ALIYU GADANGA Page 11 to 20

*#Comment share,and vote…#*
*#Intelligent writer’s asso…#*
*#Janafty….#*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty????_
*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*NOT EDITED*????
*Chapter 11*
“””Goggo na cikin kichen taji Sallaman Azeema,da hanzari ta fito tana fadin”Ah Azeema,kice kamar daga sama da daddaren nan? Tafada tana kallonta,Sunkuyar dakai Azeema tayi tana kokarin dukawa ta gaida goggon saurin Rikota tayi tana fadin”A”a tashi kada muyi haka dake,bama wannan ba,miye naga kina wani zare ido,gabadaya kamar atsorace kike,gayamin badai wani lalatattace bane ya biyoki yanzu na fita naci ubanshi,kokuma na hadashi da gadanga wlh yaci uwarshi yanzu nan fadamin waye ya biyoki naga kin Shigo a Tsorace”Dan waro ido Azeema tayi kafin tace”Ba kowa bane fa inna Dama yaya captain ya daki Azeeza saboda tamin Rashin kunya,shine na shigo nan kada na koma gida inna ta huce akaina..”Galala Goggo ta kalleta kan tace”Ai yamin daidai wlh,kema dai Azeema wlh ki kamma jikinki,in dai kina wannan sokanci wlh bazaku Shirya da gadanga ba,shi mutum ne dabayason wargi balle shashanci yo in ma kinaso sace zuciyarsa ne,na baki satan amsa ki zama mace Tukunnah bayan kinkam jikin ki Atoh..”Tafada tana Riko hannunta,Baki Azeema takama tana yar dariya,Mangare mata kai goggo tayi tana fadin”Au dariya na baki ko?yo ai gaskiya ne,ammh wani lokacin in kina wani Abun sai ki dinga Tunamin da Mahaifiyarki Fatima,wlh Azeema yadda kike da hakuri da kawaichi to Fatima ta fiki..”Tafada cikin sanyi,nan da nan idon Azeema ya ciko da hawaye,dafa kanta goggo tayi tana fadin”Karki damu Azeema wlh Tamkar Aliyu haka nake kallonki da izinin lahi sai kin zama Abun alfahari,da kin Tuna da mahaifiyarki karkiyimata kuka kiyi mata addu”a da Fatan tana kyakyawan mtsayi kinji ko? dakai Azeema ta amsa tana share,kwallah hijabin jikinta goggo ta ciremata bayan ta amshi al”qur’anin tana fadin”Maza shiga shiga ciki ki dauro alwala kizo muyi sallah sai muci abinci yanzu na gamashi da zafinsa,ai ni nagodema ja”irin nan gadanga daya bugemin Mara kunyar yarinyarnan gashi sanadin haka yata tazo wajena,duk da yanzu wasan buya ake dani Tunda Megida yadawo..”Tafada tana kyabe baki,Tura baki Azeema tayi tana fadin”kai goggo ba ina zuwa ba,kuma ni yaushe nace haka..”Goggo tayi yar dariya tana fadin”Au hakane fa,to naji baki ce ba,maza shiga kiyo ki fito an kusa sallame salla daga masallaci..”Tafada tana Ficewa daga Falon,itako Azeema dan mirmishi tayi kafin tafada bedroom din na inna wanda in ka gansa ko na wata amarya albarka saboda yadda yasha wani ubansu royal bed mai kyau da tsari gashi yana malale da capet mai kyau da tsari,da makeken wardrope dinta sai madubinta dake shake da kayan shafa na mata,wanda goggo banda kwalli bata shafa komai,ammh kullum taramata Ali gadanga yake,Tunda kawu ya daukemata Nauyin komai.
Tare sukayi jam”i da goggo suna gamawa goggo ta zubomusu abinci Shinkafa da miya sai slat datayi musu goggo fa,ba baya ba,akwai iya girki sosai kamar ka tsinke hannu,nan suka zauna Dole tasa Azeema sakin jiki don goggo dai kun santa dole ma mutum ya saki jiki da ita,da farko Azeemar kin ci tayi,aiko goggo tayimata barazana da zata kira Aliyu yanzu yazo yayimata dure,kila taci jin haka yasa taba goggo hakuri ta hau cin abinci dama yunwa takeji sosai domin tun karin safe rabonta da Abinci,Ammh tanayi tana waige da sauraran waje kada Yaya captain yazo ya Ritsata.
Itako Azeeza tana shiga gida da ihu Ta iske mallam lawal atsakar gida shida Inna Ramatu,jin ta shigo da ihu yasa Inna mikewa tana fadin”Ke lafiyanki kuwa keda wane..”gabansu Azeeza ta zube tana fadin”Inna wlh In baki dauki mataki kan Adda Azeema ba,ni zan dauka dakaina..”Tafada tana hawaye,wanda bana zafin marin da yaya captain yayimata bane,a”a takaichi yadda taga kamar yana tsausayin Azeemar ne,wanda ita ba burinta kenan ba,burinta kafin yafara son Azeemar ita ta riga ta mallake zuciyarsa Allah barshi ya dankarama Azeemar sakinta ta kara gaba.
Inna tace”Toh me tayi miki ne,nifa bangane ba? Kyabe Fuska Azeeza tayi tana fadin”Ba ba kawai mundawo daga Mkranta bane zamu bi ta kofar gidansu yaya captain Tunda Adda Azeema ta ganshi shikenan ta nufi wajensa,bansan metacemai ba,naga dai Tana ta nunoni,ban ankara ba yazo kusa dani kawai ya mareni,kuma ya saka kafa yayi Shuru dani..”Tafada tana kara barkewa da kuka kamar gaske
Kutmar ubanchan..”Inna tafada Tana rike kugu kafin ta waiga tana fadin”Ammh dai kaji Abunda tsinanniyar yarka tayi ko? ammh naga kayi Shuru bakace komai ba”Ko kallonta baiyi ba yace”Nidai ban Tsinema yata ba,sai dai in ke kika Tsinema taki,mganar kuma da makaryaciyar yarki ta fada ba gaskiya bane,na tabbata Azeema bazata kulla miki sharri har Aliyu ya dakeki ba,sai dai in rashin kunya kikamai ya hukuntaki..”Yana gama fadar haka ya mike yana kakkabe rigarsa yake dakama Azeexa tsawa yana fadin”Tashi kiba mutane waje,matukar baki zama mutum ba,har abada ni dake bazamu Shirya ba..”Yafada yana Shigewa daki.
Da kallo inna ta bishi kan takoma ta zauna tana fadin”Eh na yarda tabbas Watarana Azeema zata kashemun aure,toh kan ta kashemun ni zan mata dukan mutuwa dasai ta gwammace kida da karatu,wlh tallahi sai dai duk Abunda zai Faru ya faru..”,Tafada tana huci,ganin haka yaasa Azeeza tashiga zigata na taci uban Azeemar in tadawo itako inna huci kawai take kamar wata macen zakanya.
Shiko gadanga yana idar sallah yadawo gidan,yana shigowa yaji muryan goggo tana hira cikin hiran natane yaji ta ambaci Azeema jin haka yasa yayi burki zuwa dakinsa cuz bayasan ya mtsama yarinya Tunda ya lura tsoransa takeyi,bai cika cin abinci mai nauyi ba da daddare,shiyasa goggo bata damu da nemansa ba,balle ta kaimai Abinci,har wajen goma Azeema na gidan sai lokacin tace zata koma gida goggo tayi tayi ta tsaya ta kwana ammh taki dole ta kyaleta ammh aranta tana addu”ar Allah ya hadata da gadanga ya warfatota tadawo akwai illai tana Fitowa tsakar gida cikin sanda Ya hangota dama yaji karan bude kofa,Fitowa yayi yana kallonta tana tafiya ahankali Gyara tsayuwa yayi sai da takusa isa ga kofar gidan daya kulle Tun dazu kan yace”Ke…”,yafada cikin sanyi,Cak ta tsaya jikinta na rawa jin muryansa kafin ta waigo Arazane kallonta yayi kafin yace”Ina zaki..”?Bakinta na rawa tace,”Gi…gida…Za..zani..”harara ya zabgamata kafin yace”dallah wuce kibama mutane wajen gidan wa zaki Da daddrenan..”Yafada yana kokarin komawa daki,kin tafiya tayi ganin haka yasa ya dakamata tsaawa yana fadin”Au zaki wuce ko sai nazo na tattaka ki anan wajen ne..”Jin haka yaasa tayi dakin goggo da gudu tana rawan jiki,gyada kai kawai yayi ya rufe kofa ya koma ciki,tana shigowa daki taga goggo na mata dariya tana fadin”Allah yamaka albarka gadanga…”Take fada tana ma Azeema dariya,Azeema tayi nakwa nakwa da Fuskar kamar zatayi kuka da sauri goggo ta rikota tana fadin”Yi hakuri kema Allah miki albarka Azeemata muje mu kwanta kinji..”Tajata zuwa kan makeken gadon nata ta kwantar da ita,tana shafa kanta tace”Toh kwanta kiji gobe da safen zan rakaki har gidan kinji ko? gyada mata kai Azeema tayi tana dan mirmishi Aranta tanajin son goggo na ratsata saboda yadda take kula da ita.