh Mkranta zata ko Allo,itako da Azeeza ko mgana bata mata,in tayimata ma bata karba mata shiyasa tafita harkanta,Dayake bata zuwa mkranta tana jinyan kanta saboda kugu ya rike????,Shikanshi mallam lawal yayi mamakin ganin chanji agidan,bai dai yi mgana bane,sai yaji dadi Aransa yana fatan ya sa Ramatun ta gyara halinta ne,itako Inna Ramatu mganar saceta a kaita barikin shine ke dagamata hankali,shiyasa ko taso yin wani Abu takejin Jikinta yayi sanyi,toh tafaa sani tsab Aliyu zai iya don ba mutumci ne da shi ba.

Goggo batasan wainar da”ake toyaba ,don yanzu bata cika ganin Azeemar ba,saboda dawowar captain sai dai da safe in zata mkranta kan yatashi take shigowa su gaisa da goggon ta wuce agurguje,Shiko Captain haryanzu goggo batamai mganar data kirasa akai ba,Shikuma bai mata mgana ba,yana jiran yaji mezatacemai,Shima yana Tunanin Dauke  Azeemar  daga wanchan Rayuwa zuwa wata rayuwar mai inganci.

**************

Yanasanya mota kenan Cikin garejin yana Sauri yasamu jam”in sallar isha”i yaji maganganu daga kofar gida,koda ya fito dayake akwai wuta,kuma haske ya wadata kofar gidan,Kallonsu yayi suna tsaye Azeeza takalli Azeema tace”Gaskiya Adda Azeema kidaina sakamin ido,ina Ruwanki dani,wato ke kinyi Aure,kina bakin ciki ni kar na tsaya na nemi nawa mijin,da anyi mgana sai kice,Baba yahana,don Allah kibarni naji dadin rayuwata..”tafada tana saka hannu ta ture Azeema dake tsaye sai da ta fadi,tsautsayi yasata tafadi ta gefen hannunta sai da yayi kara,dan Ihu Azeema tayi tana dafe hannun saboda azaba,Hawaye na shatata bisa kuncinta

  Kallonsu yake cike da mamaki,kamar ya basar ya wuce,sai kuma ya tsaya yana kallon Azeezar harta kariso kusa dashi bata lura dashi ba,sai da taji ya dakamata tsawa yana fadim'”U Stupit,Come here..”Yana fada yana gyara tsayuwarsa,ba Azeeza da”aka dakama tsawa ba,hatta Azeema dake gefe saida ta razana,jikin Azeeza na rawa ta kariso tana kallonsa kafin tace”Gani.. YAYA CAPTAIN..”Ko kallonta baiyi ba,sai ya juya kan Azeema yana fadi cikin tsawa..”Au ke bazaki zo ba,jira kike na kiraki ko?i swear in kika bari nazo na sameki sai kin zagaye anguwanan kina tsallen kwado,wawiya kawai..”Yafada yana hararanta,ai Tun kafin ya rufe baki,ta kariso gabanshi jikinta na kyarma,hawaye na zubomata,Azeeza kuwa kuramai ido tayi tanajin wani dadi kamar ta rumgumeshi,hartana wani lumshe ido saboda yadda Shaukin ke Fuzgarta

Kallon Azeema yayi kafin yace”In kika bari hawayen ki ya zuba akasa,wlh sai kin duka kin lasheshi tas..”yafada ba alamar wasa atare dashi,Azeema da hanzari,ta hadiye kukan nata,tana share hawayenta,tsawa ya dakamusu yana fadin”Daga ina kuke Don ubanku yanzu dadddaren nan?..”Azeema bakinta na rawa tace”,Da..daga Mkrantar Allo..”Sauke idonsa yayi kan Azeeza wacce tayi zurfin cikin Tunani,kuramata ido yayi yana ayyana girman Rashin kunyar yarinya,kara tamke fuska yayi kafin yace yana kallon Azeema”Waye ya girmi wani acikinku..? Da rinannun idanunta ta dago ta kalli Azeeza,wacce take wani mirmishi,Daka musu tsawa yayi yana fadin”Wai bada ku nake,mgana ba,ok so kuke yanzu jikinku yagayamuku inaga.”Yafada yana kokarim zare belt,da hanzari Azeema tace”Nice,na girmeta…”Wani banzan kallo yayi mata kan yace”oh kece babba ammh kina zaune,yar kanwarki na miki Raini,harda tureki,kekuma dayake sakaryace mara wayau,har kina mata kuka ko”?yafada yana sakarmata ido

  

Jikinta na rawa kuka na neman kwacemata tafara ja baya,”Tsaki yaja yana fadin”bantaba ganin sokuwar yarinya irinki ba..”yafada yana maida hankalinsa kan Azeeza,Yaga yadda ta saki baki da hanci tana kallonshi nan da nan ranshi ya baci bai yi wata wata ya saka hannu ya shareta da mari lokaci daya ya sanya kafa yayi ball da ita,Azeeza dataji saukan mari abazata dakuma yadda ya hambareta tayi gefe tana fashewa da kuka”Nunata yayi da yatsa yana fadin”Shhiii..In kikayi Min kuka wlh Sai nayi miki bulala dari,don kaniyarki sa’arkice dazaki dinga dagamata murya,harkina dukanta, wato Abunda yafaru Ranar bai Tsorata ki ba ko?wlh na kara ganin kin mata rashin kunya,sai na saki cikin kankara kin kwana biyu,Try me an See.,Bacemin daga gani,tunkafin nafara kwallo,dake bush girl mai kama da monkey..”Da gudu Azeeza tamike ta shige gida tana kurukuruwan  ihu,kallonsa ya dawo kan Azeema dake gefe tana sharan hawaye,Wani kulilin takaichi ya tokareshi,yanzu wai wannan wawiyar itace matarshi,gaskiya goggo bata kyautamai ba

  Wucewa yayi yana fadin”Kema bita,kafin na chanza mind dina,inyi kasa kasa dake,kuma Nakara ganin kina mata kuka,sai na prison ya fiki jindadi,ko mganar banza ta fadamiki slap her,beat her,yadda zata kiyaye ki,kinji ko bakiji ba..

Da wani Rawan jiki dana baki tace”Na..naji…'” Better..”yace yana wucewa massllacin cikin sassarfa,da hanzari Azeema tafada gidan Goggo don tasan tana Shiga gidansu to tabbas sai Inna Ramatu Tarama ma Azeeza dukan da yaya Captain yayi mata,duk da yanzu tana shakkar yimata wani Abun saboda shi.

*Am Srry For d late update Na mantane ban hidi muku ba,Zaku dinga samu update din Ali gadanga duk bayan kwana daya ne,cuz am busy wlh Abubuwa sunman yawa Akwana dayan ma,karfin hali nakeyi..Masu comment da sharhi duk nagani kuma ngd sosai Am srry bansamu maida Reply ba,saboda wasu abubuwa dasuka shamin kai buh duk nagani kuma ina godiya Allah ya bar Zumunci Amin..*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button