ALIYU GADANGA Page 11 to 20

#Comment,share,vote….#
#Janafty…#
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty????_
*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
_*A big congratulation to u my Sisi of life AISHA ALTO..4Completing ur Special,Amarzing,Fantactis,Adorable and Educated Novel…GIRMAN KAI(Rawanin Tsiya) d Whole book is dedicated to me,JANAFTY…kai am out of Contol fa,don wannnan babbar kyautace wanda bazan taba mantawa da ita ba,Ina mika miki Hannun Jinjina ????Sisinah domin kin baje dukkan basiranki da Fikiranki wajen Tsara wannan Novel din,hakika kin Fadarkar damu bayan Tarin nishadi da masu karatu sukayi, kin kuma samu nasaran isar da sakonki cikin Hanya mai Sauki,ke Tadambance awajena,Hakika salonki na burgeni kuma yana Tafiya dani,ina rokon Allah yabaki ladan Fadakardamu dakikayi bayan ya duba kuran kuran dakikayi ya yafemiki Duniya da lahira..Kaunarki Araina bata da iyaka..Bazan gaji da fada ba,bakuma zanji kunyan maimaitawa ba Nagode sosai bisa karamcinki gareni My Sisi of life gabadaya shafin na yau mallakinki ne,na baki shi halak malak..Kisani ki kara sani AISHA ALTO KINA BURGENI*_????
*NOT EDITED*????
*Chapter 9*
“””Sati uku kenan da Tafiyar Aliyu gadanga ammh baizo gida ba,sai dai waya da sukeyi Shida goggo,ammh ba kullum ba saboda Tunda ya koma yazama yana keeping kansa busy baya zama sosai,akwai wasu bataliyan Sojoji da yake koyama Training bai samun lokacin kansa ma,balle na Tunani,ya tattara komai ya watsar da zarar Tunanin Abunda ya faru ya fadomai zaiyi Saurin Kaudashi ko Afuska baya nuna alama,hatta jabir duk nacinsa,da son gulmansa,sai da ya hakura,shiko Haisam yadai kirasa awaya sun yimagana,kuma duk Akan yayi hakuri da Abunda Allah ya kaddara maine,to ya zaiyi?ai baya da tacewa shikam Tunda haka Allah yayi dashi.
Ni”ima kuwa sai da ta shafe Sati a asibiti kafin asallameta tadawo gida,Jikin nata da sauki ammh kullum kwana take kuka saboda Rashin Aliyu atare da ita,Maminta ne da kawarta muneera suke kokarin kwantar mata hankali,ammh ina bata ji bata gani,game da Captain dinta zata iya komai,kawai tana kokarin nuna komai ya wuce ne saboda damuwar Maminta da Abbanta da kuma kawarta muneera,ammh taci alwashin bazata bari captain dinta ya subuce mata ba,zataje koda chan kadunan taasan in ya ganta bazai iya kauda ido akanta ba,dole zai tsausayamata su dawo su kara Shirya Auren nasu akaro na biyu,duk da ta san zata Fuskanci kalubale,har zuwa lokacin Ni”ima bata San cewa Captain dinta yayi Aure ba,shiyasa take ganin shawo kanshi mai sauki ne.
Bangaren Azeema kuwa babu Abunda ya chanza na dangane da Rayuwarta,inna da Azeeza sungama yawo da mganar a anguwa suna fadin Babanta yaga kwadayi ya auramata mara asali,kuma dan” iska,har a mkrantansu saida Azeeza taje da lbrin sai ya zamana Azeema tazama Abun nune da zunde duk sai taji duniyar tayimata kunci da zafi,ko kawayenta na anguwa haka suke kallonta suna fadin kwadayi zai kasheta ita da ubanta,Azeeza na fadn mganganun banza akanta ana mata dariya,mussaman in suka hadu a bohol taje debo Ruwa da kuka take dawowa,wajen Babanta kadai take samun sauki,sai ko wajen Baba Ade kakarta sai wajen uwa gareta goggo wanda tagama guje gujenta ta hakura taje gidan goggon wacce takamata ta Rumgumeta tana mata tsiya,ita goggo ta fadamata cewa ita ba”a Suruka take kallonta ba,a mtsayin Ya take kallonta saboda haka itama Tadauketa amtsayin uwace wacce ta haifi Aliyu da Azeema,dole Azeema ta saki jikinta duk da Nauyin da Goggo ke mata bata da yadda zatayi saboda goggo babu ruwanta hira take da ita kamar ba matar Danta ba,Tuni Azeema ta saki jikinta suka cigaba da yadda suke da goggon kamar da,agidan take Wuni sai yammah take komawa wannan bakin gida,Inna ko babu Abunda ta fasa na muzgunama Azeema sai ma Abunda yayi gaba,yanzu Azeeza Abunta yayi kamari ko mgana Azeema tayi mata tsab zata saka hannu ta shareta da mari bata da bakinn mgana don sai inna ta kusa kasheta lokacinta baiyi ba,shiyasa ko Baba bata bari yaji saboda duk hukuncin dayayima Azeeza akanta inna zata saukeshi shiyasa take hakuri tasha kukanta ta sharbe hawayenta bata da mai lallashinta,duk ta rame ta kanjame kamar ba ita ba,tayi baki,ga wasu kananan kuraje sun Fito mata in ka kalleta bazakayi Tunanin yarinyace yar shekara 20 ba,sai kayi zaton ta haurama talatin30 baya saboda wahalar rayuwa don ma goggo na tsaye kanta,Abun ne ya ishi goggo dole ta matsama Aliyu yazo gida tana son ganinshi don tanaso ya tsamo Azeema daga wannan kangin bautar datake ciki Tunda dai yanzu Shike da iko da ita,kuma tasan duk iskancin inna Ramatu tana shakar captain din.
*************
Sai da Aliyu gadanga ya shafe sati Shida baizo gida ba satin ma sai da ya biya gidan kawu bala suka gaisa da Ummah kawu ma bayanan ya tafi Abuja Haisam ma bayanan yana kano wajen aiki,Shiyasa bai dade ba daganan ya kamo hanyar Gombe zuciyarsa duk babu dadi saboda yaasan kiran gaggon bai Wuce mganar sokuwar yarinyarnan ba,wanda gabadaya baya son Tuna komai,Shidai burinsa da Addu”asa bai Wuce Allah ya bayyana mishi Asalin mahaifinsa ba ko zuciyarsa zata daina wannan Nauyin data dade tana fama dashi.
Da misalin karfe 2:30pm ya Iso kofar gidan nasu cikin lafiyayyayiyar motarsa din nan 4matic,kofar gidan ya faka motar,bai shiga da ita garejin ba nan ya barta ya bude booth ya shiga jiidan Tsaraban da yayima goggo yara na Jida suna shiga dashi cikin gidan goggo,wacce ke tsakar gida tana jin Radion ta taga Shigowar yara ko bata tambaya ba,Tunda taji dirin mota ranta ya bata gadanga ne,jikinta na Rawa ta mike har zaninta na neman Faduwa ta nufi hanyar waje Sukaci karo da gadanga ya taho jikinsa sanye da Riga da wando Rigar fara ce ammh wandon Nevy blue ce,sai takalmansa rufaffu ne, kansa babu hula gashinsa yasha gyara yana kyalli,Rumgumosa Goggo tayi tana fadin”Oyoyo gadanga..Sannu da zuwa Gadanga kusar yaki,ga soja mazan fama Ah..Soja na Azeema…”Goggo take fada tana Rumgume da Aliyun..
Dariya yake yana Rike da goggon yake fadin”Oyoyo goggo ta….Nayi kewarki sosai mamata..”Dunguremasa kai tayi tana fadin”bakayi kewata ba gadanga Tunda sai da nayi ta magiya kafin ka dawo..”Tafada tana Amsan jakar kayansa dake hannunsa,dariya yayi kafin ya saka hannu ya zagayo da hannunsa kan kafadanta kamar wasu kawaye suka jera zuwa cikin gida yana fadin”Haba goggo..Kefa kika haifi gadanga..Kinfi kowa saninshi ko zan manta da kowa wlh banda Uwar Ali gadanga..”Yafada yana wani lamgwabemata nishadi ya kashe goggo tana dariya,ahaka suka karisa daki,tana mai maraba,saboda murna ma goggo bata bashi Ruwa ba,saida tagama kawomai abinci kafin ta tuna,dariya ya dinga mata yana jin dadin zama da goggo sosai haka suka zauna sukaci abinci tare suna hira da dariya in ka kallesu bazakace mahaifiyarsa bace sai ka dauka Kaninta ne saboda yadda take yar daidai da ita.
Azeema data dawo daga kai nikan Alalan da inna ta Aiketa tunda tadawo mkranta ta bata nikan ko Uniform bata cire ba,tatafi kai nikn,,gashi ta tarar da layi sai da tadade bata dawo ba,tana ta sauri ta iso kofar gidan goggo gabanta ne ya fadi dataci karo da Motar yaya captain bakinta har rawa yake tana karkarwa,tana leken gidan ta yi Saurin Wucewa jikinta na rawa saboda tsoro,koda da takaima Inna nikan sai da ta mareta tace ta dade ta tsaya iskancinta bata dawo da Wuri ba,ita duk wannan bai dameta ba,duk fargaban Dawowar yaya captain ya dameta ammh ta godema Allah dayasa taga motarsa da sai ta shiga su hadu da juna,rike baki tayi tana Tuna karonsu dashi,kayan mkranta kawai ta cire tazo ta hau sharan gida,wanke wanke ta hada,ta duba rijiya babu wani Ruwan kirki,tunda rijiyar taja baya sosai babu Ruwa shiyasa take wahalam Aiki yanzu Tunda ga debo Ruwa ya karu,karamin hijabinta ta sanya Domin Riga da sikat ne ajikinta kayan ma sun mata kadan domin sun matseta,rashin wadatattcen kayan ne,yasa take sakasu har yanzu,botikai uku ta diba ta fice zuwa bohol din dake gaban gidan goggo da kadan,sai da ta leka ta tabbatar da kofar gidan goggon babu kowa kana ta fito ta wuce tana waigo koda taje wajen layi yayi yawa sosai,dayake anfara mtsalan Ruwa,idonta ne yakawo Ruwa data tuna da Abunda inna tace,tace in tawuce minti goma bata dawo ba,sai na lahira ya fita jin dadi,jikinta na Rawa ta shiga rokon yan matan dake wajen su bata da diba ko botiki daya ne,kallonta sukayi shekeke kafin su sheke da dadariya suna fadin”,Ahhyyyye…Sannu isassa…Kije sojan da kwadayi yakaiki aurensa yazo ya kwatan miki,an dai ji kunya mutum yazama matar aure,ammh kullum ko karen layi bai kaishi Arha ba..”Kallonsu Azeema takeyi hawaye na zubomata domin dukkansu kannen bayanta ne,kawayen Azeeza ne,batace komai ba,sai takoma gefe tana sharan hawaye tana jiran layi ya kawo kanta ta diba.