ALIYU GADANGA Page 11 to 20

shiko Aliyu Tiryan Tiryan yake bin Azeema abaya suka fita daga gidan har zuwa bakin Titi kanzil bai cemata ba,itako tsoro yahanata ko waigo Suna zuwa ya taran mata wani dan adaidaita suka gaisa cikin mutumci kafin yadan duka sukayi mgana,ya fadamai ne Nawa zai Dinga biyansa yana zuwa yana dauka Azeema kullum yakaita mkranta ya dawo da ita,nan mai Adaidaita yace ya yarda buh ammh sai dai yafison adinga biyanshi Duk sati saboda halin Rayuwa..Nan take gadanga ya amince yace yakaita ya dawo sai suyi mgana bayan ya nunamai gidan da in yakaita zaizo ya sameshi,baya yayi yana kallonta kafin yace”oya ki Shiga yakaiki..”tsam tayi kafin tafara waige waige lura da hakan dayayine yasa shima ya waiga yana fadin”wakike nema..? bakinta na rawa tace”Az…Azeza..”bata Fuska yayi kafin yace”Wai Shin tsaya na tambayeki Azeezar nan ita ta haifeki ne? kokuwa dai ke Sakarcin ki haryanzu bai nuna miki kina zubar da kanki bane come get in kafin ki bani haushi..”dago kanta Azeema tayi idonta sun ciko da hawaye kafin taji kawai taji baki ya bude tace”Ban da kowa fa,ita kadai ce wacce zan daki kirji na nunata amtsayin yar”uwanta ba sakarci bane yaya captain kulafuncin yanuwantakane..”,Tafada hawaye suna gangaromata,kuramata ido yayi baisan dalili ba,sai yaji kalamanta sun sanyarmai da jiki kallonta yake cike da tsausayi kafin ya jinjina kai yace”it ok wipe ur tears..Kije kidawo daga mkranta zamuyi mgana kinji..”yafada cikin sanyin murya gyada kai tayi tana Share hawaye kafin ta shiga adaidaita din Hannu ya sa aljihu ya ciro 1k yamikamata kin amswa tayi illah nuna mishi Hannunta datayi tana fadin”Goggo ta bani..”Kallonta yayi yadda idonta suka cika da ruwa sam baiji dadi ba juyawa yayi yana fadin”Ok Tunda kinfi son ta ringa baki da hannunta zan barmata sai ta baki..Take care of u self..”Mirmishi kawai tayi tana bin bayanshi da kallo har suka bacema ganinshi,har takai mkranta tana Tunanin yaya captain ita kadai sai sakin mirmishi take in ta tuna da wani Abun.
Itako Azeeza bata hakura ba Domin Tana Shiryawa tana Fitowa daga gida tazo gidan goggo,daga kofar gida ta tsaya ta faman leke,hango yaya captain tayi ya fito tsakar gida yana waya bayi da riga dagashi sai dogon wando gabadaya Sirrin jikinsa ya bayyana awaje,Azeeza dake labe Tuni taji ta manne da bango saboda shauki kirjinsa ta kurma ido lokaci daya tana wani lashe baki tama manta damai tazo yi Shiko yajuya baya ta jikin kofar goggo ya hango Azeeza ta leke bayan yajuyamata baya dayake kofar tanada glass daga samanta ne,mamaki yacikasa bai yanke wayar ba ya juyo yafara taku zuwa wajen yanayi yana dan kallon gefe Azeeza batama Fahimci cewa gadanga ya taho ba daga kanta kawai taji ance”Ke…”Cikin tsawa firgigit tayi saboda razana tasaka kafa zata zura da gudu gadanga yayi Wuf ya riko hijabinta yajawo ta baya ya watsar da shegiya kasa yana binta da wani banzan kallo,ammh mayyar hankalinta naga kan Suran jikinsa tana wani kifkifta ido nunata yayi kafin yace”ke ubanwa kike nema da kike ma Mutane labe..? bakinta na rawa tace”Adda Azeema..”tabe baki yayi kafin yace,”Oh yanzu kikasan da Adda Azeemar yaushema ta zama Addarki mara mutumci,ke nifa ban ma yarda dake ba gayamin waya Turoki ko Uwarkice taturo kizo ki cutar da Azeema..? yafada yana dukawa daf da ita baya Azeeza taja tafara tsorata da yaya captain din tsawa ya dakamata yana fadin”Zaki gayamin kokuwa sai na Fasa kanki da bindiga..”Jin zencen bindiga yasa Azeeza Saurin cewa”Armmm..A”a ba wanda ya Turoni..”Tafada idonta kyam akan kirjinsa sai alokacin ya fahimci inda idonta ke kai,mikewa yayi lokaci daya yajefa wayarsa cikin aljihun wandonsa yana jinjina kai yake fadin”Oho Yanzu na ganoki ke ashema ba iya rashin kunya kika tsayaba harda bin maza ko? Saurin girgiza kai tayi zatayi mgana ya dakamata tsawa yace,”Rufe min baki don ubanki zan miki karyane,kina kafe ne da ido kamar kin ga wani tsohon customer dinki ko? shegiyar daga ganin yadda kike kallona tsab aka kyaleki watarana zaki iya zama magajiyar karuwai,wlh tallahi kinji Rantsuwar dan musulmi in nakara kama idonki cikin nawa sai na fito da kwakwalwar kanki,Uselless kawai..”Yafada kan yasa kafa ya shureta yana fadin”Ur way out..Kar in kara ganin kafarki agidan nan..”Yafada yana nunamata kofa da Azama Azeeza tamike zata fice hawaye sun cikamata ido,Harta kusa Fita yace”ke tsaya..,kinga ko Azeema naga wani chanjin dabi”a awajenta ko naji wani lbrin wani Abu yafaru wanda ba halinta ba i swear daga ke har mahaifiyarka karnuka zasuyi watanda da Naman jikinku..”Yafada yana kadamata hannunsa,Azeeza tayi waje da gudu saboda kukan daya tasomata mkrantan data fasa zuwa kenan Inna Ramatu Ganinta kawai tayi ta shigo tana kuka,kuma tayi tambayar Duniyanan ammh Azeeza tayimata banza Kyaleta tayi,Saboda Yanzu kwata kwata tadaina gane kan Azeezar yanzu,itako kuka take da Duk Abunda tashirya sai Yaya captain ya Ruguxamata shirinta Kuka take da takaichi sai taga alamun Nasara sai kuma komai ya kwacemata.
Jabir da Aliyu suna cikin karyawa jabir ya samu waya daga Amminsa tana Fadamai mijin kanwarta dake jos Allah yayimai Rasuwa sakamakon hadarin mota yanzu hakama chan zata wuce yayi kokari yazo ya samu jana”iza Babu ko bata lokaci suna gama karyawa suka Shirya suka kama hanya Aliyu yayima Jabir din rakiya goggo tabisu da Fatan alheri tare da Addu”ar Allah yajikan wanda ya Rasu..Suna tafiya ba dadewa sai ga kawu bala ya zo,dayake ya shigo gombe yazo wani taro ne na Siyasa sai ya biyo nan wajen Suwaibar suka gaisa nan take fadamai yanzu su gadanga suka Dauki hanyar jos,Fatan isa lafiya yayi musu,Nan ya zauna sunata hira har bayan Azahar,har sai da Azeema tadawo mkranta ta tarar dashi,nan goggo ke koramai bayanin Duk Abunda ke Faruwa hakika ya tsausayama Azeema kuma yayi jinjina ga hikimar gadanga nan yayita ma Azeemar Nasiha tare da Shimata albarka da zai Tafi 30k yabama goggo Azeema kuma 10k yabama goggo 10k ta ijiyema mallam lawal saboda bazai iya jiransa har yadawo daga kasuwa ba,sallama sukayi cikin so da kauna tare kewa kafin su dau hanya shida tawagarsu goggo na bada sakon gaisuwa ga Umaima.
Aliyu kwana daya yayi ajos yadawo gombe yabar Jabir achan,shigan yammah yayi don bai shigo gombe ba sai Wajen biyar na yammah koda ya shigo gidan Azeema kadai ya tarar agidan wai goggo batanan Tatafi gidan kakarta Baba Ade bata da lafiya itama wainar Fulawa ta tsaya soyawa Goggo ko tace wlh bazata jirata ba,in tagama tazo daga baya toh tana kichen tana ta Faman Sauri taji shigowar yaya captain gabantane yayanke ya fadi Ras..,Sai da ta dafe saitin zuciyarta dakin goggo ya Shigo yana mamakin jin babu alamun mutum Agidan Motsin dayaji akichen ne yasashi Nufar nan Yana shiga yacikaro da Azeema tana tsaye tana kwashe wainar Fulawan Tsaye yayi yana kallonta itako ganinshi ya sata ta Rude bakinta na Rawa ta Furta..”San..nnu da zuwa..”Yamutsa Fuska yayi kafin yace”Baki amsa sallama ne?ina goggo..? ya jehomata tambayoyi fiki fiki tahau da ido kafin tace”Banji bane,goggo kuma tatafi gidan Baba Ade…”juyawa kawai yayi yana fadin!Taimakeni da Ruwa don Allah..”daga haka yafice daga kichen din.