ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

Mallam lawal dake kofar daki Tun dazu yace”Kinyi min Daidai diyar albaarka,Hukuncin yayimata kadan dakin hadamata harda dukane kila tashiga hankalinta mara Tunani kawai..”Yafada Ransa na kuna,inna Ramatu dake bayi tana Allah Allah ta fito itako Azeeza jin zafin mari yasa ta shiga kurma ihu kamar wacce ake yankawa,Ai da gudun bala”i inna Ta fito daga bayi tana tambayan lafiya,daga Azeema har mallam lawal ko kallonta ba wanda yayi sai ta isa ga Azeeza tana fadin”Ke dallah bar kuka gayamin me sukayi miki don naasan daga Uban har yar bamai kaunarki acikinsu..”Wage baki Azeeza tayi tana fadin”Inna Adda Azeema ce ta kifkifamin mari,wai don nazo ina mata mgana kan naga bata hada da kayana ta wanke ba,shine baba yace wai tayi daidai ta takaramin da duka..”Dafe kirji inna Ramatu tayi Tana fadin’Kutumar ubanchan lalle tayi kuskure,ko ni dana haifeki bantaba saka hannu na mareki ba,balle ita,in ita bata hada miki da duka ba,ni yanzu zan hadamata shegiyar yarinya dama ina da cikinta yau zan Famsheshi..”Tafada tana Nufar Azeema wacce ke tsaye tana kallon innar,mallam Lawal yana fadim”A”a Ramatu karma ki fara,kada ki soma,Allah kika tabata zan bata miki Rai..”ina ko jinshi batayi tana zuwa ta kifama Azeema mari tana fadin”Don ubanki jakarkice ita,da zaki mareta zaki ci uwarki yanzu nan don wlh sai nayi miki dukan mutuwa gaba ko sunan Azeeza kika ji kya kiyayeta..”Bata tsaya Sauraran Azeema dake fadin”Inna ki tsaya kiji metamin wlh Azeeza ce bata da gaskiya kada ki dakeni..”Take fada kuka na tahomata,ammh inna bata saurareta ba,ta jawo wani tsohon igiyan Gugansu ta shiga laftama Azeema wacce ta durkushe tana kuka,Mallam lawal yayi Saurin isa kusa da Ramatu yana kokarin amsan igiyan ammh taki bashi da gayyah ma,take zabgamai azuwan bata sani bane,Azeeza na gefe ta share hawayenta ta mike tsaye hannuwanta sarke bisa kirjinta tana kallo tana mirmishin jin dadi.

Goggo dake tsakar gida tana Taran Ruwa afamfo daidai gatangar gidansu Azeema takejin kuka da maganganu harda Muryan mallam lawal yana fadin”Kibari nace Ramatu,kibari ko..”Yake fada,da hanzari goggo ta ture botikin hannunta ta shige daki da Sauri ta dauko hijabinta da wayarta ko Rufe gidan batayi ba,ta fito da Sauri ta fada gidansu Azeema daidai lokacin da Inna Ramatu tawani bangaje mallam lawal yayi taga zai fadi Allah ya taimakeshi ya dafe duka hannuwansa akaasa,Itako inna harda hannu take hadama Azeema,Goggo data Shigo ta ruga da gudu tana fadin”innalillahi..Ramatu mezan gani haka?me Azeemar tayi miki kike mata wannan dukan..”?Tafada tana Ture Ramatun Ta Rumgume Azeema wacce Fuskarta tayi jajir,jikinta duk ya fashe saboda duka,baya inna Ramatu taja tana Huci da sauke gajiya tace”Malama babu Ruwanki,kifice ki bani waje,wlh in ban bar Azeema kwance ba bancika Sunana Ramatu ba..”Goggo ta dago kanta idonta yayi ja tace”Aikuwa bazaki cika sunanki Ramatu ba…”Tafada cikin Fushi kafin ta Fito da wayarta ta shiga latsawa A speaker Ta bude wayar saboda tana son Suji ansam kuwarshi.

Captain Aliyu yana bakin aiki lokacin da kiran goggo ya shigomai wasu bataliyane agabansa yana koya musu Training da dubarin yaki,kiran nata ya katseshi lokacin yana sanye ne da kakinsa,Ya fito a Captain dinsa sak,dakatawa yayu yakoma da baya ya Dauki kiran yana fadin”Goggo..”Muryan ta narawa tace”Gadanga ga matarka Azeema nan Ramatu takamata da duka,na mata mgana tabari tace bazata bari ba,Tace indai batama Azeema dukan mutuwa ba bata cika sunanta Ramatu,inason ka nuna mata ikonka,kanuna mata bata isa ba,indai ni Suwaiba ni na haifeka..”Tafada cikin daga murya.

Aliyu da Tunda goggo ta fara mgana jijiyoyin kansa suka mike Tuni idanunsa suka chanza launi,dunkule hannunsa yayi yanajin yadda muryan Goggo ke rawa batare da wani Tunani ba yace”Don Allah goggo ki bani dama..”, goggo ta karba da cewa”Na baka dama gadanga..Nabaka kowacce dama Tunda dai batasan mutumci ba..”Cije lebe yayi kafin yace’Ngd goggo..Yanzu Ki dauki Azeema ki Tafi da ita in Baba na nan ki fadamai *AZEEMA TA TARE ADAKIN MIJINTA..* yafada cikin tattausawa,Dariya goggo tayi kafin tace”Angama gadanga Allah yayi maka albarka…”Daga haka suka yanke kiran,Goggo ta dago tana kallon inna Ramatu da jikinta ke rawa sai yanzu ta Tuna da kashedin Captain.

Kallonta goggo tayi kafin tace”Kinga ikon namu ko,Uhmm wannan somin Tabi ne,kijira hukunci gadanga..”Daga haka Ta riko Azeeza,mallam lawal daya mike yana haki yace”Jeki da ita Suwaiba..Azeematu Allah ya albarkacin Aurenki Duniya da lahira..’,yafada wasu hawaye na ziraromai saboda takaichi,Azeema na kallon babanta na kuka,sai itama takara fashewa da kuka,ammh cikin Ranta tana amsawa Da Amin,inna Ramatu baki ta rike tana fadin”ikon Allah sai kallo,Abun rabo ne budurwa da jika,wannan wani irin Aure ne,…”Tafada tana bin bayansu goggo da kallo har suka fice daga gidan.

  Azeeza dake gefe tazama mutum mutum har su goggo suka fice,kenan yanzu Azeema zata tare adakin captain a mtsayin mata,duk tana zaune batayi wani Abu ba,ina?bazai taba yuyu ba,wlh Captain nata ne ita kadai indai bata sameshi ba,sai dai kowa ya raasa,zata iya yin kisa akansa koda kisan takama na yar”uwantane Azeema,Idonta gabadaya ya soye hawaye sun kafe saboda bakinciki,juyawa kawai tayi takoma daki ko inna dake kiranta banza ta mata don alokacin ma innar haushi take bata kamar ta makureta ta mutu kowa ya huta,in da bata daki Azeema ba babu yarda za”ayi goggo tazo har takira yaya captain yace Azeema tatare adakinta ba,Duk inna taja,Ran Azeeza tafasa kawai yake saboda kishi da hassada,Shedan sai huramata wuta yake azuciya Tare da kara tusamata tsanar Azeema Aranta,kanta ta buga agaru tana fadin” *BAZAN KYALEKI BA…WLH TALLAHI SAI NA AMSHI ABUNDA YAKE MALLAKI NA NE,KODA ZA”A ZUBDA JINI NE…*”Tafada jini na biyi goshinta kafin tafada bisa gado tana fashewa da kuka.

*Tabdijam…Hmmm…Salon yanzu ya fara zuciyar Azeeza fa ta bushe babu imani ko kadan,ga Azeema zata tare agidan mijinta ga Goggo tabama Gadanga damar daukan kowani mataki..Akwai wasa sosai agaba juz keep following zan warwaremuku zare da abawa*

       *Comment,share,and vote..*

        *Janafty…*

        *Intelligent writers asso….*

*ALIYU GADANGA..!*

 _(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

  *Srry 4d late update…Bohot bohot love Habibaties…*

            *Chapter 12*

_Kaduna_

   “””Yau din Takama weeked ne,Lahadin karshen mako ne,kowani soja dake barikin manya da kanana suna gidajensu domin Hutawa hakane ta faru da Captain Aliyu,Shima din Tunda ya dawo sallar asuba yakoma bai iya tashi ba saboda gajiya da barci.

  Cikin barci yakejin kiran waya da karan Door bell atare,Wayar nasa tana kan Side Drower din gadon nasa ne,hannu kawai ya mika ya dauko wayar da niyyar kasheta sunan Jabir daya gani ne,yasashi ya daga kiran yana fadin”,Hey Dude wht wrong kakemin irin wannan kiran..? ya fada Muryansa da alamun barci daga chan bangaren Jabir ya amsa da fadin”Dallah mallah ka watsake daga wannan barcin Gani akofar Apartment dinka..”Aliyu najin haka ya datse kiran yana tsaki yasan halin Jabir kamar maye da takura,mirginawa yayi gefe ya cigaba da barcinsa ammh sai me karan Door bell din fa bai tsaya ba,har filo yasa ya Toshe kansa ammh duk abanza,Mikewa yayi ya duro daga kan gadon,sanye yake da wani 3quater din wando babu ko Riga ajikinsa ya fito daga bedroom din yana bata rai isa yayi isa ga kofar ya bude jabir dake Tsaye hannu harde akirji Ya bayyana Kare kofar Aliyu yayi yana rollin din idonsa kafin yace”Ya? lafiya mallam kazo kahanani barci sai famam bugamin kofa kake sai kace naci bashinka ban biya ba..”?ya fada yana ballamasa harara.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button