ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

Inna Ramatu taga Azeema ta dade bata dawo ba ga kullin Alala zai kumbura bata dawo ba,Ranta ya baci ta kwalama Azeeza kira,wacce ke daki tana kwance tana hutawa,tana kuma saka yarda zata zama mallakin Captain taji kiran innar,tana fitowa inna tace”Taje wajen bohol ta kirawomata Azeema tace in bazata kawo mata Ruwan bane ta sani..”Tura baki Azeeza tahauyi don ita ta tsani aike,Dakyar ta shiga daki ta sawo hijabinta ta fice afusace,Bagazan bagazan take tafiya Ranta bace Shikuma yana kokarin Fitowa daga motarsa ya bude gareji zai sakata yaga Wucewar Azeeza kamar wata jaka,baima ganeta ba,yadda yaga ta wucene ya bita da kallo,don shi ya zatama inna Ramatun ce,tsaki yaja kafin ya Rufo motar yana kokarin komawa cikin gida kamar an ce ya daga kai sai ya hangi Azeezar tsaye gaban Azeema domin Tazaran kadan ne da gidan goggon,yana hange bohol din da duk Abunda yake faruwa.

  Tana zuwa batayi watawata ba ta ture Azeema datayi nisa cikin Tunani, sai da takusa faduwa tayi Saurin dafa bango,dagowa Azeema tayi tana fadin”Haba Azeeza baki da hankali ne,kikamin wannan bangazan..”,Wani kallo Azeezar ta wurgamata kan tace”Anyi miki Din,ba inna ta aikeki ba,tun dazu kinzo kin tsaya kina bin Mutane da kallo,kamar wata sakarya..”Tafada da alamar raini,gabadaya wajen suka kecemata da dariya,Azeema ta karisa wajen kawayenta suka tafa suna dariya suna nuna Azeema dake hawaye,wani saurayi ne,dan kasan layinsu ne,sunansu sulaiman Ya tsawatar musu ammh sai suka buge damai Rashin kunya,Yana ganin haka dama layi yazo kanshi botikin daya diba ya mikama Azeemar yana fadin”Karbi ki Tafi dashi gida,ni zan jira sai na kara diba..”Azeema da hawaye ya cikamata ido ta kalleshi tana fadin’Nagode..”Tafada Hawaye suna kwararomata,Daukan Ruwan tayi ta juye adaya botikin nata ta Cicciba zata dora akanta,sai ta kaasa sai Sulaimam din yasa hannu ya taimakamata ya dora mata ammh duk da haka sai da Ruwan ya jikata,har hijabin jikinta ya lafe bisa jikinta,albarkatun kirjinta duk sun bayyana waje,hawaye na zuba ajikinta ta dago tana fadin”Nagode sosai..”mirmishi yayi mata bai ce komai ba,tazo zata wuce su Azeeza suka kwashe da dariya suna nunata sai ta zargu tafara hardewa ganin haka yasa Azeeza tahowa gabanta batai wata wata ba ta sanya hannu ta tura Azeema baya ji kake chambal…!Azeema ta fadi cikin katuwar kwatamin kwatan dake wajen botikin Ruwan ya watse bisa jikinta itakuma tayi tsamo tsamo cikim kwata,gabadaya wajen ya dau ihu,Shiko sulaiman baki ya rike cike da mamaki ganin tsabar mugunta wajen Azeeza.

Takaichi Tare da bakinciki sukayima Azeema dirar makiya tana zaune cikin kwata take bin Azeeza da kallo Tana zubar hawaye,itako Azeza banda nunata tana dariya ba Abunda takeyi tana fadin”Tabdijam lallema Adda Azeema kina nufin Ruwan botikin wannan kazamin zaki kaima na gida,wlh da sake kima sake Tunani..”Tafada tana Wurgama sulaiman din wani kallo dama ta tsaneshi saboda sam ko a anguwar baya daukan Raini baya sakarmata Fuska sam.

Yanajin Abunda tace ya nufeta yana fadin”Lalle yarinyar nan baki da kunya yanzu zan koya miki hankali…”Ya fada yana karisowa,kusa da ita baiyi wata wata ba ya daga hannu zai mareta sai yaji ance daga baya cikin wata kakkausan murya..’Hey Leave her…'”Sukaji an fada daga bayansu gabadayansu suka waiga suna kallon mai mgana.

Dukkansu sai da suka Razana hadda Azeema dake zaune cikin kwata tana kuka,yana Tsaye hannayensa gabadaya ya zuba su cikin Aljihun wandonsa,Fuskarasa Murtuke babu Annuri ko kadan har wani ja tayi saboda bacin rai,Azeza da kawayenta yake bi da wani wulakantattacen kallo,wanda Tuni suka Tsorace kamar su saki Fitsari awando ganin yadda yake kallonsu Jiyoyin kansa na mikewa saboda bacin rai,Kallonsa ya maida kan Azeema dake zaune cikin kwata tana kuka Jikinta duk ya baci ga Shi hijabinta duk ya manne mata ajiki,baisan dalili ba,sai yaji wani mugun Haushi ya tokaresa kamar ya bita cikin kwatan ya ci ubanta Tunda ta zama solobiyo,Sulaiman kuwa yana ganin captain ya koma gefe yana dariyan mugunta domin yasan daga yanayin kallon dayake musu yau din nan sai sun gane basu da wayau..

Taku yafarayi zuwa garesu yana wani kame idonsa guda daya na salon mugunta,Tuni suka tsorata suka fara ja da baya,Azeema ko jikinta na rawa ta mike saboda atunaninta wajenta zaizo ya fara ta kanta sai ta ga yayi Pointing dinsu Azeeza yana fadin1,2,3,4,5,6….All af u come here…’,Yafada cikin gadara,Ai da wani tsoro suka fara kallon junansu tsawa ya daka musu yana fadin”don’t Force me to Mention my Statement..All of u will be in Tourble i swear..”,Yafada yana wani buga kafansa akasa,wanda saida Mutanen wajen suka Razana.

_Wowow…Ran Maza fa ya baci..Su Azeeza kun Shiga Tarama ba Uku ba,do da Alamu Fushin sojan zai sauka bisa kanku,kilama Harda horan Sojoji zai baku????Wayyo,Allah ya kwaceku maganinku kenan,Fans ya kuka gani kuna goyan bayan Captain yaci kaniyar su Azeeza?..Cike Tagging dinki da kayatattacen Sharhi ta hakan ne kadai zan gane kuna biye dani_

         *Comment,share and vote…*

         *#Janafty…#*

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

      *Chapter 10*

     “”Jikinsu na rawa suka fara takowa zuwa gabansa,kowacce tanaji kamar ta saki Fitsari awando saboda tsoro da Razana,Kafin su kariso ya sunkuya akasa ya sanya hannu ya dauko wata sanda baya yakoma daga chan wajen inda ya faka motarsa ya shiga jan Dogon layi,yana gama ja,cikin wani Fusata yazo ya wucesu kamar kiftawa da bismillah ya isa chan nesa da bohol din ma nan yaja wani dogon layi,Ko kallonsu bai yi ba,daga chan bangaren ya nunasu da hannu yana fadin”Ku yan iska ko? marasa mutumci,dama kune marasa tarbiyan anguwan ko? ok To iskancinku yazo karshe daga yau oya all of u ku fara frog jump daga inda layin chan yafara zuwa inda ya kare,kuma 50 zakuyi each zuwa da dawowa to be counting one ne…”Yafada cikin gadara da isa.

  Gabadayansu suka kalli juna ganin zasu batamai lokaci yasa ya fara taku zuwa garesa ai da gudu suka isa ga layin kowacce ta duka tafara,daga nesa yace”duk wacce batayi da kyau ba,ko ta gama sai ta sake so is better da ki zage kiyi yadda nace…”Yafada yana harde hannuwansa akirji Sulaiman dake gefe yana kunshe dariya yace”Yallabai zanyi musu couting.”,Da kai ya amsamai yana cije lebe kafin yace”ka sa ido akansu..Duk wacce bata yi dakyau ba juz ka waremin ita yau zasu ci ubansu ne..”,Yar dariya Sulaiman yayi yana fadin”Baka da mtsala yallabai,ya fada yana kallonsu yana fadin”Toh maza kuyi da jiki…one,two…three,wlh kika bari aka barki abaya zan tsayar dake..”Yafada yana dariya jin haka yasa suka zage sai yi suke kafin kace kwabo sun Fita hayyacinsu ko goma basuyi ba,ammh haka suke kuka da majina,Tuni layin ya cika da mutane anata dariya wasu kuma na murnan Abunda ke faruwa don daman kowa yasansu Azeeza alayin basu da kunya ko kadan,wasu sai fadi suke gwara hakan,kila daga yanzu sayi hankali.

  Azeema na gefe tana barin jiki Tana kallonsu Azeeza yadda suke kuka harda majina,Dasun bude baki zasu yi mgana sai captain yace +anoder 50 din,dole sukayi Shuru da bakinsu domin Wannan wahala tayi kama da wahalan gidan yari ne,Shiko yana gefe ya harde hannuwa bisa kirji yana kallonsu yana dan murmusawa,Da kallo yabi Azeema yadda tayi wani kalan Tsausayi nufota yayi sai ta hau ja da baya,tana ganin ya kariso sai ta duka ta kama kunni tana fadin”Don Allah kayi hakuri nima zanyi..Zanyi..”Take fada tana kokarin Fara tsallan kwado tsawa ya dakamata yana fadin”Stand…”mikewa tayi jikinta na bari,Tsaki yaja kafin ya juya yana fadin”Ina abubuwan dakika zo dasu diban Ruwa..”Bakinta na rawa ta nunamai botikan guda biyu,don dayan kam ya fashe,bai kara kallonta ba ya isa garesu,da hanzari ya isa ga bohol din yasa hannu ya ture layin dake kai ya aza botikinta Yasa dayan laullausan hannunsa yafara buga bohol din,Jikin Azeema na rawa take binshi da kallo yana zubamata ruwa bai dauke hannunsa ba,sai da ya cika duka botikan guda biyu,da hannu biyu ya daukesu atare,ya nufota cike da mamaki mutane ke binsa da kallo yanayin komai cikin Jarumta da takama,sai da yazo gabda da ita kafin yace”Wuce muje bush girl kawai…”Yafada yana huci jikinta na rawa ta mika hannu tana fadin”ba..Bari na dauka..”Wani dirty look ya watsamata kafin yace”Leave dis place now…”Yafada a tsawace,da hanzari tashiga gaba tana bin su Azeeza da kallo wadanda sukayi chanza kammanin saboda wahala ga Sulaiman Shiko ba mutumci da gayyah sai yace basuyi daidai ba,sunyi yafi ashirin ammh yace biyar ne,mai kyau sauran sai sun sake,Bayanta yake bi dauke da ruwa,Ransa na masa kuna banda An raina masa wayau wai wanna ce matar da”aka Aura masa,kullum gantali alayi kamar wata karya,Saboda cin mutumci harda Debo Ruwa saboda Rainin wayau,Kallonta yake tana tafiya wani takaici ya makarosa ji yake kamar ya shakota ya kifkifamata mari saboda haushi,Suna zuwa kofar gidansu taja ta tsaya tana so ta kalleshi ammh tsoro yahanata,Kanta na kasa tace’Don..Allah ka..kayi hakuri ka…”Bata gama Rufe baki taga ya wuceta ya shige gidan dauke da Ruwan baki ta rike tana bin bayansa da kallo,kafin jikinta asanyaye tabi bayansa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button