ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

_Allah yayi ma Rayuwarki Albarka Diyata LADINGO IKON ALLAH…Akullum ina alfahari dake Endless of love Dota_????

    *Comment..And share…*

    *Janafty…*

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

       *Chapter..15*

  “”Da Sauri ta kwashe wainar Fulawan ta kashe gas din,Fridge ta bude tadaukomai Ruwa mai sanyi sama ta taka tahau ta bude drower din dake kichen ta dauko wani filet mai hade da kofuna da hanxari ta daurayesu ta dora Ruwan bisa kafin ta jeramai kofuna guda 2 Ta nufo Falon tana Faduwar gaba.

Yana Zaune kan daya daga cikin kujerun Falon  saboda gajiya ko Takalmin kafansa bai cireba ya kishingida da cussion din kujeran idanunsa alumshe kamar mai barci,Tana isowa falon taja Center Table din dake tsakar dakin Ta dora Ruwan akai,ganin idanunsa alumshe yasa Tamike salaf salaf zata fice taji yace”ok ni kikeso na zuba Ruwan dakaina kenan ko? haka kika ga goggo na min..? kyam ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya kafin ta waigo still dai haryanzu idanunsa alumshe suke Tahowa tayi tazo ta durkusa ta Bude Ruwan ta zubamai cikin kofin data hado dashi mikamai tayi tana fadin”ga Ruwan yaya captain..”Bude idanunsa yayi karaf ko suka hada ido,jikinta ne yafara rawa tana neman Mai bari da Ruwa yayi Saurin Amsan Ruwan yana fadin”ke shin wai meke damunki ne?ji yadda kikeneman min barin Ruwa ajiki..”Sunkuyar dakai tayi batayi mgana ba,bai sha Ruwan dayawa ba ya mikamata ta karba Mikewa tayi zata maida Farantin kichen taji yace”Jeki dawo yau dai naji menene mtsalarki..”yafada kai tsaye gabanta ya fadi tayi Saurin kallonshi shima ita yake kallo kauda kai tayi kafin ta Shige kamar zata fadi,bin bayanta yayi da kallo yana Tunanin anya yarinyarnan bata da Shafan Aljanu.

.  

  Sai da tabata lokaci kafin takoma,ita duk ta tsargu saboda bata da hijabi Sai wata doguwar Rigar Atamfa cikin wanda goggo ta dinkama ne,chan nesa dashi taje tazauna kanta na duke tana wasa da gefen dankwalinta kamar wata yarinya,kallonta yake yana Tunanin wani abu kai tsaye yace mata”Taso ki dawo nan mgana zamuyi kuma ba’a mtsayin mata da miji  amtsayin Yaya da kanwa..”jin haka yasa tadago tana kallonsa gyadamata kai yayi alamar tabbatarwa tashi tayi ahankali ta isa kujeran dayake zatayi kasa yayi Saurin riko hannunta yayi ya zaunar da ita agefensa yana fadin”Sit here..”Jikinta ne yahau rawa lokacin da hannunsa yatabi nata balle da kafadanta ke dukan nashi,ganin yadda Ta rudene yasashi dan matswa Shidai baiji komai ba,kodon baisaka Abun aka bane baisani ba.

  Yadade yana karema Surarta kallo Azeema ba Farace ammh tana da, hasken Fata sosoi wahalace ta maidata baka Tana da doguwar Fuska mai dauke da kyawawan idanuwa,hancinta bai cika tsawo ba,ammh yadace da kyakyawan Fuskarta tana gashin gira hade dana ido Masu kyau da Tsari bakinta dan karami ne,ammh leben sama yafi na kasa girma da kadan,in ta tsuke bakin sai ya birgeka yakuma baka Sha”awa doguwa ce bata da jiki,ammh tana Fadin kugu da kirji mai kyau kirjinta ba”a cike yake ba,sakamakon nonuwanta basu da wani girma na azo agani ammh Suna tsaye cur dasu,zarazaran yatsun hannunta yakoma yanabi da kallo kawai lokaci daya yaji ya tsaida kallonsa kan dokin wuyanta yadda wasu kananun gashi suka kwanta awajen,cikin kankanin lokaci tsigar jikinsa tafara tashi lumshe manyan idanunsa yayi kafin yakira sunanta.

  “AZEEMA….”Cikin Sanyin murya da muradi bata amsa ba,ammh sai tadago tana kallonshi saboda jin muryan dayayi amfani da ita wajen kiranta idanunsa ya bude fess akanta yana kallonta sadda kai tayi kasa kafin ta amsa.

  “Na”am…”gyara zama yayi kafin yace”Don Allah tambayanki zanyi waht i want is to tell me,d truth kinji ko..”Gyada mai kai tayi kafin tace”Toh insha Allahu.”good yafada kafin yaciga ba da cewa,”Ina so kifadamin hakikanin meke damunki?mekike bukata?me kika nema na Halin Rayuwa kika Rasa Azeema,in mganar Gidanku ne,yanzu kin dawo nan buh ammh har yanzu abubuwanki basa raguwa sai karuwa don Allah kifadamin meye ke damunki kokuma miye matsalarki? kudi? mkranta kikeson achanza miki? kokuwa baki son zama da goggon ne natafi dake kaduna ai zaki zauna abariki ko? Duk Abunda yake fada tanajin sa,wani tsausayin kanta ya kamata tare da Tsausayin yaya captain,jin Abunda yace na karshe ne yasata dago kanta tana mirmishi ammh hawaye sun cikamata ido kai tsaye ta girgiza kai batayi mgana ba,Hade naman goshinsa yayi kafin yace”To meye? kifadamin meke damunki kinganni nan banda yawan mgana i know ahaka halittata take buh ur own Azeema yayi yawa baki da sakewa ko kadan..”Yafada da alamar Abun ya dameshi.

  Dago kanta tayi tana kallonsa kafin tace”Hakika in nace nayi rashin wani Abu toh na zama butula babu Abunda na nema na rasa kuma ni babu Abunda ke damuna,in akwai Abunda na Rasa arayuwata abu dayane yaya captain..’kallonta yayi kafin yace”Maza fadamin meyeshi nikuma nayi miki alqawarin mgance miki duk wani Abunda ke damunki..”tadade kanta asunkuye kafin tadago idanunta na fitar da amon hawaye tace muryanta na Fitar da amon kuka.. *UWA…UWA..* ita na rasa yaya captain na rasa uwa wacce zata nunamin banyi daidai ba in gyara! na rasa uwa wacce zatamin fada ko tabani shawaran in wata mtsala ta sameni!,na rasa uwa wacce zan kwanta bisa kafadanta nayi kuka ta lallasheni!na rasa uwa wacce zata kalle ni ta sakamin albarka,duka na rasa wannan yaya captain na taso arayuwata nikadai nake gudanarshi,babana yana Sona ammh tsoron inna ramatu baya barinsa ya kebe dani ballatana har yasan damuwata na kasance duk wani damuwa da zan Shiga sai dai nayi kuka adaki ni kadai na lallashi kaina bani da dan”uwa ko wani Shakiki da zan Fadama damuwata yabani Shawara haka nake rayuwata nikadai,toyaya kewa tare da damuwa bazasu taru sunman yawa ba,ka fadamin yaya captain Tayaya…?Tafada tana Rushewa da kuka kamar zata shide.

Gabadaya kalamanta ya Sakashi jin wani tsabar tsausayinta ya kara mamayeshi kallonta yake tana kuka lokaci daya Shima damuwarshi ta dawo sabuwa,yasani shi mahaifi ya rasa ammh Goggo da kawu bala basu taba bari yayi kukan maraici ba,koda aboye koda asarari ne,itafa bata da kowa ba uwa ba,ba uba mai kula ma dangi ba wani dan”uwa sai da wanda Allah yaduba ya tsausayamata tabbas tafishi jin dacin rashin Abun Aranta fiye da yadda yakejin nashi Aransa.

Saboda tsausayinta baisan sadda ya mika hannu ya rikota ba,ya kwantar da kanta bisa kafadanshi yana bubbuga bayanta yana fadin”shiiiii….am srry kinji Stop Craying i promise i won let u down insha Allahu…”Yake fada yana sharemata hawaye da hannusa,gyara mata zama yayi suna facing din juna yace yana riko hannuta”Yanzu Firstly do u luv me,zaki zauna dani duk da ana ce nidin bani da cikakken asali wasu ma cewa suke bani da uba..? dago kanta tayi tana kallonsa dan hararansa tayi kafin tace”injiwa..? haba dai suma wasa sukeyi..” karkatar dakai yayi yana fadin,”Eh mana ko,kin manta dalilin haka aka hanani Auren Ni”ima Shine ma dalilin dayasa Auren yakoma kanki..”yafada yana cije lebe,kallonsa tayi kafin tace”Kayi hakuri haka Allah ya kaddara itadin ba matarka bace,..Kayi kokarin cire sonta aranka sai kaga komai ya wuce..”Zuru yayimata da ido kafin yace”who told u cewa haryanzu am in luv wit Ni”ima..”Sadda kai tayi taki mgana girgiza hannunta yayi yana fadin”Kiyi mgana waya fadamiki..”Kai tsaye tace”Azeeza ce…”Ware ido yayi kafin yace”Ohh i seee… wato ita ta zaunar dake ta tsaramiki haka,to kila ni nafadamata ko..”?yafada Fuskarsa na chanzawa saurin cewa Azeema tayi”A”a ni batace kai kafadamata b…”Toh meyasa kike yarda da duk Abunda tace miki,kina zaton ita da mahaifiyarta suna kaunarki ne,kinga dole fa in kinaso tamu tazo daya dake Azeema u should learn how to respect ur self,kiwani zauna yarinya karama na zana miki zence kawai don ta maisheki mara wayau..”yafada cikin Fushi Saurin Sadda kai tayi kafin tace”Kayi hakuri baza akara ba..”tafada tana Kwace hannunta ita tsoronta kada ya zuciya ya kaftamata mari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button