ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

  Inna Ramatu na zaune bisa kujeran Tsugunno atsakar gida tanata bala”i ita kadai ba Azeemar babu Azeezar ba wanda ya dawo,kawai sai ganin tayi Tsulum Mutum ya shigo gidan bai dire ko”ina ba sai agabanta ya ijiyemata botikan Ruwa ta dago ta kallonsa cike da mamaki,kafin ta mike tana zare,ido lokacin idonta ya sauka kan Azeema data shigo ta rabe gefe tana hawaye,Cikin wani masifa inna Ramatu ke fadin”Kai mallam lafiyanka kuwa zaka shigo gidan matan Aure babu Neman izini..”Tafada tana binsa da harara,domin ta ganeshi yaron nan ne mara kunya,don tanajin Haushin Rashin gaishetan da bayayi.

Ko kallonta baiyi ba,saima juyawa dayayi zai Fice yana kallon Azeema data rabe gefe tana zuban kwallah,kallonta yayi dakyau lokaci daya dayaji Tsausayinta ya tsirgamai saboda koda yaushe cikin kuka take kuma duk ganin da zai mata cikin wahala ne,Ransa ne yayi zafi Shiyasa ya waiga yana fadin”plz Inna kada Akara aikan Azeema zuwa dibo Ruwa infact duk wani aike adaina aikenta,Cuz yanzu ba da bane,tana da hukunci da Nauyin igiya uku akanta,in don wanda zai dinga debo miki Ruwa ne babu mtsala zan neman miki ammh plz and plz kada in kara ganin Azeema awaje matukar ba mkranta zata ba…”Yafada idonsa kyam a na inna Ramatu wacce ta Rike baki saboda mamaki.

  Inna Ramatu hannunta abaki Tana fadin”Eh lalle sannu Lawali..Toh baza”a daina aikenta ba din,amtsayinka nawane zaka zo kana bani Umarni…”dan mirmishi yayi kafin ya tako zuwa gabanta yace”Inna kin taba zuwa bariki don Allah…”Yafada yana sosa sajensa bayan ya kafamata ido,Ganin haka yasa inna ta fara ja da baya tana kifkifta ido,Daure Fuska yayi kafin yace”Toh matukar baki bi Umarni na ba,zan sa azo asace min ke,sai kin kwana kin wuni acikin Firiza mai maida jikin dan Adam kankara,kafin na hadaki da sojoji su huce Haushi akanki..Maza ki amsa min da Toh…”yafada yana Buga hannunsa bisa cinyarsa sai da tayi kara,ai inna Ramatu bakinta na Rawa take fadin”Toh..Toh angama yallabai..”Take fada tana Dafe bakinta jikinta ba inda bai Rawa saboda jin ya ambaci xai saka asaceta tasan tsab zai iya don ba mutumci ne dashi ba..

Ganin yadda take Rawan jiki yasa dariya yakusa subucema Azeema tayi Saurin dafe bakinta,Aliyu ya bita da kallo kafin yadan murmusa yana kallon Inna Ramatu”Ahankali ya Furta “Good…”Yafada yana juyawa bai ko kalli barayin da Azeema take ba ya fice daga gidan cikin Takunsa na Takama da Jarumta,Yana ficewa Inna Ramatu ta hau leka kofar waje tana fadin”Baza abi ba din..”Tafada tana zare ido,dariyan Da Azeema take boyewa sai da ta Fito,kallonta Inna tayi tana fadin”Zan ci ubanki shegiya mai Farar kafa,wlh in yasa aka sace ni daga ke har Lusarin ubanki in nadawo bazaku ji da dadi ba..”Tafada kafin buguzun buguzun takoma daki tana borin kunya,ammh jikinta tsab da tsoron Captain..

Shiko yana fitowa ya nufi wajensu Azeema yaga yadda sukayi saboda wuya,yana zuwa yace su dakata kowacce ta mike,ai fa nan fa daya gabadayansu gwiwa tayi sanyi basa iya mikewa saboda yadda sukaji Jiki,tsawa ya daka musu suka tsaya kan kafafunsu suna rawan jiki,Kallonsu yayi yana dan mirmishi kafin yace”Gud job..Kun gaji gashi kunyi zufa,so kowacce taje ta cika botiki daya kafin in Tuna wani pushiment zaku yi next..”Kallonsa sukayi suna hawaye,Itako Azeeza duk azaban data ke ciki kallonsa take cike da so da kauna,yadda ya tsaya sai taji kamar taje ta Rumgumeshi,har wani lumshe ido takeyi tana lasan baki tsawan daya kara daka musu ne ya fargar da ita,gabadayansu suka je,kowacce taje ta cika botiki daya,na mutanen dake wajen suna gamawa yace kowacce ta dauko akanta tazo nan,haka suka dauko suka zo,suna zuwa yace”Kowacce ta kalli yar”uwanta..,Bayan sun kallah yace”Kowacce ta juye Ruwan jikin nakusa da ita…”Kwalalo ido sukayi suna binsa da kallo,tsawa ya daka musu yana fadin”in na kirga uku bakuyi Abunda nace ba,zan sauya ra”ayi daga wanka Ruwa zuwa na kasa kuma wlh zanyi Abunda nace..”Yafada kai tsaye,ah bai gama Rufe baki sukayi ma kansu wanka da Ruwa,kallonsu yayi yaga kowacce tayi tsamo tsamo kamar wasu zakaru Dariya ta kamasa,ammh sai ya matse da kallo ya bisu kafin yace”Yauwa kun warware gajiya by now kowacce tasaka gwiwanta akasa ammh kuma ta juya ta kalli hanyar gidansu..”yafada yana mirmishin mugunta,Zubewa sukayi kowacce na kuka harda majina,domin ji suke tamkar gangar jikinsu bazai iya Daukansu ba.

Wucewa yayi yafara tafiya kafin yace”Kowacce tafara jan gwiwa har zuwa gidansu,wlh tallahi duk wacce tatashi na ganta ko na kamata,yau sai ta zagaye anguwan nan tana jan gwiwa,toh tun kuna son kanku da Arziki kuyi yadda nace,dis one na small one,duk Randa kuka karama matata Rashin kunya  zanyi Doubling din hukunci danayi muku yau,so be carefull..”Yafada yana wucewa kafin yace”1,2,3…Start…”Da hanzari kowacce ta fara suna jan gwiwa suna kuka wiwa,Inda Allah ya taimakesu duk yan wajajen nan,gidajensu babu nisa sosai,nan kowacce ta nufi gida da jan gwiwa tana kuka harda majina,Shiko Aliyu gida ya shige ko ajikinsa,shiko Sulaimam bai Tafi ba sai da akaci aka sude sai dariya yake Ransa fes anyi maganin marasa kunya.

  Sai ga inna Ramatu da kanta ta fito tana hada Kulin Alalan tanayi tanama Azeema Allah ya isa,sai ga Azeeza ta shigo da jan gwiwa tana kuka Fuskarta ta hade da majina da kuka,ga jikinta ajike da Ruwa da hanxari tayi Wurgi da ludayin hannunta tana fadin”Na shiga Tara ni Ramatu Azeeza gamo kikayi kokuwa karo kikayi keda mai akori kura,yayi miki wannan damejin da jiki…”Tafada tana karisawa gareta tana riko Azeeza,gocewa Azeeza tayi ta zauna dirshan Tana kuka gwiwanta duk sun sale saboda janta datayi akaasa,Kafafunta kuwa ciwo suke matw kuka take tana hadawa da ihu tana fadin”Wayyo inna wlh kafata zafi takemin kuguna,ya rike ban iya mikewa saboda azaba..”Tafada hawaye suna zubomata,Azeema dake lekensu ta window ta kece dadariya tana kama bakin ganin yadda Fuskar Azeeza ta dawo kamar wacce akayi wasan kura da ita,kallonta inna tayi tana fadin”ke wai tsaya Hatsari kikayi ne komiye..?”Azeeza na kuka tace”Wani hatsari inna,ba yaya captain bane saboda naje kiran Azeema tazo in jiki ba,sai ta dauko Ruwa tazo zata wuce shine santsi ya kwasheta tafada kwata,shine shine fa,yazo ya hadamu nida su lantana,yasakamu tsallon gwado bayan mungama yasa mukama junanmu wanka,duk hakan bai ishesa ba,sai da yasamu kowannenmu yaja gwiwansa zuwa gida..”,Takarishe tana yaye zanin jikinta gwiwanta ya bayyana Duk ya sabe,baya inna Ramatu taja tana salallami take fadin””Kutmar ubanchan,yanzu Shi yayi muku hakan?gyada kai Azeeza tayi tana fyace majina,Haba Inna ta rike tana fadin”Lalle ya cika mara mutumci ai sai ki tashi ki gasa jikin ki,kiyi hakuri..”da mamaki Azeeza ke kallonta kafin tace”Inyi hakuri fa kikace inna,nazata zaki Ramamin kan Adda Azeema tunda akanta ne yayi mana haka..”baya inna taja tana fadin”Wa ni? Rufamin Asiri nima bai dade da fita daga gidan nan ba,yamin kashedi sosai kan Azeema yace duk Randa na saba umarninsa,sai ya saka ansace,na kwana afiriza mai maida jikin mutum kankara,kafin ya hadani da sojoji suyi wasan kura akaina,..”Tafada tana waigen kofa,zaro ido Azeeza tayi tana fadin”da gaske inna…”Gyada mata kai tayi tana fadin”Wlh kinga kuwa ko saceni yayi babanki bazai damu baTunda yafi son Wanchan sakaryan Akanmu..”Shuru Azeeza tayi batama inna mgana ba,Tunaninta yatafi kan Tunano Fuskar Abun kaunarta,Inna da hanzari taje ta hura wuta ta saka Ruwan zafi kafin tazo ta ciccibi Azeemar zuwa kofar dakinta inda ta Shimfida mata tabarma,Azeezar sai wash wash take saboda azaba ammh kuma ko Ranta batajin Haushin Captain ba,saima tsanar Azeema daya kara cika zuciyarta ta kudiri niyar ko ta halin kaka sai ta mallaki muradin Ranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button