ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

   Suna karisowa goggo Ta Rumgume gadanga tana fadin”Oyoyo gadanga..Kai ammh kai ja”irin yaro ne ka iya zuwan da Annabi ya hana..Au tare ma kuke da jabiru kai marabanku da bakin sassafe..”Ta fada tana Sakin Gadanga takamo hannu jabir wanda ya duka yana gaisheta Fuskarsa Gadanga ba walwala yace”Wai goggo daga ina kikene da wannan Farar safiyan..”,? Bata Fuska tayi kafin tace”ya’yana na Raka mkranta sun makara suna Tsoron duka,shine naje mkranta na fadamusu basu da hankali ne,matar auren zasu daka,kuma ma matar Auren matar soja,Aliyu gadanga..”Tafada kai tsaye ko ajikinta galala Gadanga yake kallonta kafin yace”Wasu ya”yan naki..? asakarce goggo ta kalleshi don ta gane tambayan Rainin wayau yayi mata,kauda kai tayi kafin tace”Matarka Azeema da kanwarta Azeeza ko ba ya”yana bane..? tafada tana zubamai ido,Bata Fuska gadanga yayi kamar zaiyi kuka,Tsaki goggo taja kafin tace”Ohon maka kabar wani tabe Fuska kamar kaga kashi,ni wlh al”amarinka wani lokaci na ban mamaki,bansan wakake tabema Fuska ba,mganata ko ni din kaina..? dariya ta kwacema Jabir yace”kai goggo ya”za’ayi ya tabe miki Fuska,kila mganar ne bataimai dadi ba..’Yafada yana kallon gadanga Ta wutsiyar ido wanda yayi gaba yana fadin”,Don Allah goggo kibar wannan mganar juz open d door..”Harara Ta zabgamai kafin tace”Alqur”an Sai ka fasasara mai kace daga karshe,kasan dai na hanaka juyamin yare ko”Ta fada a fusace,dariya ta kullema Jabir ciki yace”Goggo cewa fa yayi ki bude kofar..”Dariya goggo tayi kafin tace”oh yanzu nagane,nima fa da inajin Turancin nan miyar kuka ne suka danneshi wlh,ammh da in na Fara Turanceku harshi gadanga sai na kureshi..”Ta fada tana bude kofar gidan wanda ta samai kwado sanda zata Fita,Dariya takama Aliyu,sai dai ya share Shiko Jabir harda kaiwa kaasa saboda dariya,Aliyu ne ma ya kwashi jakukkunansu ya Shiga dasu Kafin yakoma ya Shigar da mota gareji,Shiko Jabir yana chan wajen goggo yana janta da hira suna dariya datace zata dora musu girki cewa sukayi akoshe suke..Komawa goggo tayi ta zauna Aranta tana fadin”Dama banyi niyyah ba,kwaci kaniyarku don Ni ina da Sauran dan wake na najiya wanda Azeema tayimana..”tafada Aranta tana mirmishin mugunta,tunda ta lura daga gadanga har abokin nasa yan Air ne,komai sai sun Tsara suke aiwatarwa.

Shiko Aliyu yana Shiga Sashensa Abunda ya bashi mamaki abude ya gani bai kawo komai Aransa ba,sai ya ce kila goggoce ta bude don tagyaramai ammh sai mai ko”ina tas sai tashin kamshi,ga remot kan kujera ga Talabijin akunne,bai gama mamaki ba sai da ya leka kichen yaga komai net..Ga kuloli nan da alamu ba”a dade da wankesu ba,baki ya rike yana Tunani ko goggo ta dawo shashenshi da kwana ne,don ya san zata aika,Da hanzari ya fice zuwa dakin goggo suna tsaka da hira da jabir ya Fado yana Fadin”goggo chan Shashen kika koma da zama kuma? akarkace goggo ta kalleshi kafin tace”me..?meka gani hala..”yace”alamun mutum na Rayuwa awajen..’tsaki goggo taja kan tace”ji wata tambayar banza,dama da mutum mana,ka manta ka ijiye mata…Toh Azeema ce ke zaune aciki..’Tafada kai tsaye tana Hararanaa,Tsaye yayi yana zare ido,don shifa ya manta da wata Azeema balle har ya Tuna da Abunda ya faru dafe kai yayi kafin yace”Toh goggo miye laifin barayinki,naga dai kema kina da dakuna..”goggo tace”Eh na saukan baki ba,ammh ba wajen ijiye matar gadanga ba,..”Tafada tana kallonsa,yanajin Abunda goggo tace yafice saboda yasan halin goggo ta kan wannan mganar sai ta maida Abun ya zama babba,yana Fita jabir ke tambayan goggo dama Azeema tatarene,nan fa goggo ta gyara zama ta kwashe From A to z bata rage komai ba.mamaki yakama jabir don ko kadan Aliyu bai Fadamai ba Fatan Alheri yayi musu da Fatan zama lafiya.

  Shiko Aliyu saboda bacin Rai waje yakoma ya zauna akofar gida yana latsa latsen waya saboda Haushi,yasan Halin goggo tsaf zatamai tas agaban Jabir shikuma ya samu Abun Tsokanarshi,shiyasa ya fice daga gidan ko Ransa zaiyi sanyi,yafi awa biyu har aka kira sallar azahar yatafi massllaci yayi achan suka hadu da jabir suka dawo Tare nan kofar gidan sukaci burki Aliyu Daure Fuska yayi saboda ya riga yaasan Goggo ta fadamai komai Saboda bakin goggo fa Sikat ne yariga ya santa Sarai Shiyaasa yasha kunu kallonsa jabir yayi kafin yace”Kai Dude ashe Azeema tatare,Toh yanzu ina zan Dinga sauka Tunda yanzu kayi iyali..”Kai Tsaye Aliyu yacemai”Nima Tunanin danakeyi kenan,gwara na saman maka wani waje don bazan iya hadaka shashe daya da iyalaina ba..”kallonsa Jabir yayi kafin yace”Kan ubanchan,yo meye Nufinka bunsuru ka maidani..Toh kona ina akuyanci bazan bi iyalinka ba..”Ko kallonsa Aliyu bai yi ba yace”Kaji dashi dai.”Jabir yace”Muji dashi dai,Wai Dude ya mganar zuwa wajen yarinyar nan kafa san don ita nazo garin nan..”wani kallo Aliyu ya watsamai kafin yace”Dama ni kake jira na rakaka..? gyada mai kai yayi dan mirmishi Aliyu yayi kafin yace”U are not Serious,Tunkan dare yayi maka mallam kanemi mai rakaka,Ban da kana ajawo gaja harwata budurwace zaku hadu awaya kafara Dating dinta kuma wai harda zuwa zaka wajenta,toh bada niba Allah kiyaye hanya..”Yafada yana buga kafadanshi.

  hararansa Jabir yayi kafin yace”Toh ina Ruwan mutum..Karkaje kar Allah yasa ka rakani nima ba bako bane a gombe,mganar budurwata kuma ka iya bakinka don daga yanayin muryata nagane cewa babbyn Ta hadu wLh..”Dariya Aliyu ya fashe dashi kafin yace”Allah mazaje.Toh anjuma ka Shirya muje sai na ganta.”Riko kafadansa yayi kafin yace”Da gaske Dude..”gyadamai kai yayi Alamar da gaske ne,Hannu jabir ya bashi suka kashe kafin yace”Tanque Dude…,”Bakomai yima kaine ai..”gadanga yafada Saurin mikewa Jabir yayi yana Fadin”bari na kirata nabata Suprise kasan bata san na Shigo gombe Ba..”Kallonsa kawai Aliyu yayi kafin yace”yakamata mr love..”ya fada yana bin Jabir din da kallo yadda ya wani rabe gefe yana rage murya girgiza kai kawai Aliyu yayi yana tsausayawama  Jabir don ya shiga tsaka mai wuya kafara soyayyah da wacce baka taba gani ba.

  Yana nan zaune yana latsa wayarsa yaji karan mashin agabansa,kamar zai Share sai kuma yaji ya kasa yana dagowa yayi mugun gani Azeema ce da Azeeza sukayi 2parking kuma Azeema ce a tsakiya ga Azeeza nada jiki duk ta cinye wajen Shiyasa aka matse Azeema ajikin mai mashin,kutumar ubanchan Galala Aliyu yayi yana kallon yadda kirjin Azeema ya manne da bayan mai mashin,Azeeza data Fara sauka ta gefen ido ta kallon Aliyu tana ganin yadda kacokan hankalinsa yana ga bin Azeema da wani kallo,Addu”a take aranta Allah yasa yazo ya mareta,domin Tun asaman layi Azeema taso su sauka Azeeza ta hana kamar ta sani suna shaho kwanar layin tahangi jabir,kafin ta hangi yaya captain da gayyah takara matse Azeema ta kara hadewa damai mashin kuma taki yarda asaukesu ko”ina sai kofar gidan goggo,itako Azeema bata lura da Abunda ke Faruwa ba ta dirko daga kan mashin tana laluban jakarta zata dauko kudi,daga bayanta taji ance”kai…”gabadayansu suka waiga har mai mashin din,yana tsaye ya harde hannuwansa bisa kirji da hannu ya nuna mai mashin din kafin yace”kai..Come here,karka bari nazo domin Abun bazai yi kyau ba..”

  galala mai mashin din ke kallon Aliyu kafn yace”,Kai mallam dawo Natsuwarka domin ni bakaga nayi kama da lusarin Namiji ba,anki azo din zokayi Abunda zakayi don uwarka…”Jin Abunda yacene ya kusa saka Azeema Fitsari awando,saboda tsoro baya taja kafin tace”Armmm…Yayan mune fa mallam..,”Tafada bakinta na Rawa shiko Aliyu mamaki ya daskaran dashi,saboda jin kai tsaye wani banza ya zaganmai uwa Takowa ya farayi yana kallon mai mashin din yana wani cije baki,ganin haka yasa Azeeza Saurin Rumgume Azeema tana fadin”wayyo Adda Azeema kibama yaya captain hakuri,sai da nace mudaina hawa mashin ammh kullum sai kice sa mun hau ai ga irinta nan..”Wani banzan kallo Aliyu yabi Azeema dashi ashe bata da hankali bai sani ba,duk duniya babu Abunda ya tsana irin yaga mace ta hau mashin koda ita kadai,wato ita saboda taceewa su biyu suke hawa saboda wulakanci ko,yau zai koyamata hankali,shikuma mai mashin din daga yau bazai kara Dauka wata mace ba sai dai ko in matarshi ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button