ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

   

    Sakinta yayi yana fadin”it ok kikiyaye gaba,komai ta tambayeki as From today karki bata wata fuskan da zata sake sanin Sirrinki kina gaba da ita,ita din kanwarki ce so be carefully…’Yafada yana kauda kai shuru tayi tana wasa da hannunta kafin bazato yaji ta jehomai tambayar

  “Toh in kadaina son Ni”ima wakake so..? saurin kallonta yayi yana hade naman goshinsa Cike da mamaki saurin sadda kai tayi,cike da kunya Dan dariya yayi kafin yace”Ada nasota lokacin danake Tunanin Ita zatama abokiyar rayuwata buh tun lokacin da mahaifinta yanemi cimin zarafi naji tafita daga Raina,any way kobana sonki Azeema kinada wani babban mtsayi Araina keda mahaifinki domin kun sharemin kasan da mahaifin Ni”ina ya watsamin..”Yafada yana kallonta kur da ido,kallon ne yabata kunya tayi Saurin tashi ta fice waje da gudu,da wani kallo yabita yadda kugunta ke kadawa rausayar dakai yayi yana cije baki,nan take mganar Jabir ta fadomai Aranar da”aka daura musu aure….

  _Yarinyar tayi zaka samu duk Abunda kakeso wajen mace,tama fi Ni”imar komai…_Tuna haka dayayi ne yasashi shan mur yana kunkuni shidakai na yadda har jabir yarigashi gano Abunda shi yakamata yafara ganowa.

  Azeema na Fita waje tacikaro da goggo daga gefe zaune kan wata kujerar roba dake wajen tana cin gyadanta soyayyiya hankalinta kwance baki Azeema ta rike kafin tace!la..Goggo yaushe kika dawo..”Kallonta tayi kafin tace”Na jima Azeema..”Karisawa Azeema tayi tana fadin”wlh goggo bamuji shigowarki ba..”Goggo tace”Ai bazaku ji ba,na Shigo ina ta rafka sallama har daga makota anajina,harfa leka dakin nayi naga ko barci kike sai na samu ana zantawa tsakanin mata da miji,shine nace toh toh..Bari nayi baya har kugama kada na katseku..”Tafada tana dariya kunya takama Azeema sai ta labe bayan goggo tana yar dariya.

  

  Gyadar goggo ta nunamata tana fadin”kega Abunda baba Ade tabani tace sai kinzo zaki karbi naki..”mikewa Azeema tayi tana fadin”la gyada goggo,yanzu kuwa zan mata dirar makiya sai tabani nawa..”tafada tana fadawa daki,koda ta shigo sai taga kamar gadanga na barci sai ta shige kurya tadauko Abayarta ta fito harta kai kofa zata fita taji ance daga bayanta..”Ina zaki..?”Saurin waigowa tayi still idanunsa na kulle,cewa tayi”Gidan Baba ade zani..”lalle yarinyarnan to ki koma ki cire hijabin sai gobe yanzu yammah tayi..”Ya bata amsa.

  Tura baki tayi da jin Abunda yake cewa,bude idanunsa yayi karaf ko suka hada ido dashi ga gudu ta kariswa bedroom din goggo tana dafe kirji,shiko mamakinta ne yacika ashe ta iya tsiwa dama,mirmishi yayi shi kadai kan yamike agajiye ya fice nan waje yaga goggo suka gaisawa alwala ya daura yafita sallar mangariba,itama goggo tayi nata ta shiga ciki tayi sallarta ita da Azeema wacce goggo kema gwalo da dariyan hanata fita da gadanga yayi sai mata kwalelen gyadan takeyi itako duk Haushi ya cikata sai da goggo tagama jan mata rai kana tabata gyadan,shiko gadanga a massallaci ya zauna har akayi issha,”i kafin yakoma gida,kuma bai ma koma barayin goggo ba yashige daki yayi Shirin kwanciya saboda gajiya.

      ****************

  “Oh my god Sweetheart don Allah kibar wannan kukan,bai da wani amfani juz keep praying in Captain mijinki ne,ko duk duniyanan zasu hadu wlh basu isa suhana ba,kuka bai da wani amfani…”Muneera take fada tana Riko Hannun Ni”ima,Share hawayenta Ni”ima tayi kafin ta dago idanunta jajir Tace”Ya zanyi Ya kikeso nayi Sweetheart..Wlh i love Captain Bazan iya hakurin rashinshi ba,bakiji menake fadamiki bane,he told me bazai taba Aureba Sweetheart,yayi Aurensa ya barni.”Tafada wasu hawaye suna kwaranyomata, Rumgumeta muneera tayi tana lallashinta tana fadin.

  “Nidai ki daina yawan kukan nan Sweetheart..Wlh banijin dadi,insha Allahu captain Sai yazama naki da yardan Allah…”tafada tana bubbuga bayanta Lamo Ni”ima tayi tana Shesshekan kuka ahaka Mami tazo ta samesu Tana tsaye tace”Kingan ta nan Muneera haryanzu kukanta yaki karewa,Ni narasa wannan bala!in,sai kace Aliyun ne, kadai Namiji aduniya ko Rasashi Tamkar rasa rayuwace gabadaya,Allah tun inajin Tsausayinta hartakoma bani Haushi,ai sai kiyita kece keda wahala..”Tafada kafin tafice Cikin Fushi da nuna Abun ya dameta.

  Bayanta Ni”ima tabi da kallo hawaye suna kwaranyomata,Zame jikinta tayi ta mike Tafada bedroom dinta tana sharan kwallah,bayanta Muneera tabi da kallo tana mamaki wani irin sone Ni”ima kema Captain data kasa hakura dashi Tunda yayimata nisa,gabadaya ta rame ta dishe ta lallace kamar ba ita ba,Abun nacimata Tuwo akwarya ammh babu yarda zatayi domin hartagaji da ba Ni”imar baki tahakura takoma ta zuramata ido saboda al”amarin nata yawuce duk yadda bawa zaiyi tsammani.

   ______________

Azeeza ko alama bata ja da baya ba,Abunda yakara bata tsoro ko School Azeema bata nemeta ba Abun ya matukar Dauremata kai,tafara Tunanin kodai ta ganotane ammh duk da haka bata ja baya,ba washegari dataje mkrantar agaban idonta maikeken yazo yayi Dropin din Azeema kuma Abunda kowa bai sani ba Duk motsin Azeemar a idonta domin tana labe akofar gidansu tagazuwam mai keken yazo Daukan Azeema,batayi mamaki ba,tasan kila aikin yaya captain ne,don taga He is very smart yana da Saurin Ramfo mutum tana ganin Azeema ta Shigo cikin mkrantar ta nufi ajinsu sai ta chanza shawara sai tabaro ajinsu ta ratso ta tsakiyar mkranta kamar zata office din Principal nan sukacikaro da Azeema wacce ke kallon Azeezar Tunda daga nesa tasha mur tana kallonta ammh ta kauda mata kai.,Kiran ta Azeema tahauyi ammh Azeeza tayimata banza kamar bataji ba,da hanzari Azeema tatake mata baya da dan gudunta sai gashi tasha gabanta tana fadin”Haba Azeeza mgana fa nike miki ke man banza..”Wani kallo Azeeza ta maka mata kafin ta raba ta gefenta zata wuce,ammh sai Azeema taki bata damar haka Ta hanyar riko hannunta.

Cak Azeeza ta tsaya ammh bata waigo ba,juyo da ita Azeema tayi tana fadin”Wai Azeeza duk miye ya faru ne ? nine fa Addanki Azeema ai yaci komiye nayi miki bai dace nayi mgana acikin mutane ki tsinka ni ba..”Yamutsa Fuska Azeeza tayi kafin tace”Dole na Tsinka Adda Azeema naga kin zabi Namiji,Namijin ma bare akaina,kinga ai sai naja baya..”Ware ido Azeema tayi kafin tace”lala..Injiwane Duk duniyar nan ina da kamarki ne..”Bata Fuska Azeeza tayi kafin tace”ba gashi ba,Tunda har wanda aka lakaba miki amtsayin mijinki ya iya cimana mutumci dagani har ke da baba ba wanda ya ragamawa..”Tafada harda matso kwallah Zuramata ido Azeema tayi kafin tace”Shi yaya captain din? da hanzari Azeeza tace”eh mana Ranar dana biya miki yayi min kaca kaca hardacemin wai daga gani na watarana magajiyar karuwai zan zama..’Takarishe fada harda fashewa da kukan karya.

Baki Azeema ta rike tana kallon Azeeza,Zuciyarta takasa gasgasata,Saboda Duk kalamanta babu gaskiya,ganin haka yasa Azeeza tashiga jerama Azeema rantsuwa hartana fadin yace kema wani Shiri kawai yake akanki da zarar yacinma burinshi zai baki takardanki,nidai don Allah Adda Azeema karki kuskura kiba dan iskan sojan nan kanki saboda bai da wani buri,illah ya maidaake karamar bazawara ya sakeki kuma Allah duk Abunda kikaga yanayi Duk shawaran uwarsace goggo…”Ai Sai Azeema tazama out of control zuciyarta tashiga zafi lokaci daya wani bangare na zuciyarta na amincewa da kalaman Azeeza wata kuma na kwabarta,Zuciyarta ta bata cewa in mganar Azeeza gaskiya ne,to ai yaya captain bai taba nuna wani zalama akanta ba asalima basu taba zaman Fahimta ba sai jiya,kodai kodau duk cikin plan nasa ne,Goggo kuma bazata taba cin amanarta ba,itace makwafin mahaifiyarta ta ci kashinta da fitsarinta goggo ta goyata da bayanta duk Abunda uwa zatayi ma danta shi goggo take mata,gaskiya bazata taba yarda da goggo za”a cuceta ba,to ammh mganar Azeeza Abun dubawane,domin akankantar Shekarunta bazata kitsa mgana kai tsaye ba,itako Azeeza ganin yadda Azeema tashiga Rudani Shiya bata damar kara mata famfo tana tsaro mata wasu mganganun wanda ita da kanta ta tsarasu,nan da nan Azeema ta amince da Azeeza ,100% harda kukanta tana fadama Azeeza ita yanzu yazatayi batasan ya rayuwarta zata je ba,shawara Azeeza tabata kan daga mkranta ta wuce gidan Baba Ade koda goggo taje ta tubure tace wlh bazata koma gidan goggo ba,bayan kwana biyu kuma ta bijuro da zencen sai yaya captain ya saketa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button